Naɗin Olubadan: Tinubu da manyan jami’ai sun ziyarci Ibadan
Published: 26th, September 2025 GMT
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ziyarci birnin Ibadan, a yau Juma’a domin halartar bikin miƙa sandar sarauta ga sabon Olubadan na Ibadan, Oba Rashid Adewolu Ladoja na 44 da ake kan gudanarwa yanzu haka.
Shugaba Tinubu da tawagarsa sun sauka a filin jiragen sama na Ladoke Akintola da ke Ibadan ne da misalin ƙarfe 1:30 PM na rana inda Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo ya yi masa maraba.
Aminiya ta ruwaito cewa, tun kafin isowar Shugaba Tinubu aka fara gudanar da bukukuwan al’adun gargajiya da suka danganci miƙa sandar sarauta ga sabon Olubadan Oba Rashid Adewolu Ladoja.
Juma’a a Ibadan, babban birnin Jihar Oyo ya samu halartar manyan mutane da suka haɗa da Sarakuna da tsofaffin Gwamnoni da wakilan Majalisun Tarayya daga Jihohi daban daban na ƙasa.
Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar IIIda Alaafin na Oyo Oba, Abimbola Owoade da Soun na Ogbomoso Oba Ghandi Afolabi Olaoye suna daga cikin manyan Sarakunan da suka bayyana a zauren taro na Mapo da ke tsakiyar birnin Ibadan, inda ake yin wannan taro.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Oba Rashid Adewolu Ladoja
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sake kai hari a Kwara, sun sace mutum 11
’Yan bindiga sun yi garkuwa da aƙalla mutum 11 mazauna garin Isapa da ke kusa da Eruku a Ƙaramar Hukumar Ekiti ta Jihar Kwara.
Harin ya faru ne sa’o’i kadan bayan sakin wasu masu ibada da aka yi garkuwa da su suna tsaka da ibada a coci.
An haramta cin naman Kare da Kyanwa a Indonesia An sako ɗalibai 25 da ’yan bindiga suka sace a KebbiA cocin CAC da ke Ekuru, ana gudanar da bikin godiya domin murnar ’yantar da mambobi 18 da aka yi garkuwa da su kusan wata guda da ya gabata, sai ’yan bindiga suka kutsa suka yi garkuwa da mutum 38 bayan sun harbe uku har lahira.
Sabon harin, wanda ya faru da misalin ƙarfe 6:00 na yammacin Litinin, an ce ’yan bindiga kimanin 20 zuwa 30 ne suka kai shi.
Bayanai sun una cewa maharan su rika yin harbi ta ko’ina yayin da suke kutsa cikin garin, lamarin da ya sa mutane suka ranta a na kare.
Wata tsohuwa ta ji rauni sakamakon harbin kan mai uwa da wabi.
Wani jagoran al’umma da bai amince a bayyana sunansa ba, ya tabbatar da lamarin, inda ya ce: “Mutane 11 aka yi garkuwa da su, bakwai daga cikin su ’yan gida ɗaya. Waɗanda aka sace sun haɗa da mace mai juna biyu, masu shayarwa biyu da kuma kananan yara.”
Shaidar y ace sunaye mutanen sun hada da Talatu Kabiru, 20, Magaji, 6, Kande, 5, Hadiza, 10, Mariam, 6, Saima, 5, Habibat (mahaifiya), Fatima Yusufu (mahaifiya), Sarah Sunday, 22 (mai juna biyu), Lami Fidelis, 23 (uwa mai shayarwa) da kuma Haja Na Allah, ita ma uwa mai shayarwa.
Shaidun gani da ido sun ce ’yan bindigar sun bi wasu sassa na garin, inda suka bar alamun ramukan harsashin harbe-harbe a bangon gidaje da ƙofofi.
An gano harsashin bindiga AK-47 da aka harba daga wurare da dama bayan ’yan bindigar sun ja da baya tare da mutanen da suka yi garkuwa da su.
Lamarin ya haifar da tsananin tashin hankali a yankin da makotan garuruwa, yayin da jami’an tsaro da ’yan sa-kai ke ƙara ƙoƙari wajen gano maharan da ceto waɗanda aka sace.
Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kwara, Adekimi Ojo, ya tabbatar da lamarin ga yana mai cewa: “Eh, lamarin ya faru, amma ba zan iya cewa komai da yawa ba yanzu ba. Ina gab da shiga Isapa daga Ilorin. Zan ba da rahoto idan na isa.”
A yanzu haka dai Najeriya na fuskantar ɗaya daga cikin mafi munin matsalolin tsaro a tarihin ta. Hakan dai ya haifar da rufe makarantu da dama, musamman a Arewacin ƙasar.