Ba Za A Iya Dakile Ci Gaban Hakkin Dan Adam Na Xizang Da Kowace Irin Karya Ba
Published: 30th, March 2025 GMT
A bana aka cika shekaru 60 da kafuwar jihar Xizang mai cin gashin kanta ta kasar Sin. A ranar 28 ga watan Maris, wato ranar tunawa da ’yantar da miliyoyin bayi manoma a Xizang, gwamnatin kasar Sin ta fitar da wata takardar bayani mai taken “Ci gaban hakkin bil’adama a Xizang a sabon zamani”, wadda ta yi amfani da cikakkun bayanai na gaskiya don nuna yadda aka samu manyan sauye-sauye a jihar a cikin shekaru gommai da suka wuce.
“Ci gaba da aka samu a Xizang ya wuce yadda na yi zato, kuma mutane a nan suna rayuwa irin ta zamani sosai.” Wannan shi ne yadda babban dan jaridar kafar watsa labarai ta 24NewsHD ta kasar Pakistan Ali Abbas ya fada bayan ziyararsa a jihar. A cewarsa, karin mutane a duniya sun fahimci cewa, don neman kawo baraka ga kasar Sin ne wasu kasashen yammacin duniya suke kara wa miya gishiri a batun hakkin bil’adama a Xizang. Sannan game da batun ko an kiyaye hakkin bil’adama da kyau ko a’a a Xizang, bayanan sun riga sun ba da kyakkyawar amsa a kai, kana hakikanan labarun zaman rayuwar jama’ar jihar su ma sun bayyana gaskiya, don haka babu wata karya da za ta iya rufe ko kuma goge ainihin halin da ake ciki a jihar. (Mai fassara: Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Tinubu Ya Taya Amusan Da Gumel Murnar Samun Nasarori A Ɓangarori Daban-daban
Shugaban ya yaba da abinda ya kira kwarewa da juriya irin na Amusan, tare da cewa aikinta ya sake misalta irin daukakar da yan Nijeriya za su iya samu ta hanyar aiki tukuru da nuna kwazo, Tinubu ya yi fatan Gumel da Amusan su ci gaba da samun nasara a ayyukansu tare da ba su tabbacin gwamnati za ta ba su cikakken goyon baya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp