Aminiya:
2025-11-18@14:02:57 GMT

A gaggauta binciko makasan ’yar jaridar Arise TV —Tinubu

Published: 30th, September 2025 GMT

Shugaba Bola Ahmed Tinubu tare da uwargidansa, Sanata Oluremi Tinubu sun bayyana alhini kan kisan gillar da aka yi wa  Somtochukwu ‘Sommie’ Maduagwu, waata ’yar jarida mai gabatar da labarai a gidan Talabijin na ARISE TV.

A wata sanarwa da fadar shugaban ƙasa ta fitar, shugaba Tinubu da uwargidansa sun yi Allah-wadai da kisan, suna mai bayyana cewa a matsayin babban rashi a ƙasar da kuma fagen aikin jarida.

’Yan sanda sun cafke ababen zargi 4 a Yobe An ƙaddamar da shirin rajistar yaran da ba su zuwa makaranta a Gombe

Aminiya ta ruwaito cewa, marigayiyar ta rasu ne bayan wani farmaki da ’yan fashi suka kai gidanta da ke Katampe a Abuja, a ranar Litinin da ta gabata.

Tinubu ya yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta gudanar da cikakken bincike, tare da tabbatar da cewa wadanda suka aikata laifin sun fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Ita ma uwargidan shugaban ƙasar ta bayyana marigayiyar a matsayin jaruma mai ƙwarewa da gaskiya a aikinta, tana mai cewa murya irin tata tana da tasiri matuƙa wajen wayar da kai da isar da gaskiya ga al’umma.

 

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: ARISE TV

এছাড়াও পড়ুন:

Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas

Gobara ta laƙume rayukan wasu yara biyu ’yan gida ɗaya a unguwar Rumuola da ke ƙaramar hukumar Obio/Akpor a Jihar Ribas.

Bayanai sun ce ibtila’in ya auku ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Lahadi, lokacin da gobarar ta tashi a ɗaya daga cikin wasu ɗakunan haya da mahaifiyar yaran ta kulle ’ya’yanta huɗu ta tafi sayen kayan girki.

Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe

A cewar mazauna yankin, cikin yaran huɗun, biyun da suka riga suka kwanta barci sun ƙone su kurmus, yayin da sauran biyun da ke farke suka samu damar tserewa.

Aminiya ta ruwaito cewa, mazauna yankin da sun ankara da gobarar ce bayan sun hangi yadda hayaƙi ya turnuƙe sararin samaniya, lamarin da ya sa suka gaggauta kiran ma’aikatar kashe gobara kuma suka kawo dauki domin tarar hanzarin lamarin na hana gobarar bazuwa zuwa sauran gidaje.

Yadda ake kwashe komatsai bayan ibtila’in gobarar

Haka kuma, wani mazaunin yankin ya musanta jita-jitar da ake yadawa a kafafen sada zumunta cewa gobarar ta tashi ne a harabar wata kwaleji ta Captain Elechi Amadi da ke Rumuola, yana mai bayyyan cewa lamarin ya faru ne a bayan makarantar, inda ake da dogayen gine-gine da ke ɗauke da iyalai sama da 27.

Ya bayyana takaicin cewa dubban mutane sun rasa matsugunni a sanadiyar gobarar wadda ta ƙone dukiyoyin da darajarsu ta kai miliyoyin naira.

Mai magana da yawun ’yan sanda a Jihar Ribas, SP Grace Iringe-Koko, ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa yaran biyu da suka mutu shekarunsu na haihuwa ba su gaza biyar da tara ba.

Ta ce an fara bincike domin gano musabbabin gobarar, kana an gayyaci mahaifiyar yaran domin amsa tambayoyi.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Za mu ceto ’Yan Matan GGCSS Maga cikin ƙoshin lafiya — Gwamnan Kebbi
  • Sace Ɗalibai: Gwamnatin Tinubu ba ta shirya kawo ƙarshen ta’addancin ’yan bindiga ba — Amnesty
  • Gobara ta laƙume rayukan yara biyu ’yan gida ɗaya a Ribas
  • ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe
  • ’Yan sanda sun kama ƙunshe 66 na Tabar Wiwi a Gombe
  • Bai Dace Adalci Ya Zama Na Sayarwa Ba – Tinubu Ga Alƙalai 
  • Hauhawar farashi ya ƙara raguwa a Nijeriya — NBS
  • Ɗan Najeriya ya kashe mahaifinsa, ya yanki ƙannensa da wuƙa a Amurka
  • Kuri’un Jin Ra’ayi Na CGTN Sun Shaida Adawar Sassan Kasa da Kasa Da Burin Masu Tsattsauran Ra’ayi Na Japan Na Ruguza Odar Kasa Da Kasa Ta Bayan Yakin Duniya Na 2 Dangane Da Batun Taiwan
  • Sanusi II Kaɗai Muka Sani A Matsayin Halataccen Sarkin Kano – Kwankwaso