2025-11-27@23:00:39 GMT
إجمالي نتائج البحث: 205
«carar zakaran»:
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta samu nasara a wasan mako na 14 na Nigeria Premier Football League (NPFL), bayan da ta doke Ikorodu City da ci 2–1 a filin wasa na Muhammad Dikko, da ke birnin Katsina. Wannan ita ce nasara ta uku da Pillars ta samu a kakar bana, cikin wasanninta 14, inda ta yi kunnen doki uku, sannan ta sha kashi shida. ’Yan bindiga sun yi yi garkuwa da mutane 11 a Kwara Chelsea za ta kece raini da Barcelona a Gasar Zakarun Turai Kafin wannan wasan, Kano Pillars ta yi wasanni takwas a jere ba tare da samun nasara ba. Pillars ta zura kwallayenta ne ta hannun Rabiu Ali, wanda ya zura ta farko a...
Wata gobara ta tashi a sansanin ’yan gudun hijira na Mafa da Jihar Borno ta lalata matsugunan wucin gadi guda 40 tare da kayan abinci da sauran kayan gida. Kamar yadda rahoton ke nunawa cewar, lamarin ya faru ne da misalin karfe 11:20 na safiyar Laraba. An tuntuɓi hukumar kashe gobara ta tarayya da ta Jiha nan take, yayin da ƙungiyoyin sintiri ƙarƙashin jagorancin DPO na Mafa suka taimaka wajen daƙile cunkoson jama’a da kuma hana satar kayayyaki. Daga ƙarshe rahoton da ke garin na nuna cewar an kashe gobarar ba tare da an samu rahoton raunuka ko asarar rayuka ba. Har yanzu ba a tantance adadin kadarorin da suka lalace ba, kuma ana ci gaba da bincike kan musabbabin...
Wani magidanci tare da ɗaukacin iyalinsa huɗu sun rasu sakamakon wata gobara da ta tashi a sanadin kunna maganin sauro a layin Baba Impossible da ke Unguwar Kundila, da ke Ƙaramar Hukumar Tarauni a Jihar Kano. Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, ta tabbatar da tashin wutar da misalin ƙarfe 4:13 na Asubar ranar Laraba. NAJERIYA A YAU: Halin Kunci Da Matan Da Aka Yi Garkuwa Da Su Ke Tsintar Kansu A Ciki Kotu ta sanya ranar fara shari’ar shugabannin ƙungiyar Ansaru Mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya ce sun samu kiran wani ma’aikacinsu, HFS Abba Datti, game da gobarar. A cewarsa ba tare da ɓata lokaci ba suka tura jami’ansu daga hedikwatar hukumar zuwa wajen...
Shugaban ƙungiyar masu sayar da tsofaffin ƙarafa a jihar Gombe, A.A. Laja, ya ce gobarar da ta tashi a kasuwar tsofaffin ƙarafa da ke kasuwar katakon jihar ta jawo masa asara da ta kai sama da Naira miliyan 500. Lamarin ya faru ne a daren Laraba, inda wutar ta ƙone shaguna fiye da 30 da ke ɗauke da kayan kasuwancinsa. Sanatan Enugu ya mutu a Birtaniya ‘Yadda aka harbe mijina a gabana lokacin sace daliban Kebbi’ A.A Laja, wanda ya yi magana da wakilinmu jim kaɗan bayan aukuwar lamarin, ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 10 na dare, ta kuma ci gaba da ci har zuwa karfe 4:00 na Asuba, saboda rashin isowar jami’an kashe gobara cikin...
Wata mummunar gobara ta tashi cikin daren Laraba ta ƙone shaguna a kasuwar Katako da ke Gombe, lamarin da ya yi sanadin salwantar dukiya ta miliyoyin naira. Shaidu sun ce gobarar ta fara ne wajen misalin ƙarfe 1:00 na dare sakamakon zargin matsalar wutar lantarki, inda ake kyautata zato cewa an bar wasu na’urorin lantarki ne a kunne bayan an rufe kasuwar. DAGA LARABA: Hanyoyin Da Suka Kamata A Bi Wajen Ceto Daliban Kebbi Da Aka Sace Amurka za ta binciki zargin yi wa Kiristoci kisan kiyashi a Nijeriya ranar Alhamis Hakan a cewar shaidun ya haddasa tashin gobarar bayan wutar lantarki ta dawo. Gobarar dai ta ci gaba da ƙone shaguna da kadarori iri-iri, lamarin da ya jefa ’yan...
Gobara ta laƙume rayukan wasu yara biyu ’yan gida ɗaya a unguwar Rumuola da ke ƙaramar hukumar Obio/Akpor a Jihar Ribas. Bayanai sun ce ibtila’in ya auku ne da misalin ƙarfe 10 na dare a ranar Lahadi, lokacin da gobarar ta tashi a ɗaya daga cikin wasu ɗakunan haya da mahaifiyar yaran ta kulle ’ya’yanta huɗu ta tafi sayen kayan girki. Mayaƙan ISWAP sun kashe kwamandan soji a Borno ’Yan sanda sun kama ƙunshi 66 na Tabar Wiwi a Gombe A cewar mazauna yankin, cikin yaran huɗun, biyun da suka riga suka kwanta barci sun ƙone su kurmus, yayin da sauran biyun da ke farke suka samu damar tserewa. Aminiya ta ruwaito cewa, mazauna yankin da sun ankara da gobarar...
El-Rufa’i ya kara da cewa mutane amintattu za a ba su mukamai idan ADC ta samu nasarar kwace mulki a hannun APC a 2027, yana mai cewa cewa kashi 40 cikin dari na mukamai za su je ga matasa. Ya yi kira ga magoya bayansa da su kiyaye masu yaudara da ke kokarin raba kan jam’iyyar, yana cewa, “APC ba za ta bar ku ku tafi cikin sauki ba, ku yi hankali.” Haka kuma, ADC ta gudanar da taron masu ruwa da tsaki a Jihar Zamfara, wanda mataimakin sakataren gudanarwa na kasa na jam’iyya ya shirya, don karfafa hadin kai tsakanin ‘yan jam’iyya da kuma karfafa musu gwiwar yin rajista da samun katin zabe. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Tambarin Dimokuradiyya Rikicin...
Rundunar ’yan sandan Jihar Kaduna ta cafke wasu mutum uku da ake zargi da safarar bilAdama wadanda aka ceto yara 17 daga hannunsu a garin Zariya. Wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, DSP Mansir Hassan, ya fitar, ta bayyana cewa yaran da aka ceto ana zargin an shirya safarar su ne zuwa Abuja da wasu sassan ƙasar da ma ƙetare. An dakatar da Hakimi da Dagaci kan rikicin manoma da makiyaya a Gombe Atiku ya karyata ba sojan da ya yi takaddama da Wike kyautar motar SUV Sanarwar ta bayyana cewa “an tari hanzarin ababen zargin ne da misalin ƙarfe huɗu na yammacin ranar 12 ga watan Nuwamba. “A wannan lokaci ne jami’an sashen Ɗan Magaji da...
“Mun yi imani cewa ‘yan wasanmu tare da kwarewar da suke da ita, zai janyo wa Nijeriya abin alfahari, ba kawai a ranar Alhamis ba, har ma a duk tsawon wasannin share fagen da zamu buga”, hakan yasa muke da kwarin gwuiwar cewar kasarmu za ta iya samun tikitin shiga gasar cin kofin Duniya,” in ji Gusau. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Babu Wani Abu Kuskure Ga Sojan Da Ya Yi Sa-in-sa Da Ministan FCT – Matawalle November 13, 2025 Manyan Labarai Majalisar Tarayya Za Ta Binciki Masaƙa Ta Kaduna Da Sauran Gine-ginen Gwamnati 11,000 Da Aka Yi Watsi Da Su November 13, 2025 Manyan Labarai Lambar Yabo Da LEADERSHIP Ta Ba Mu, Ta Ƙara Zaburar Da...
A shekarar 2023, Ronaldo, wanda ke taka Leda tare da Al Nassr ta Saudiyya, ya tabbatar da maganar da ya yi na cewa, zai rataye takalminsa nan ba da jimawa ba, “Idan ina nufin nan ba da jimawa ba, watakila shekara daya ko biyu zan ci gaba da kasancewa a wasan,” in ji shi. Ronaldo wanda ya lashe kyautar Ballon d’Or sau biyar yana da burin buga Kofin Duniya na shida a shekara mai zuwa, ya kusa lashe kofin a shekarar 2006, lokacin da Portugal ta sha kashi a hannun Faransa a wasan kusa da na karshe, a halin yanzu, Portugal ba ta sami gurbi a gasar 2026 ba, wadda za ta gudana a Amurka, Kanada, da Mexico, amma...
