FBI ta sanya la’adar N15m kan dan Najeriyar da take nema ruwa a jallo
Published: 25th, September 2025 GMT
Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka (FBI) ta sanya la’adar Dala 10,000, kwatankwacin Naira miliyan 15 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kama wani ɗan Najeriya mai suna Olumide Adebiyi Adediran.
Ana dai neman Olumide ne a Amurka ruwa a jallo bisa zargin aikata laifukan zamba da dama.
A cewar sanarwa da aka wallafa a shafin FBI a ranar Laraba, ana tuhumar shi da laifukan zamba a banki, zamba da takardun shaida, laifukan da ake zargin ya aikata a jihar Illinois tun shekarar 2001.
Adediran, mai shekaru 56, yana amfani da sunaye daban-daban kamar Kevin Olumide Adediran, Eric O. Williams, Maxo Alexandre, Olumide Adkins, da Edward N. Anderson.
Ana zargin ya yi ƙoƙarin cire kuɗi daga takardun banki na bogi da kuma amfani da bayanan sirri na ’yan ƙasar Amurka da aka sace don buɗe asusun banki da na katin bankin.
FBI ta ce Olumide ya tsere daga jihar Illinois a ƙarshen Disamban 2001, kafin fara shari’arsa.
A ranar 2 ga Janairu 2002, kotun tarayya ta fitar da sammacin kama shi kan karya sharuddan belinsa.
Sanarwar ta ce: “Ana neman Olumide Adebiyi Adediran kan karya sharuddan belinsa. A watan Agusta 2001, an zargi Adediran da shiga wani banki a Champaign, Illinois, inda ya yi ƙoƙarin karɓar kuɗi daga cek na bogi da aka ajiye.
“Haka kuma ana zargin ya yi amfani da bayanan sirri da aka sace na Amurkawa don buɗe asusun banki da na katin banki. Ya tsere daga yankin Central District na Illinois a ƙarshen Disamba 2001, kafin fara shari’arsa kan tuhumar zamba a banki, zamba da takardun shaida, da kuma zamba da katin banki.
“A ranar 2 ga Janairu 2002, kotun tarayya ta fitar da sammacin kama shi a Central District na Illinois, Illinois, bayan an tuhume shi da karya sharuddan belinsa.”
FBI ta bayyana cewa Adediran yana da alaƙa da yankin kudancin Florida kuma har yanzu yana cikin jerin mutanen da ake nema.
FBI ta ce, “FBI za ta bayar da lada har zuwa Dala $10,000 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kama da hukunta Olumide Adebiyi Adediran.”
FBI ta bukaci duk wanda ke da bayani kan inda yake da ya tuntubi ofisoshinta a Amurka ko ofishin jakadancin Amurka mafi kusa da shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dan Najeriya
এছাড়াও পড়ুন:
Barazanar Amurka Ta Kara Haraji Game Da Batun Ma’adanan Farin Karfe Ba Hanya Ce Mai Bullewa Ba
Ya kuma ce matakan takaita fitar da ma’adanan farin karfe da Sin ta dauka a baya bayan nan, ba su da alaka da kasar Pakistan. Yana cewa matakai ne da gwamnatin Sin ta dauka bisa doka da oda da nufin inganta tsarinta na fitar da kayayyaki. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA