Ana Hasashen Adadin Zirga-Zirgar Fasinjoji Yayin Hutun Bikin Tsakiyar Kaka Na Sin Zai Kai Biliyan 2.36
Published: 29th, September 2025 GMT
Ma’aikatar sufuri ta kasar Sin, ta ce adadin zirga-zirgar fasinjoji yayin hutun bikin tsakiyar kaka na Sin dake tafe nan da ‘yan kwanaki, zai kai kimanin biliyan 2.36.
Da yake karin haske kan hakan, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Lahadin nan, mataimakin ministan ma’aikatar Li Yang, ya ce yayin kwanaki takwas na hutun da za a fara tun daga ranar Laraba, za a samu karuwar tafiye-tafiye na yawon bude ido ko na ziyartar ‘yan uwa.
Li, ya kara da cewa, an yi kiyasin ganin tafiye-tafiye kimanin miliyan 295 a duk rana cikin kwanakin hutun masu zuwa, karuwar da ta kai kaso 3.2 bisa dari kan na shekarar 2024 da ta shude.
An kuma yi hasashen kaso kusan 80 bisa dari na jimillar tafiye-tafiyen za a yi su ne ta amfani da ababen hawa masu zaman kansu. (Mai fassara: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina
Kwamishiniyar Ilimi ta Jihar Gombe, Dokta Aishatu Umar Maigari, ta ce talauci da nuna bambanci na daga cikin manyan dalilan da ke hana yara mata damar samun ilimi a jihar.
Ta bayyana hakan ne a wajen bikin Ranar Yara Mata ’Yan Makaranta ta Duniya ta shekarar 2025, wanda Shirin AGILE tare da Access Initiative Africa da Nudge Initiative suka shirya a Gombe.
Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro ’Yan ta’adda sun kashe sojoji 4 a wani sabon hari a BornoA wajen bikin, Uwargidan Gwamnan Jihar Gombe, Asma’u Inuwa Yahaya, ta yaba da yadda gwamnatin jihar ke ƙoƙarin tabbatar da cewa ba a bar wata yarinya a baya wajen samun ilimi.
Ta ce Gwamnan jihar, ya bai wa ilimin yara mata muhimmanci, wanda hakan ya sa ake samu ƙaruwa yara mata da ke zuwa makaranta.
Kwamishiniyar, ta ƙara da cewa ma’aikatar ilimi tana aiki wajen samar da sabbin manufofi da tsare-tsare da za su taimaka wajen rage waɗannan matsaloli da tabbatar da damar ilimi ga kowa cikin adalci.
A nata jawabin, Kodinetan Shirin AGILE, Dokta Amina Haruna Abdul, ta ce bikin na bana an shirya shi ne don ƙarfafa gwiwar yara mata wajen ci gaba da neman ilimi duk da ƙalubalen da suke fuskanta.
Ta gode wa Uwargidan Gwamnan da ma’aikatar ilimi bisa goyon bayansu.
Haka kuma, Akawun Majalisar Dokokin Jihar Gombe, Barista Rukayyatu Jalo, ta shawarci yara mata da su dage wajen yin karatu, inda ta bayyana cewa ilimi ne hanyar da za ta gina rayuwarsa.
Wasu daga cikin ɗaliban da suka halarci bikin, sun bayyana farin ciki da godiya kan shirya taron saboda yadda ya ƙara musu ƙwarin gwiwa.
Ɗalibai da dama sun gudanar da muhawara da wasan kwaikwayo a wajen taron.