Hare-haren daukan fansa da Iran ta kai wa haramtacciyar kasar Isra’ila ya yi sanadiyyar janyo hasarar dala miliyan 200 Harin da aka kai wa matatun mai na Haifa na ɗaya daga cikin ayyukan da Iran ta yi a matsayin ramuwar gayya ga harin da Isra’ila ta kai a lokacin yaƙin kwanaki 12. Shirin “Lambar” a cikin ɓangarensa na “Sa ido”, ya magance wannan aikin. Waɗannan matatun mai suna daga cikin muhimman wurare na dabaru a Isra’ila, waɗanda ke cikin ɗaya daga cikin muhimman tashoshin jiragen ruwa kuma suna aiki a matsayin babbar cibiyar jiragen ruwa da ke jigilar mai zuwa ƙasar. A cewar ƙididdiga da ƙayyadaddun fasaha, matatun mai na Haifa suna da ƙarfin samar da tan miliyan 9.8 a...
Sakamakon kwamitin, wanda ke dauke da kusan shafuka 40 ya bayyana shawarwari kan gyare-gyare da matakan da za a dauka na gaggawa. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Kano Na Tattauna Batun Fara Amfani Da Harshen Hausa A Wurin Koyarwa A Makarantu November 5, 2025 Labarai Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista November 5, 2025 Labarai Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio November 5, 2025
Kungiyar Likitoci Mata ta Najeriya (MWAN) reshen Jihar Gombe, tare da hadin gwiwar Hukumar Ci gaba ta Arewa maso Gabas (NEDC), za su gudanar da gwaji kyauta na gano cutar sankarar nono da ta mahaifa ga mata fiye da 500 cikin tsawon kwanaki uku. Wakiliyar kungiyar MWAN, Dr. Hauwa Saurayi, ce ta bayyana haka a hira da manema labarai a Gombe, a cikin shirin bikin Watan Wayar da Kan Jama’a game da Cutar Sankara. Ta ce an shirya gwajin ne domin inganta gano cutar tun da wuri da kuma bada magani cikin lokaci, kasancewar cancer na nono da na mahaifa su ne manyan cututtukan sankara da suka fi addabar mata. Dr. Hauwa Saurayi ta jaddada cewa gano cuta tun da...
Rahotanni sun nuna cewa shugaban kungiyar Ansarullah Abdul-malik al-houthi yayi gargadin cewa yankin yana gab da fuskantar gagarumin rikici da isra’ila da kasashen yamma a yanki, don haka yasha alwashin cewa tsayin dakar dakarun kasar yafi karfi fiye da baya kuma a shirye take ta kalubalanci duk wanda yayi mata shisshigi a nan gaba. Wadannan kalaman suna nuna irin yadda ake samun karuwar fadace-fadace a yammacin asiya yayinda kungiyoyin dake goyon bayan yan gwagwarmayar daga yaman da labanon ke ciin shirin ko ta kwana na yaki da isra’ila da kawayenta na kasashen turai, haka kuma jawabin ya jaddda irin dabarun yaki da kungiyoyin yan gwagwarmaya da isra’ila suka bi bayan yakin gaza da kuma sabunta kokarin sojojin Amurka a yankin...
Rahotanni sun bayyana cewa, wata gobara ta ƙone wani shagon Adidas Sports da ke cikin rukunin babban kantin nan na sayar da kayayyaki na Jabi Lake Mall, Abuja da tsakar daren Alhamis. Daily Trust ta ruwaito cewa, shagon ne kaɗai gobarar ta shafa. An kuma samu rahoton cewa, an baza jami’an kashe gobara daga Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya, da na Kamfanin Berger da na hukumar kashe gobara ta Abuja da kuma jami’an ’yan sanda zuwa wurin. Ƙasashe 12 da suka samu tikitin Kofin Nahiyyar Afrika na mata Gwamnan Bauchi na neman ƙirƙirar sabbin ƙananan hukumomi 29 A lokacin da Wakilin Daily Trust ya kai ziyara da safe zuwa wurin, an shawo kan gobarar. Wani ma’aikaci a shagon ya ce...
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba October 27, 2025 Manyan Labarai Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Da Burgediya Janar Yake a Matsayin Sarkin Ƙabilar Sayawa October 27, 2025 Manyan Labarai Shugaba Tinubu Ya Gana Da Sabbin Hafsoshin Tsaro October 27, 2025
Wannan tabbacin ya zo ne a daidai lokacin da farashin famfon mai ke canzawa a faɗin ƙasar, wanda tun daga kusan ₦189 a kowace lita a shekarar 2023 zuwa sama da ₦1,000, kafin ya daidaita tsakanin ₦800 da ₦900 a farkon shekarar 2025. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai An Zaɓi Birgediya Janar Yake A Matsayin Sarkin Sayawa Na Farko Duk Da Zanga-zanga October 27, 2025 Labarai Tsohon Gwamnan Jigawa, Lamido Ya Bayyana Aniyar Takarar Shugabancin Jam’iyyar PDP Na Ƙasa October 27, 2025 Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025
Tsohon gwamnan, wanda ya dade yana cikin jam’iyyar PDP kuma fitaccen mai fada a ji a cikin jam’iyyar, yana neman jagorantar jam’iyyar yayin da take shirin yin babban taronta na kasa. Ana sa ran jam’iyyar PDP, wacce ta mulki Nijeriya daga 1999 zuwa 2015, za ta zabi sabon Shugabanta na kasa da sauran shugabannin jam’iyyar a lokacin babban taron jam’iyyar da za a yi a Ibadan a jihar Oyo a watan gobe. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Sojoji Sun Kashe ‘Yan ta’adda 10, Sun Ƙwato Makamai A Borno October 27, 2025 Labarai Matasa 5 Sun Mutu A Hatsarin Jirgin Ruwa A Gombe October 27, 2025 Manyan Labarai Matatar Dangote Za Ta Faɗaɗa Ƙarfin Aiki Zuwa Ganga...
“Yayin da ake gudanar da samamen bisa ga bayanan sirri daga wasu mazauna garin Farin Ruwa da ke karamar hukumar Shanono, jami’an hadin gwiwa na rundunar yaki da ta’addanci ta rundunar da kuma jami’an rundunar da ke Shanono, sun gudanar da samamen na kwarewa a ranar Juma’a, 24 ga Oktoba, 2025, da misalin karfe 02:00 na dare. Hakan ta sa, an samu nasarar kama wasu mutane biyu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne,” in ji sanarwar. Kwamishinan ‘yansanda, CP Ibrahim Adamu Bakori, ya yaba wa al’ummar Farin Ruwa, yana mai bayyana yadda suka bayar da bayanan sirrin a matsayin muhimmin abu ga nasarar aikin. Ya bukaci mazauna yankin da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani...
Wannan nasara mai ban mamaki ta sa kungiyar Niger Tornadoes ta koma matsayi na biyu a teburin gasar, inda yanzu take da maki 17 a kasan Nasarawa United. Hakazalika, sakamakon ya bar Kano Pillars a cikin mawuyacin hali a gasar yayin da ta ke matsayi na 19 da maki 8 kacal. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Kamfanin Samar Da Kayayyakin Gida Na Mai Da Gas Na Shekarar 2025 Kamfanin GEIL October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ɗan Majalisa Na Shekarar 2025: Benjamin Okezie Kalu October 26, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Banki Na Shekarar 2025 Bankin Providus October 25, 2025
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Kiwon Lafiya Gwarzuwar Ma’aikaciyar Jinya Ta Shekarar 2025: Misis Mabel Ijeoma Duaka October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Mai Koyar Da Wasanni Na Shekarar 2025 Justine Madugu October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Lafiya Na Shekarar 2025 Dakta Seidu Adebayo Bello October 25, 2025
“Ban taba tunanin zan zama taurariya a duniya ba.” Daga Yobe Zuwa Fagen Duniya An haife ta a Jihar Kano kuma ta tashi a Yobe, labarin Nafisa ba shi da wuya kamar yadda yake da ban sha’awa. Mahaifinta ya rasu tun tana jaririya, kuma mijin mahaifiyarta mai suna Alhaji Yusuf Umar Kaigama ya rene ta, wanda ya dasa mata dabi’u na tarbiyya da azama. Tana kuma ɗauke da tsatson sarautar zuriyar sarakuna biyu masu daraja ta masarautar Kano, wato Sarkin Kano Ibrahim Dabo da Sarki Abdullahi Maje Karofi. Amma bayan jinin sarautar da take ɗauke dasu, yunwar ta na neman ilimi ya sa ta zama daban. A yanki da matsalar staro ta yi katutu wanda kuma yake dakushe duk wani...
Ba wai nasara kawai ba ce; saƙo ne, cewa masu horarwa na Nijeriya na iya kai wa matakan duniya, kuma ƙwarewar gida har yanzu tana da muhimmanci. Hanyar Da Ba A Yawanta Binta Labarin Madugu ba na nasara cikin dare ɗaya ba ne, yana yi ne sannu a hankali da ƙwarewa mai ɗorewa. Daga farkon ayyukansa na horarwa ya fara da Adamawa United da ƙungiyar mini-football ta Nijeriya, zuwa aiki a matsayin mataimakin mai horarwa a gasar WAFCON huɗu (2012, 2014, 2018, 2022), ya gina suna saboda natsuwa, sassaucin dabaru, da basira. Lokacin da ya karɓi cikakken jagorancin Super Falcons a shekarar 2024, da yawa sun yi shakku kan iya cika takardun zama wasu ƙwararrun masu horarwar na ƙetare da...
