Ɓarawon da ya sato motar asibiti daga Nijar ya shiga hannu a Jigawa
Published: 9th, October 2025 GMT
Jami’an Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) a Jihar Jigawa, sun kama wani matashi da ake zargi da sato motar asibiti daga Jamhuriyar Nijar, yayin da yake ƙoƙarin shigowa da ita Najeriya.
Kwanturolan hukumar a jihar, Tahir Abdullahi Musa ne, ya tabbatar wa manema labarai hakan a Dutse.
Falasdinawa na murna da tsagaita wutar hare-haren Isra’ila a Gaza Sauye-sauyen Tinubu ba su rage talauci a Najeriya ba — Bankin DuniyaYa ce an kama wanda ake zargin mai suna Yusif Bashir da motar asibiti ƙirar Toyota Land Cruiser mai lambar ONG-0777, bayan ya shigo da ita ta iyakar Babura da Jamhuriyar Nijar.
Tahir, ya ce tuni hukumar ta fara shirye-shiryen miƙa sh ga rundunar ’yan sandan jihar, domin ci gaba da bincike.
Ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da haɗa kai da sauran hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a jihar.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: ɓarawo Jigawa Motar Asibiti Nijar Zargi
এছাড়াও পড়ুন:
Kungiyar ‘Yan Dako Ta Kasa Ta Nada Sabon Sakatare A Jigawa
Kungiyar ‘Yan Dako ta kasa reshen jihar Jigawa ta kaddamar da Malam Muhammad Tajudeen Maigatari a matsayin sakataren kungiyar na jihar.
Da yake jawabin a lokacin bikin kaddamawar a garin Maigatari, Shugaban kungiyar na jihar Malam Nasiru Idris Sara, ya bayyana shugabanci a matsayin rikon amana a maimakon hanyar tara dukiya da alfahari, a don haka akwai bukatar sakataren ya yi aiki tukuru dan kare martabar sana’ar dako da masu yin ta.
Yana mai cewar shugabancin kungiyar zai hada kai da shugabannin kananan hukumomi da masu rike da sarautu da jami’an tsaro a matsayin abokan kawo cigaba wajen daga likkafar sana’ar dako.
Nasiru Idris Sara ya kuma yi kira ga daukacin ‘yan dako a fadin jihar da su yi rijista da kungiyar domin kasacewa a karkashin inuwa daya ta yadda za su ci moriyar tanade tanaden ta, sannan su kasance masu mutunta shugabanci da kuma bin doka da oda domin inganta rayuwar su.
Ya ce yayin da kungiyar ta ke da ‘yan dako kimanin dubu 20 a karkashin ta, akwai bukatar duk ‘yan dakon da ba su da katin zabe su karbi sabo ko kuma su sabunta wanda ya bata ko ya lalace domin amfani da damar su wajen zaben shugabanni.
A sakon sa, Hakimin Maigatari Alhaji Sani Alhassan Muhammad wanda ya sami wakilcin Sarkin Kasuwar Maigatari Alhaji Muhammadu Sarkin Kasuwa, ya bukaci sabon sakataren kungiyar Malam Muhammad Tajudeen ya kasance mai nuna gaskiya da adalci wajen huldar sa da ‘yan dako da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci, inda ya bayyana murnar samun wannan mukamin.
Cikin wadanda suka halarci taron sun hada da Sarkin hatsin Maigatari, Malam Mu’azu Bako da Shugaban leburorin Dingas na Jamhuriyar Nijar Malam Lawwali Hassan.
Usman Mohammed Zaria