Tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka bisa jagorancin Adam Smith ta kammala ziyara a kasar Sin a jiya Alhamis 25 ga wannan wata, kafofin watsa labaru na kasa da kasa sun maida hankali sosai kan batun.

Kafin ziyarar tawagar, shugabannin kasashen Sin da Amurka sun zanta ta wayar tarho, da yin musayar ra’ayoyi kan dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka da batutuwan da suke sa lura tare, kana sun tsara taswira kan yadda za a raya dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kama a mataki na gaba.

Bisa wannan yanayi, ziyarar tawagar membobin majalisar wakilai ta kasar Amurka ta shaida muhimmiyar rawar manufofin da shugabannin kasashen biyu suka tsara, da ci gaba da karfafa mu’amalar dake tsakanin manyan jami’an kasashen biyu, wannan ne mataki mai muhimmanci wajen kiyaye dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka.

Farfesa na kwalejin nazarin dangantakar dake tsakanin kasa da kasa na jami’ar Renmin ta kasar Sin Diao Daming ya yi nuni da cewa, ziyarar tawagar membobin majalisar wakilai ta Amurka a kasar Sin a wannan karo ta taimaka wa membobin majalisar su kara sanin hakikanin halin kasar Sin, da kara fahimtar kasar Sin, ta haka za su nuna ra’ayi bisa tushe yayin da suke tattauna batutuwan dake shafar kasar Sin.

Kamar yadda kasar Sin ta jaddada a yayin tattaunawar, ana fatan majalisar wakilan Amurka za ta maida hankali ga kasar Sin da dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka yadda ya kamata, da sa kaimi ga yin mu’amala da hadin gwiwa a tsakaninsu, don taka muhimmiyar rawa wajen sada zumunta da samun bunkasa tare a tsakanin kasashen biyu. (Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka membobin majalisar a kasar Sin

এছাড়াও পড়ুন:

Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano

Zamu kawo muku cikakken bayani idan sun bayyana.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Rundunar Ƴansanda Ta Kama Gaggan Ƴan Fashi 9 A Kano October 13, 2025 Labarai Magance Bala’o’i: Gwamna Lawal Ya Jaddada Ƙudirin Gwamnatin Zamfara Na Ci Gaba Da Haɗin Gwiwa Da NEMA October 13, 2025 Labarai Ba Bu Dalilin Da ASUU Za Ta Fara Yajin Aiki, An Biya Duk Buƙatunsu – Ministan Ilimi  October 13, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Zargin Batanci: An Sasanta Da Malam Lawal Triumph Da Majalisar Shura Ta Kano
  • Dan Majalisar Tarayyar Kaduna ya bar Jam’iyyar PDP
  • Majalisar Shura ta fara ganawar sirri da Malam Triumph
  • Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh
  • Yanayin Sashen Samar Da Gidaje Na Sin Ya Kara Inganta Tsakanin 2021 Zuwa 2025
  • An Gudanar Da Taron Hadin Kai Na Raya Albarkatun Kasa Tsakanin Sin Da Mozambique
  • Li Qiang Ya Halarci Bikin Murnar Cika Shekaru 80 Da Kafuwar Jam’iyyar WPK Ta Koriya Ta Arewa
  • Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Iran Ya Ja Kunnen Amurka Kan Taba Jiragen Dakon Man Kasa
  • Majalisar Turai Ta Bukaci Kasashen Nahiyar Su Kakkabo Jiragen Yakin Rasha
  • Majalisa Na Duba Yiwuwar Amincewa Da Gudanar Da Zaɓen 2027 A Rana Ɗaya