A shekarar 2008, Skales ya shiga gasar Zain Tru Search kuma ya lashe yankin ArewaTsakiya na gasar. A lokacin, ya riga ya saki waƙarsa ta farko “Must Shine”, wacce ta samu yawan fitowa a tashoshin Rhythm FM a Lagos, Jos, da Abuja. Ana tuna shi da burinsa na zama babban mawaƙi da sha’awar ilimi, ya ɗauki sunan mataki SKALES, wanda ke nufin “Seek Knowledge, Acƙuire Large Entrepreneurial Skills”. Daga baya ya koma Lagos, inda ya sanya hannu kan yarjejeniyar rikodi da Empire Mates Entertainment (E.M.E.) a shekarar 2009. Waƙarsa ta shekarar 2009 “Heading for a Grammy”, wadda take waƙar ƙarfafa kai, ta samu wahayi ne daga ƙalubalen rayuwarsa a wancan lokaci. Skales yana ɗaya daga cikin manyan mawaƙan da suka...
Sauyin shugabannin tsaro dai ya nuna matakin da Tinubu ke ɗauka wajen sake fasalin tsaro, amma kuma ya buɗe sabon babi na tattaunawa kan yadda ake kula da tsofaffin hafsoshin da suka ba ƙasa hidima tsawon shekaru. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwarzon Ma’aikacin Banki Na Shekarar 2025 Dakta Tony Okpanachi October 25, 2025 Manyan Labarai Muna Duba Ƙudirin Ƙirƙiro Jihohi 55 – Barau Jibrin October 25, 2025 Manyan Labarai Gwarzon Shugaban Kamfani Na Shekarar 2025 Gbenga Olu Komolafe October 25, 2025
Har ila yau, an kama wasu mutane biyu da ake zargi a kauyen Doka da ke Kachia, kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, yayin da ake zarginsu da safarar bindigogi kirar AK-47 guda uku ga ‘yan bindiga a cikin wata mota kirar Golf. Da yake mayar da martani kan wannan ci gaban, Gwamna Uba Sani ya yabawa hukumar DSS kan nasarar da ta samu, inda ya jaddada aniyar gwamnatinsa na kawar da miyagun laifuka a fadin jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas October 23, 2025 Manyan Labarai Gwamna Uba Sani Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Yada Labarai Ahmed Maiyaki October 22, 2025...
Shugabannin jam’iyyar PDP Na Arewa Sun Amince Da Turaki A Matsayin Ɗan Takarar Shugabancin Jam’iyyar Na Ƙasa
Sanarwar da aka fitar a karshen taron ta bayyana cewa, matakin na daga cikin kokarin da ake yi na karfafa hadin kan jam’iyyar da tabbatar da daidaiton wakilcin yanki a cikin tsarin shugabancin jam’iyyar PDP. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai Gwamnatin Tarayya Ta Jajantawa Waɗanda Fashewar Tankar Mai Ta Rutsa Da Su A Neja October 23, 2025 Manyan Labarai Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Naira Biliyan 2.5 Na Aikin Haƙo Uranium, Mai Da Iskar Gas October 23, 2025 Labarai NUJ Reshen Kano Ta Taya Ahmed Mu’azu Murna Kan Naɗin Da NAHCON Ta Yi Masa October 23, 2025
Wannan tsarin na taimaka wa yara su samu ilimi mai zurfi da zai ba su damar daidaita da tsarin rayuwarsu na yau da kullum. Makarantun suna da ɗakunan kwana, gidajen malamai, wutar lantarki mai amfani da hasken rana, rijiyoyin burtsatse, kujeru, kayan karatu, da cibiyar koyon sana’o’i kamar ɗinki, sassaƙa, kwamfuta, da sauransu. Haka kuma, gwamnan ya gyara Ma’aikatar Harkokin Mata da Ci gaban Jama’a ta Jihar Zamfara da kuma Kwalejin Fasaha da Kimiyya ta Zamfara (ZACAS). A ɓangaren lafiya kuwa, gwamnatinsa ta gyara asibitoci da cibiyoyin lafiya da dama a faɗin jihar. Don rage mace-macen mata da jarirai a yayin haihuwa, ya ɗauki ƙarin ma’aikatan lafiya, tare da samar da magunguna da kayan aiki, tare d harkar kyautata kiwon...
Wasu direbobi sun bayyana cewa tsarin ya taimaka wajen tabbatar da tsaro, ko da yake fyana jinkirta tafiya. Wasu kuma sun ce farashin sufuri ya ɗan ƙaru sakamakon sabon tsarin. Mutane da ƙungiyoyin farar hula sun yaba da nasarar, amma sun buƙaci gwamnati ta tabbatar da cewa yaran da aka ceto sun samu kulawa, ilimi, da sake gana su da iyayensu. Dakta Sabo ya ce hukumar sufuri za ta ci gaba da haɗa kai da jami’an tsaro tare da faɗaɗa ayyukanta domin tallafa wa tattalin arziƙin jihar. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Mutane 3,433 Sun Rasa Rayukansu A Haɗurra 6,858 A Cikin Watanni Tara October 20, 2025 Manyan Labarai Kotu Ta Yanke Hukuncin Kisa Ga Mutane Biyu Da...
A daren Lahadi a ƙasar Chile, ƙasar Morocco ta kafa tarihi bayan da ta doke Argentina da ci 2-0 a wasan ƙarshe na gasar Kofin Duniya na ƴan ƙasa da shekaru 20, wanda hakan ya bai wa ƙasar damar lashe wannan kofi a karon farko a tarihin ta. Yassir Zabiri, wanda ke taka leda a ƙungiyar FC Famalicao ta ƙasar Portugal, shi ne gwarzon wasan bayan da ya ci ƙwallaye biyu a ragar Argentina tun a farkon rabin lokaci. Nasarar ta tabbatar da ƙarfin Morocco a gasar, inda ta doke ƙasashe masu ƙarfi irin su Koriya ta Kudu, da Amurka, da Faransa a hanyarta ta zuwa wasan ƙarshe. Wang Yi Ya Gana Da Takwaransa Na Kasar Morocco Morocco Ta Shigar...
Don haka, an nada “tsohon kaftin din kungiyar kuma mataimakin koci, Gambo Muhammad, tare da mai horar da masu tsaron gida, Suleiman Shuaibu, su maye gurbin wadanda aka sallama na dan wucin gadi. Bugu da kari, Koci Garzali Muhammad (Kusa) daga Junior Pillars zai taimakawa wadanda aka nada na dan wucin gadin”. LEADERSHIP ta ruwaito cewa, kungiyar mai taken ‘Sai Masu Gida’ tana fama a ‘yan makonnin nan. Hukumar kwallon kafa ta Nijeriya ta kuma ci tarar kungiyar tarar kudi sama da Naira miliyan 9 biyo bayan rikicin da ya ɓarke a yayin da suke karawa da wata kungiya a filin wasa na Sani Abacha. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Wasanni Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A...
Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa, wanda ake zargin wanda aka ce shi ne Shugaban kungiyar ‘yan acaɓa reshen Ejiba, ya amsa cewa, ya siyo ƙwayoyin ne a wani shagon sayar da magunguna da ke Egbe domin kai wa abokan hulɗar sa da ke cikin dajin. Babban sakataren yaɗa labarai na shugaban karamar hukumar Yagba ta yamma, Adeyemi Babarinde Sunday, ya ce an kuma samu wanda ake zargin da kuɗi har ₦600,000, wanda ake zargin kudaden hada-hadar ta’addanci ne. ShareTweetSendShare MASU ALAKA Labarai An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza October 19, 2025 Labarai Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani October 19, 2025 Manyan...
Saboda haka, an samu labari daga bangaren Obi cewa, tsohon dan takarar shugaban kasa ba za yi zaben fid da gwani ba da Atiku. Sai dai kuma, sakataren yada labarai na jam’iyyar ADC, Bolaji Abdullahi ya ki cewa uffan kan jita-jitan da ke cewa jam’iyyar ta yanke shawarar gudanar da zaben fid da gwani, wanda hakan ya saba wa tsammanin wasu mambobin, musamman daga bangaren Obi. A cewar Bolaji, a halin yanzu ADC ba ta mai da hankali kan wane zai tsaya takara a karkashin tutan jam’iyyar ADC a zaben 2027 ba. “A halin yanzu dai, babu wanda aka tattaunawa kan cewa shi ne sahihin dan takara ko kuma za su gudanar da zaben fitar da gwani. Idan mun kai...
Sashen Cinikayyar Kamfanonin Sarrafa Hajoji Na Sin Ya Bunkasa Da Kaso 4.7 Bisa Dari Cikin Watanni Tara Na Farkon Shekarar Nan
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Nazarin CGTN: Jamaar Duniya Sun Yi Ammana Amurka Za Ta Fi Jin Jiki Daga Yakin Haraji October 15, 2025 Daga Birnin Sin Shugaban Zaunannen Kwamitin Majalisar Wakilan Jama’ar Sin Ya Gana Da Mukaddashin Shugaban Majalisar Dattawan Kasar Liberia October 15, 2025 Daga Birnin Sin An Bude Bikin Baje Kolin Kasuwanci Na Kasa Da Kasa Na 138 A Guangzhou October 15, 2025
Gwamnan Kaduna Ya Taya Al’Amin Murnar Nasarar Lashe Gasar Ƙirƙirar Fasaha Ta Duniya A Ƙasar Birtaniya
An tallafawa ‘yan Kasuwa ƙanana, kuma an rage fitar da hayakin da ke gurɓata muhalli a faɗin nahiyar Afirka. Gwamna Uba Sani ya bayyana wannan nasara a matsayin babbar gagarumar bajinta da kuma abin alfahari ga Jihar Kaduna da NIjeriya baki ɗaya, yana mai jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da zuba jari a fannin kimiyya, fasaha da kirkire-kirkire domin bunƙasa tattalin arziki da bai wa matasa dama. “Wannan nasara ta sake tabbatar da ƙwarewar ƙirƙira da ƙarfin tunanin matasan Jihar Kaduna. Muna gina tattalin arzikin da ke dogaro da kirkira wanda ke daraja ra’ayi tare da haɓaka baiwa” in ji Gwamna Uba Sani. “Daga ajujuwa zuwa manyan matakan duniya, matasan Kaduna suna jagorantar makomar...
A zaman na ranar Talata, lauyan masu shigar da kara, Salisu Muhammad-Tahir, ya shaida wa kotun cewa biyu daga cikin wadanda ake tuhumar, Abubakar da Odlyne, ba a samu gabatar da su a gaban mai sharia ba duk da kokarin tilasta musu halartar zaman. Muhammad-Tahir ya ce “Mun yi iya bakin kokarinmu don tabbatar da kawo su gaban mai shari’a, amma muna neman afuwar kotu,” in ji Muhammad-Tahir, inda ya bukaci alkalin da ya dage sauraron karar tare da tsare Ogugua a gidan yari har sai an gabatar da wadanda ake nema. Lauyan wanda ake kara, Gideon Uzo, ya roki kotun da ta bar wanda yake karewa ya ci gaba da zama a hannun hukumar hana fataucin mutane...
Bugu da kari, an rufe shafukan hakar ma’adanai haramtacce 98 a fadin kasar. “An kiyasta cewa Nijeriya na asarar kusan Dala biliyan 9 a kowace shekara sakamakon haramtacciyar hakar ma’adanai. Wannan sata ta albarkatunmu da ya kamata ta bunkasa kasarmu ta wuce kima, kuma lokaci ya yi da za a kawo karshensa,” in ji Abdulraheem. A cewar sa, kwamitin na da alhakin hana asarar kudaden shiga, tabbatar da gaskiya da adalci a harkokin hakar ma’adanai, da tabbatar da cewa dukiyoyin ma’adanin kasar suna ba da cikakken gudunmawa ga ci gaban tattalin arziki. “Yayin da muke ci gaba, daya daga cikin manyan manufofin wannan kwamitin shi ne hana asarar kudaden shiga da haramtacciyar hakar ma’adanai da ayyukanta ke...
Gwamnatin tarayya ta yi asarar jimillar gangar danyen mai miliyan 13.5 wanda kudinsa ya kai dala biliyan 3.3 sakamakon sata da fasa bututun mai tsakanin shekarar 2023 zuwa 2024, in ji wata kungiya mai fafutukar kare masana’antu ta Nijeriya (NEITI). Sakataren zartarwa na NEITI, Dokta Ogbonanya Orji, ne ya bayyana hakan a Legas a taron kungiyar masu ba da rahoto kan makamashi ta Nijeriya (NAEC) na 2025 a Legas ranar Alhamis. Ya koka da cewa, rashin gaskiya da rikon amana ne ya dabaibaye masana’antar mai da iskar gas, yana mai cewa akwai bukatar yin gaskiya da aiwatar da sabon tunani na fasaha wajen tafiyar da harkar mai da iskar gas a kasar. Orji ya lura cewa, kudaden da aka yi...
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya kiyasta cewa Najeriya ta yi asarar kimanin dala biliyan 10, kwatankwacin Naira tiriliyan 14.5 sakamakon rikicin Boko Haram a yankin Arewa maso Gabas. Wakiliyar UNICEF a Najeriya, Wafaa Saeed, ta bayyana hakan a Maiduguri ranar Laraba yayin ƙaddamar da wani shirin farfaɗo da rayuwar yara da rikici ya shafa ta hanyar ba su horo da tallafi. Falasdinawa na murna da tsagaita wutar hare-haren Isra’ila a Gaza Majalisa ta yi watsi da zargin Amurka na yi wa Kiristoci kisan gilla a Najeriya An wakilta Saeed ta hannun Manajan Kare Yara na UNICEF, Shah Mohammad Khan, inda ta ce rikicin da ya daɗe ya rage girman tattalin arzikin ƙasar, ya kuma lalata...
Lokacin da mai gabatar da shirin, Seun Okinbaloye, ya tambaye shi ko ya damu saboda yawancin ‘yan ƙabilar Ibo na goyon bayan Obi, Kalu ya cd, “A’a, kawai ban son yin magana a kansa.“Idan kana son na tattauna a kan Peter Obi, to ka gayyace mu duka mu biyun mu zauna a tattauna ta awa biyu; kai za ka zauna a tsakiya, shi a gefe ɗaya, ni kuma a ɗaya gefen. Sai mu tattauna.”“Peter Obi ba jagorana ba ne. Ni ne ɗan siyasa mafi shahara daga yankin Kudu maso Gabas. Na taɓa lashe jihohi biyu a ƙarƙashin jam’iyyar PPA, kuma na taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa.“Kuri’u na miliyan 4.9 na samu a shekarar 2007 har yanzu suna nan. Jam’iyyata ta...
Ana fargabar mutuwar wasu mutane masu ababen hawa da wasu da ke hanya sakamakon faɗuwar wata tankar mai da ke ɗauke da mai a ranar Juma’a ta kuma tada gobara a hanyar Abeokuta zuwa Sagamu a Jihar Ogun. An samu rahoton cewa tankar ta faɗi ne ta gefenta sannan man da ke ciki ya zube a kan titin Abeokuta zuwa Kobape-Siun-Sagamu a daidai wurin musayar hanyar. Boko Haram ta wuce yadda mutane ke tsammani — Jonathan NAFDAC ta lalata magungunan jabu na N15bn a Oyo Kakakin Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa na Jihar Ogun, Babatunde Akinbiyi a cikin sanarwar da ya fitar, ya ce lamarin ya janyo tashin gobara. Ya kuma ɗaura laifin haɗarin a kan gudun wuce ƙima...
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, har yanzu bai ayyana cewa ko zai tsaya takarar shugaban ƙasa a 2027 ba. Yayin da wasu ’yan siyasa kamar Peter Obi da Rotimi Amaechi suka nuna sha’awar tsayawa takara, Atiku ya ce “lokaci bai yi ba” domin yanke hukunci. Isra’ila ta kame dukkan jiragen ruwan da ke koƙarin kai kayan agaji Gaza An naɗa Remi Tinubu Sarauniyar Yaƙin Akko Kwanan nan, wasu rahotanni sun bayyana cewa Atiku ya faɗa wa BBC Hausa cewa zai bai wa matashi damar tsayawa takara. Wannan ya haifar da cece-kuce a kafafen sada zumunta. Amma hadiminsa, Paul Ibe, ya ce ba a yi wa maganganun Atiku kallo na tsanaki ba, an fahimce su ba daidai ba. Ibe, ya...
Sule ya bayyana cewa, “ilimi shi ne abu mafi mahimmanci da gwamnatinsa ta fi mayar da hankali akai, hakan ne ya sa aka ware kashi 36 cikin 100 na kasafin kuɗin jihar na shekarar 2025 ga sashen ilimi”. Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa ta dawo da tallafin karatu na ƙasashen waje, inda a halin yanzu take ɗaukar nauyin ɗalibai 155 da ke karatu a fannoni daban-daban a ƙasashe daban-daban na duniya. Ya ƙara bayyana cewa, gwamnatin jihar na ɗaukar nauyin ɗaliban jinya da kuma wasu a jami’o’i daban-daban a faɗin ƙasar. “Mun kuma biya kuɗin rajistar jarabawar kammala sakandire ta kasa (NECO) ta shekarar 2025 ga ɗalibai sama da 24,000 na makarantun sakandare na gwamnati, domin...
Kwamitin ladabtarwa na Hukumar Ƙwallon Ƙafa FIFA ya sanar da matakin da ta ɗauka a kan tawagar ƙwallon Afirka ta Kudu, inda ta rage mata maki, sannan ta ci ta tarar kuɗi. Kwamitin ya bayyana cewa ƙasar ta karya doka ne ta hanyar amfani da ɗan wasa da bai cancanci buga wasan ba, a fafatawar da suka yi da Lesotho, inda Teboho Mokoena ya taka leda a ranar 21 ga Maris, 2025. FIFA ta ce amfani da ɗanwasan ya saɓa da sashe na 19 da kundin laifuka na hukumar, sannan ya kuma saɓa da sashe na 14 na kundin shirye-shiryen farko-farko na gasar cin kofin duniya na shekarar 2026. FIFA ta ce bayan nazarin binciken da aka gudanar, ta ƙwace...
Sabuwar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barau FC daga jihar Kano ta samu nasararta ta farko a gasar Firimiyar ta Nijeriya (NPFL) bayan doke Kun Khalifa daga jihar Imo a wasan mako na 5 da aka buga a birnin Aba. Wannan shi ne karon farko da ƙungiyar ta samu nasara tun bayan haurowarta gasar. A minti na 14 da fara wasan ne Kun Khalifa suka fara zura ƙwallo a ragar Barau FC. Sai dai minti biyu kacal bayan haka, Yahaya Ibrahim ya farke wa Barau FC kwallo, wanda ya buɗe musu ƙofar dawowa cikin wasan. Mataimakin Shugaban BUK Ya Buƙaci ‘Yan Siyasa Da Su Yi Koyi Da Tallafin Karatu Na Barau Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibril Ya Yi Alhinin Rasuwar...
Dakarun Operation Haɗin Kai su kama wani mutum da ake zargi yana kai wa Boko Haram man fetur a Jihar Borno. Wanda aka kama, mai suna Thomas James, mai shekaru 54, an cafke shi ne ranar 23 ga watan Satumba a kusa da sansanin Forward Operating Base da ke Ngwom. PENGASSAN ta tsunduma yajin aiki kan korar ma’aikata a kamfanin Dangote Jami’ar Bayero ta sallami ɗalibai 57 kan maguɗin jarrabawa An same shi da kwalabe 23 na man fetur da ya ɓoye cikin jaka a lokacin da yake tafiya daga Maiduguri zuwa Gamboru Ngala. Bincike ya gano cewa yana yi wa Boko Haram safarar man fetur, sai dai wannan karon an yi nasarar kama shi. Wanda dai ba shi ne...
Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Sakandare a Nijeriya (NECO) ta jaddada cewa Jihar Kano ce ta fi kowace jiha samun nasara a sakamakon jarrabawar bana, tana mai ƙaryata rahoton da jaridar Premium Times ta fitar, wanda ya ce Jihar Abia ce ke kan gaba. A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa rahoton da jaridar Premium Times ta wallafa ba shi da tushe balle makama, inda ta bayyana shi a matsayin mai cike da ruɗu da rashin inganci. Makon gobe za a dawo jigilar jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna — NRC Tun daga shekarar 1899 Faransa take haddasa mana rikici — Nijar “Rahoton ya ce bayan bincike da kuma nazarin bayanan sakamakon jarrabawar bana, Premium Times ta tabbatar...
Kasashen Afirka ta Kudu da Sin sun kaddamar da wani sabon yunkuri na zurfafa dangantakar tattalin arziki, inda Beijing ta yi alkawarin zuba jari a fannin hakar ma’adinai, makamashi, da ababen more rayuwa. Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Pretoria ke fuskantar matsanancin matsin lamba daga sabbin harajin da Amurka ta sanya mata wanda ke yin barazana ga damar da ta ke da ita a karkashin dokar bunkasar Afirka da damammaki (AGOA). Taron bunkasa harkokin kasuwanci na kasashen Afirka ta Kudu da Sin karo na 9, wanda aka gudanar a ranar Talata, ya jaddada aniyar kasashen biyu na karfafa hadin gwiwar tattalin arziki. A wajen taron, shugaban kungiyar tattalin arziki da cinikayya ta kasar Sin da Afirka ta...
Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta zargi Faransa da ɗaukar shekaru tana haifar da rikice-rikice da rashin tsaro a ƙasar da maƙotanta na yankin Sahel, tun daga shekarar 1899. Firaministan Nijar, Ali Lamine Zeine, ne ya yi wannan furuci ranar Asabar yayin gabatar da jawabi a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 (UNGA 80) da ke gudana a birnin New York na ƙasar Amurka. Ɗalibi ya kashe malaminsa har lahira a Kuros Riba Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki a Zamfara Lamine Zeine ya zargi Faransa da yin amfani da ƙungiyoyin “ta’addanci” domin tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasarsa da maƙotanta na yankin Sahel, inda ya buƙaci mahukunta a Paris su “tuna tare da ɗukar alhakin laifukan...
Gwamnatin Jamhuriyyar Nijar ta yi zargin cewa tun daga shekarar 1899 Faransa take fafutikar tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasar da maƙotanta na yankin Sahel. Firimanistan Jamhuriyyar Nijar, Ali Lamine Zeine, ya yi wannan caccakar ce kan Faransa a ranar Asabar yayin da yake gabatar da jawabi a Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA 80) da ke gudana a birnin New York na Amuka. Ɗalibi ya kashe malaminsa har lahira a Kuros Riba Ma’aikatan jinya sun tsunduma yajin aiki a Zamfara Lamine Zeine ya zargi Faransa da yin amfani da ƙungiyoyin “ta’addanci” domin tayar da rikici da haddasa rashin tsaro a ƙasarsa da maƙotanta na yankin Sahel, inda ya buƙaci mahukunta a Paris su “tuna tare da...
Haka kuma, ya fadi zaben shugaban kasa na 2015 ga dan takarar jam’iyyar APC, Marigayi Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a watan Yuli na wannan shekara. Akwai zazzafar muhawara kan dokar da ta bai wa Jonathan damar sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027, tsohon gwamnan Jihar Jigawa kuma daya daga cikin shahararrun jiga-jigan jam’iyyar PDP, Sule Lamido, a kwanan nan ya bayyana Jonathan a matsayin mafi kyawun dan takarar shugaban kasa na PDP a zaben 2027. Lamido ya kuma yi kira da shugabancin jam’iyyar na kasa su yi kokarin tabbatar da an tsayar da shi takarar shugaban kasa a 2027. Jonathan ya ce, “Dimokuradiyya a Nahiyar Afirka na fuskantar babbar barazana, sannan ta kusa da rushewa sai dai masu...
Yadda Sauye-Sauyen Da Aka Yi A Fannin Mai Da Iskar Gas Suka Samar Da Gagarumin Ci Gaba A Wannan Shekarar
Shugaban a kasidar da ya gabatar a wajen taron mai taken: “Ingantattun Sauye-Sauyen da Nijeriya ta kirkiro da su domin cin gajiyar albarkatun da ke a Man Fetur da Iskar Gas”, ya jaddada mahimmancin da ke a fannin Makamashi, musamman wajen kara bunkasa tattalin arzikin kasa da kuma yadda Afirka, za ta amfana. Ya ci gaba da cewa, sabon sauyen da aka samar a kasar nan a karkashin dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021 ta samar da sabon sauyi, a bangaren gudanar da shugabanci na gari. Shugaban ya kara da cewa, Hukumar musamman a karkashin shugabancin shugaba Tinubu, ta kara zagayewa wajen sanya ido sosai a fannin na sarrafa Mai da Iskar Gas. Ya ce, Hukumar kusana a cikin shekaru...
Wannan domar dai an dogara da kundin tsarin aikin gwamnatin Tarayya bisa ga sashe na 10(1) na dokar Ilimi ta (National Minimum Standards and Establishment of Institutions) ta shekarar 1985. A baya-bayan nan, an gano cewa sama da mutum 22,500 sun yi amfani da takardun bogi daga jami’o’i marasa izini a Benin da Togo daga shekarar 2019 zuwa 2023. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Rundunar Sojoji da Ma’aikatan Kwalejin Horasda Kananan Hafsoshin Soji Ta Jaji Sun Tsara Shirin Samar Da Fahimta Tsakanin Sojoji Da Fararen Hula.
Rundunar Sojoji da Ma’aikatan Kwalejin Horasda Kananan Hafsoshin Soji Ta Jaji Sun Tsara Shirin Samar Da Fahimta Tsakanin Sojoji Da Fararen Hula. Rundunar Sojoji da ma’aikatan kwalejin su ta Jaji, ta kammala wani shiri na musamman wanda ke nuna wa ‘yan jarida da sauran masu halartar atisaye, sani da gogewar al’amuran yau da kullum a irin salon rayuwar sojan da ke cikin rukunin. A wata sanarwa da kakakin kwalejin, Laftanar Kanar Victor Olukoya ya fitar, ya ce an shirya wannan horon ne da nufin samar da kyakkyawar fahimta da hadin gwiwa tsakanin sojoji da masu ruwa da tsaki na farar hula domin samun kyakkyawar alakar aiki wadda a karshe za ta taimaka wajen magance matsalolin tsaron kasa cikin...
Wata kotu ta musamman a Coimbatore da ke kasar Indiya, ta yanke wa wani dan Najeriya mai suna Samson Chukwunonso hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari kan laifin safarar miyagun kwayoyi. Jaridar Times of India ta ruwaito cewa lamarin ya faro tun a watan Yuli na shekarar 2012, lokacin da jami’an hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta India (NCB), reshen Chennai, suka kama wasu fakiti guda uku a ofishin aika sakonni. An kama ɗan sandan bogi a Kano Sanata Natasha ta koma Majalisar Dattawa A cikin fakitin, an gano tabar wiwi mai nauyin kilo 1.195 da methaqualone giram 200, wanda darajarsa ta haura kimanin Dalar Amurka 240,000 a kasuwar duniya. Bincike ya gano cewa fakitin na da...
Hukumar Ƙididdigar a Najeriya, NBS ta ce arzikin cikin gida da ƙasar ke samu ya ƙaru da kashi 4.23 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2025 da muke ciki. Sabbin alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa an samu ƙarin kashi 3.48, idan aka kwatanta da daidai wannan lokacin a 2024, lamarin da hukumar ta ce alamu ne na bunƙasar tattalin arzikin ƙasar. An gudanar da bikin ɗaga tutar Falasɗinu a Birtaniya CAC ta soma yi wa kamfanoni rijista da fasahar AI NBS ta ce fannin aikin gona ne kan gaba wajen samar da ƙaruwar arzikin ƙasar, wanda ya ƙaru zuwa kashi 2.82 saɓanin kashi 2.60 a 2024. Sauran fannonin da hukumar ta ce an samu ci...
Haddadiyar Kungiyoyin Makiyaya na kasashen Africa (CORET) ta bayyana cewa an samu karin yawan ɗalibai a makarantun makiyaya cikin watanni goma da aka fara shirin ciyar da ɗalibai. Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana haka a taron kwana ɗaya da aka gudanar a Kaduna domin ƙara wa ma’aikata da abokan hulɗarsu ƙwarewa kan harkar ciyar da ɗalibai. Taron ya mayar da hankali ne wajen duba nasarorin da aka samu cikin watanni goma tun lokacin da aka fara shirin a Ladduga, Karamar Hukumar Kachia ta Jihar Kaduna, da kuma Maigatari a Jihar Jigawa. Babban Sakataren CORET, Muhammed Bello Tukur, ya bayyana cewa shirin ya shafi makarantun makiyaya kawai a jihohin Jigawa da Kaduna. Ya...
A ɓangare ɗaya kuma Turkiyya na ƙara nuna damuwa bayan harin da Isra’ila ta kai a birnin Doha. Mai magana da yawun ma’aikatar tsaro ta Turkiyya, Rear Admiral Zeki Akturk ya yi gargaɗin cewa “Isra’ila za ta iya faɗaɗa hare-harenta baya ga Ƙatar. Za ta iya ingiza yankin baki ɗaya cikin bala’i.” Mece ce shawarar da Masar ta bayar? Shawarar da Masar ta bayar ya ƙunshi samar da tsarin haɗe ayyukan sojin ƙasa da na sama da cibiyoyin tsaro, tare da haɗe cibiyoyin horaswa da ayyukan soji. Haka nan kuma ƙasashen ne za su yanke hukunci kafin amfani da dakarun bayan tattaunawa a tsakaninsu. Kafar yaɗa labarai ta Al Akhbar da ke Lebanon ta ce a ƙarƙashin tsarin, Masar ta...
Iran Ta Yi Nasarar Gwajin Tauraron Dan’adam ” Nahid 2″ Da Zai Samar Wa Yankunan Karkara Hanyar Sadarwa Ta “Internet”
Ministan sadarwa na Iran Sitar Hashimi ya bayyana cewa, an sami nasara a gwajin da aka yi na sabon tauraron dan’adam, mai suna “Nahid 2” wnada aikinsa shi ne samar da hanyoyin sanarwa na internet masu nagarta. Ministan sadarwar ya kuma ce dukkanin bangarorin tauraron dan’adam din sun yi aiki yadda ake so a yayin gwajin da hakan yake a matsayin wani ci gaba a fagen sadarwa a Iran. Har ila yau ministan Sadarwar Sitar Hashimi ya kuma ce; A tsakanin kauyuka 10,000 da ba su da hanyoyin sadarwa, yanzu an rage su da 2000, kuma ana ci gaba da aiki tukuru domin isa ga kauyunan da suke nesa,masu wahalar zuwa. Ministan sadarwar na Iran ya kuma kara da cewa;...
Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi. Ministan Noma Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta Jihar Jigawa. Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya. Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa....
Don tunkarar zaɓen 2027, wata Ƙungiya a ƙarƙashin inuwar Tinubu/Barau/Atah Movement a ranar Alhamis a Kano ta shirya taron addu’o’i na musamman domin samun nasara ga shugaban Ƙasa Bola Tinubu da Sanata Barau Jibrin. Taron addu’ar wanda ya samu halartar Malaman addinin Musulunci da magoya bayan jam’iyyar APC daga Ƙananan hukumomin Jihar 44, an gudanar da shi ne a Gidan Baballiya Kurna da ke Ƙaramar hukumar Fagge. Likitoci sun yi barazanar sake tsunduma yajin aiki An saki fursunonin siyasa 52 a Belarus A yayin taron addu’o’in malaman sun kammala karatun Alkur’ani mai girma tare da gabatar da addu’o’i na musamman kan takarar Tinubu a wa’adi na biyu da kuma burin Barau ya zama Gwamna a 2027. Malaman sun kuma yi...
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba Duk shekara rayuka da dukiyoyi na kara salwanta sakamakon ambaliyar ruwa. Duk da jan kunne da hukumomi a matakai daban-daban keyi, rayukan mutane da dukiyoyi na kara salwanta. NAJERIYA A YAU: Tasirin Takaddamar NUPENG Da Dangote A Kan Tattalin Arzikin Najeriya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari ne kan rayukan da suka salwanta a damunan wannan shekarar. Domin sauke shirin, latsa nan
“Wannan matakin ya zama dole don dakatar da saran gandun daji, kare muhalli, da tabbatar da ɗorewar albarkatun ƙasa,” in ji Dokta Hashim. Ya yi gargaɗin cewa, duk wanda ya karya doka zai fuskanci hukunci mai tsauri. “Za a tsaurara doka, tare da biyan tarar ₦500,000 da kuma yiwuwar ɗauri a gidan yari saboda amfani da injin sare bishiya ba tare da izini ba, da kuma tarar ₦250,000 kan kowace bishiya da aka sare ba bisa ka’ida ba. “Haka kuma za a umurci waɗanda suka aikata laifin da su sake dasa bishiyar sannan kuma za a ƙwace injin,” in ji shi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban...
Ya yaba da jajircewar Gidauniyar Abdullahi Maikudi, yana mai kira ga sauran masu kudi da kungiyoyi su yi koyi da wannan aiki na alheri. Ya kara da cewa a matsayinsa na dan arewa, ba zai daina fafutukar ganin matasa sun samu damar da za ta inganta rayuwarsu ba. A yayin taron, daliban da aka dauki nauyin karatunsu sun bayyana farin ciki da godiya ga gidauniyar, inda suka yi alkawarin jajircewa a wurin karatunsu don su dawo su yi wa al’umma hidima. Taron ya kasance cike da nishadi, addu’o’i da kuma kira ga hadin kai wajen gina al’umma ta hanyar ilimi. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura...
Kwanan baya, kafofin watsa labarai na kasa da kasa sun mai da matukar hankali kan bikin tunawa da cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya, wanda aka yi a birnin Beijing na kasar Sin a ranar 3 ga wata. Kana, kafofin watsa labarai da dama na kasashe daban daban sun rika amfani da kalmar “Zaman lafiya” a lokacin da suke watsa labarai kan wannan gagarumin biki. Yakin duniya na biyu ya bakanta ran bil Adama, kuma kasar Sin ta cimma nasarar yaki da mamayar dakarun kasar Japan bayan al’ummomin kasar sun shafe tsawon shekaru 14 suna yaki, lamarin da ya ba da muhimmiyar gudummawa ga...
Gwamnatin Saudiyya ta sanar da sanya tarar kuɗi kan masu aikata ayyukan da suka shafi rashin ɗa’a a cikin al’umma, musamman a lokutan salla, domin kare mutunci, tsaro da kuma zaman lafiya. Sabbin matakan, wanda za a fara aiwatarwa nan take, sun shafi masu sanya kaya marasa mutunci a bainar jama’a, da masu kunna kiɗa lokacin salla, da masu bahaya ko zubar da shara a wuraren da doka ta haramta. Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 13 a Borno Hisbah ta kama mai safarar mutane da mata 12 A cewar sabuwar doka, duk wanda aka kama da kunna kiɗa a lokacin salla zai biya tara ta Riyal 1,000 (kimanin Naira 390,000) a karon farko, kuma idan aka sake kama shi, tarar...
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani da ake zargi da safarar mutane (wanda aka sakaya sunansa) a wani wurin garejin motoci tare da wasu mata 12 da ake zargi da safarar mutane da ke shirin tafiya Legas. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mataimakin Kwamandan Hukumar ta Hisbah, Sheikh Mujahideen Aminuddeen. Ganawa da Tinubu: Buƙatun Gwamnonin Arewa maso Gabas Matasa sun kashe ’yan bindiga 6 sun sha alwashin kare kansu Sanarwar ta bayyana cewa, jami’an rundunar sun kama mutumin ne a wani garejin motoci da ke kan titin Zariya. Hukumar ta bakin mataimakin ta bayyana cewa, jami’an Hisbah ƙarƙashin jagorancin OC Muhammad Bashir na garejin motoci sun kama wakilin safarar wanda aka ce ya fito daga Jihar...
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani da ake zargi da safarar mutane (wanda aka sakaya sunansa) a wani wurin garejin motoci tare da wasu mata 12 da ake zargi da safarar mutane da ke shirin tafiya Legas. Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mataimakin Kwamandan Hukumar ta Hisbah, Sheikh Mujahideen Aminuddeen. Ganawa da Tinubu: Buƙatun Gwamnonin Arewa maso Gabas Matasa sun kashe ’yan bindiga 6 sun sha alwashin kare kansu Sanarwar ta bayyana cewa, jami’an rundunar sun kama mutumin ne a wani garejin motoci da ke kan titin Zariya. Hukumar ta bakin mataimakin ta bayyana cewa, jami’an Hisbah ƙarƙashin jagorancin OC Muhammad Bashir na garejin motoci sun kama wakilin safarar wanda aka ce ya fito daga Jihar...
A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya kuma umarci da a maido da babban daraktan yada labarai, Mista Ayo Adewuyi ya kammala wa’adinsa na ragowar shekaru uku, wanda zai kare a shekarar 2027. Shugaba Tinubu ne ya nada Adewuyi a shekarar 2024. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdolrahim Mousavi ya bayyana cewa, rundunar sojin saman kasar Iran a matsayinta na bangaren da ke sahun gaba na kare ikon sararin samaniyar kasar, ya rataya a kansu wajen ci gaba da kara kokarinsu na bunkasa tsaon sararin samaniyar kasar, domin tabbatar da cewa an dakile duk wata barazana ta makiya a kan akasar. A cikin sakon da ya aike na ranar tsaron sararin sama ta kasa, Janar Mousavi ya yi tsokaci kan yadda yanayin tsaro na yanki da na duniya ke ciki, inda ya bayar da misali da irin abubuwan da al’ummar Iran suka samu a tsawon shekaru 8 a bangaren ayyukan tsaro da kariya, wanda kuma ya tabata a yakin...
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Sanadiyyar ambaliyar ruwa a gonaki amfanin gona na miliyoyin Naira ne suka salwanta inda ɗaruruwan filayen noma suka shefe da ruwa a Jihar Taraba. Kodayake, ba a bayyana ko an sako ruwa daga Logdo Dam ba ne daga jamhuriyar Kamaru ba, amma kogin Benuwe da ke Taraba ya yi ta malala daga gaɓarsa wanda ya yi sanadin ambaliya da lalata ɗaruruwan filayen noma. ACF ta yi Allah-wadai da rushe kasuwar Alaba Rago Gwamnatin Gombe da Rotary sun yi shirin rage mutuwar mata da yara Daily Trust ta gano cewa ruwan ya fara ƙaruwa a kogi a ’yan kwanakin da suka gabata, kuma a yanzu kogin ya yi ta malala a gefan koguna inda ya haddasa ambaliya a faɗin jihar. Ambaliyar...
Jimilar Darajar Hada-Hadar Shige Da Fice A Fannin Bayar Da Hidimomi Ta Kasar Sin Ta Kai Yuan Tiriliyan 3.9 A Rabin Farko Na Shekarar Bana
Bikin CIFTIS na bana, zai kunshi nune-nune daga kasashe, da hukumomin kasa da kasa sama da 70. Kuma kusan kamfanoni 2,000 ne suka shirya shiga bikin a zahiri. (Safiyah Ma) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Yakin duniya na II abu ne da ya keta kasashe da iyakoki da launin fata, wanda a karshe ya kawo hadin kai tsakanin kasa da kasa domin wanzar da zaman lafiya da ci gaban duniya. Shekaru 80 bayan samun nasarar yaki da masu danniya, ya kamata a yi waiwaye, a nazarci nasarar da aka samu da kyar, da tsamo hikimomi da dabaru da ma hanyoyin karfafa gina duniya cikin kawanciyar hankali da lumana. Yayin da al’ummomin kasashen duniya ke ganin wasu kasashe na kokarin lalata wannan nasara, ya zama wajibi a tsaya tsayin daka wajen bijire musu, don ganin ba a bar su sun mayar da hannun agogo baya ba. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya...
A ranar 27 ga watan nan na Agusta, za a bude cibiyar tattarawa da watsa labarai game da bukukuwan cika shekaru 80 da samun nasara a yakin turje wa harin Japan da karshen yakin duniya na II. Cibiyar wadda take hotel na Beijing Media Center, za ta bayar da shaidar watsa labarai da shirya damarmakin hirararki ga ‘yan jarida na kasar Sin da na ketare. (Fa’iza Mustapha) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dakarun Kare Juyin Juya Halin Musulunci na Iran sun bayyana cewa: A shirye suke su tunkari duk wata barazana da makarkashiyar ‘yan sahayoniyya da Amurka Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fitar da sanarwa a ranar 16 ga watan Agusta na tunawa da dawowar fursunonin da aka ‘yantar zuwa mahaifar ta daular Musulunci. Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Fursunonin da aka ‘yantar madaukaka, sune ainihin bayyanar gwagwarmaya da tsayin daka na ruhi da kuma bege na dabaru. A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar 16 ga watan Agusta na bikin tunawa da dawowar ‘yantattun fursunoni (fursunonin yakin shekara ta 1980-1988 a yakin da aka kakaba kan Iran), da tunawa da yakin kwanaki 12 da...
Majalisar dokokin jihar Kano ta karbi karin kudirin kasafin kudi na shekarar 2025 daga bangaren zartarwa na jihar domin tantancewa. Bukatar, wacce aka mika ta wata wasika daga bangaren zartarwa, ta nemi amincewar majalisar ta kara kasafin kudi naira biliyan 169,522,463,294.82 domin daukar muhimman ayyukan raya kasa a fadin jihar. Kakakin majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore ya bayyana cewa hukumar zartaswa na kokarin ganin an kara wa kasafin kudin domin gudanar da ayyuka masu ma’ana da za su shafi rayuwar mazauna. Bayan sun yi duba, ‘yan majalisar sun mika kudirin dokar ga kwamitin kasafin kudi na majalisar domin tantancewa da daukar matakin da ya dace. A wani labarin kuma, Majalisar ta kuma samu takarda daga bangaren...
Wani dattijo ya rasu a sakamakon hatsari da gobarar tankokin sakon iskar gas da ta auku a yankin Zariya da ke Jihar Kaduna. Aliyu Ramalan Babbale mai shekara sama da 70 ya rasu ne a lokacin da yake ƙokarin tsira da ransa a sakamakon hatsarin tankokin a safiyar ranar Litinin. Dattijon ya gamu da ajalinsa ne a kan hanyarsa na zuwa gona, lokacin da wasu tankokin dakon gas biyu suka kama da wuta bayan su gogi juna. Mai auran babban ’yar marigayi Malam Abdullahi Magaji, ya yi wa Aminiya bayanin yadda lamarin ya faru, akan rasuwar marigayin. ya ce, “A jiya da safe marigayin yana kan babur ne a kan hanyarsa na zuwa gona, sai waɗannan motocin ɗakon man gas...
Ali Akbar Velayati mashawarcin jagoran juyin juya halin Musulunci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan harkokin kasa da kasa ya tabbatar da cewa “Jamhuriyar Musulunci tana adawa da shirin kwance damara na kungiyar Hizbullah” yana mai jaddada cewa Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar kasar Labanon da kuma gwagwarmayarsu. Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Tasnim na Iran a ranar Asabar, Velayati ya ce bijiro da batun kwance damarar Hizbullah ba sabon abu ba ne a Lebanon. “Kamar yadda wannan yunƙurin ya gaza a baya, wannan karon ma ba za iyi nasara ba, kuma ‘yan gwagwarmaya zasu ci gaba da yin tsayin daka a kan manufofinsu da kuma dakile wannan makirci,” in ji shi. Ya...
Wannan hukunci ya fito daga kwamitin ɗa’a da ladabtarwa na UEFA, kuma zai fara aiki nan take a wasan Barcelona na gaba a Turai. Barcelona za ta fara sabuwar kakar wasa ne da RCD Mallorca ranar Asabar, 15 ga watan Agusta. Za su ci gaba da fafutukar lashe kofuna a ƙarƙashin sabon kocinsu, Hansi Flick. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Ya kuma lura da cewa, tattaunawa da ‘yan bindiga a wasu jihohin suka yi ya kara ta’azzara satar shanu, inda ya ce, Sam hakan, ba za a amince da shi ba. Dangane da ta’azzarar rashin tsaro, Gwamna Bago ya ce, za a nemi taimako daga shugaba Bola Tinubu da mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun jaddada cewa: Duk wata barazana ga tsaron Iran za ta fuskanci kakkausan martani mai zafi fiye da tunani Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran sun fitar da sanarwar cikan kwanaki 40 da shahadar shahidan Iran a lokacin wuce gona da iri na yahudawan sahayoniyya da Amurka, inda suka jaddada cewa: Duk wata barazana ga tsaro da yankin kasar Iran za ta fuskanci kakkausar martani da ya zarce tunanin makiya, kuma zasu kasance mafi tsanani fiye da abin da ya faru gamakiya da amsu kiran yaki a martanin alkawarin gaskiya na uku. A cikin wata sanarwa da Dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran suka fitar a cikan kwanaki...
Hukumomi sun ce wannan kame na daga cikin ƙoƙarin hana Boko Haram samun kayan aiki da kuɗaɗe a yankin Arewa maso Gabas. Yanzu haka an killace wanda ake zargin, kuma ana ci gaba da bincike a kansa. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
Gobara ta ƙone gidan Barden Bauchi Hakimin Ƙasar Lere, Alhaji Sulaiman Muhammad da ke unguwar Gwallaga a cikin garin Bauchi. Sa’in Tafawa Balewa Mallam Yunusa Ado ya tabbatar da faruwar lamarin, da cewa “Wannan gobara ta auku ne akamakon kawo wutan lantarki da hantsi ranar Litini 4/8/2025 lokacin Hakimin na Fadarshi dake garin Zwall.” Mallam Yunusa ya ce, “Gidan ya ƙone ƙurmus, an yi asarar dukiya mai tarin yawa amma an yi sa’a da hatsin ne ya faru, amma ba a samu asarar rai ba, kuma babu wanda ya jikkata. Ya bayyana cewa makwabta da zuwan jami’an sun taimaka an aka fitar da motar da ke garejin zuwa waje, amma an tafka asara. Sa’in yace “Muna addu’ar Allah Ya Maida...
Shima da yake gabatar da nasa jawabin, shugaban jam’iyyar APC magoya bayan Aminu Sani Jaji a Zamfara, Honorabul Lawalli Attahiru Dogon Kade, ya bayyana dan majalisar a matsayin Mutum jajirtacce mai hannun kyauta da taimakon jama’a, inda ya ce mutum irin Aminu Sani Jaji ake nema a matsayin Gwamnan Zamfara, domin shi kadai ne zai kai jihar ga tudun mun tsira. Lokacin da ya ke zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala taron, Honorabul Aminu Sani Jaji, ya gode wa al’ummar Zamfara bisa nuna kauna da yarda da suka yi mishi, inda ya sha alwashin yi musu sakayya akan haka. “Dukkanin abubuwan da muke yi muna yin su ne domin al’umma, kuma jama’ar nan ita taga dacewa...
Mai Martaba Sarkin Dutse, Dr Hameem Nuhu Muhammadu Sunusi ya kaddamar da rabon zakkar kudi ta shekarar musulunci ta 1446 a gundumar Yayari dake Karamar Hukumar Buji. A jawabin sa, Mai Martaba Sarkin ya ja hankalin al’umma da su ci gaba da fitar da hakkin Allah domin samun makoma a nan duniya da kuma gobe kiyama. Ya nuna gamsuwa da nasarorin da Gundumar ta samu wajen tattara zakka a masarautar sa. Daga bisani ya karrama Hakimin Yayari, Alhaji Garba Muhammad da Dagaci da kuma Mai Unguwar cikin garin Yayari. A jawabin sa, Sa’in Dutse, Mallam Mahmud Yunusa yace gundumar Yayari ce ta zo na 1 a tattara zakkar kudi yayin da Gundumomin Gantsa da Fagam suka zo na...
Nijeriya, wadda take ta daya a jerin ƙasashen da suka fi iya ƙwallon mata a Afirka, ta zura ƙwallon da ta ba ta nasara ne a gab da tashi wasa a karawarta da Afirka ta Kudu a wasan kusa da na ƙarshe. A yanzu za a iya cewa Nijeriya ta cimma burinta na ‘Mission ɗ’, wato lashe kofin a karo na 10 a tarihi kuma ta ci gaba da jan zarenta na tawagar mata wadda babu kamarta a wannan nahiyar. Nijeriya ta ƙara kafa wani tarihin kasancewar ita ce ta farko da ta lashe sabon kofin na gasar bayan sauya shi da aka yi daga wanda aka saba amfani da shi a baya. A ƙarshen wasan Rasheedat Ajibade ta Nijeriya...
“Kiyasin ƴan Nijeriya miliyan 20 ke rayuwa da cutar hanta, kuma mutum miliyan 18.2 sun kamu ne da cutar rukunin B, sannan wasu mutum miliyan 2.5 sun kamu da cutar rukunin C. Abin takaici, ƴan Nijeriya 4,252 ne ke mutuwa a duk shekara sakamakon ciwon hanta da aka kasa maganceta ke haifarwa,” ya shaida. A jawabinsa na fatan alkairi, mai riƙon muƙamin wakilin hukumar kula da lafiya ta duniya (WHO) a Nijeriya, dakta Aleɗ Gasasira, ya yi kira ne ga gwamnatin tarayya da ta tashi tsaye wajen yin na mijin ƙoƙari kan cutar hanta, yana mai cewa cutar tana shafar miliyoyin jama’a a ƙasar nan. Gasasira, wanda ya samu wakilcin dakta Mya Ngon, a faɗin ofishin WHO da ke Nahiyar...
Umarnin NYSC ta amince da sanya siket ga mata masu hujjar sanya wa saboda addininsu. Umarnin NYSC ta dawo da su ta ‘yan matan da suka shigar da ƙarar tare da ba su takardar shaidar kammala NYSC. Kotun kuma ta bayar da umarnin bai wa kowacce daga cikinsu kuɗaɗe har ₦500,000 a matsayin diyya saboda tauye musu ‘yancin su. Kotun ta kuma bayyana cewa cin zarafi da muzantawar da suka fuskanta daga hannun jami’an NYSC ya ci karo da ‘yancinsu na yin addini da bayyana shi a aikace. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake...
Da safiyar yau Litinin ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya gudanar da taron manema labarai, bisa taken “Cimma burikan da aka tsara domin neman bunkasa tattalin arziki da zaman takewar al’umma a tsakanin shekarar 2021 zuwa shekarar 2025”. A yayin taron, jami’in babbar hukumar buga haraji ta kasar Sin ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2021 ya zuwa yanzu, tattalin arzikin kasar Sin ya bunkasa bisa shirin da aka tsara, kana, bisa hasashen da aka yi. Sakamakon haka, jimillar haraji da kudaden da hukumomin buga haraji sun karba ta zarce kudin Sin Yuan tiriliyan 155, adadin da ya kai kaso 80 bisa dari na yawan kudaden shiga na kasar Sin. Cikin adadin, kudin haraji zai kai sama...
Kwanan nan jam’iyyar PDP ta gudanar da taron kwamitin zartarwa karo na 100 da aka gudanar ranar 30 ga Yuni, PDP ta warware rikicin da ya dade yana ci mata tuwo a kwarya na batun mukamin sakataren jam’iyyar na kasa wanda ta tabbatar da Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar. Duk da wannan warware batun, Atiku da wasu magoya bayansa sun fice daga jam’iyyar sakamakon rashin warware rikicin gida na jam’iyyar. A ranar 1 ga Yuli, Atiku da Peter Obi da Rotimi Amaechi da Nasir El-Rufai, da wasu sun kulla hadaka a karkashin jam’iyyar ADC, sun ce sun yi wannan hadakar ne domin kalubalantar APC a zaben 2027. A matsayin wani bangare na wannan yunkurin hadin gwiwa, sun nada...
Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (4)
Hikimar Rashin Hade Farkon Shekarar Musulunci Da Tarihin Manzancin Annabi (SAW) Masu karatu har yanzu dai muna kan bayani game da abubuwan da suka sa Sahabbai ba su kafa tarihin kirgen shekarar musulunci ba da wasu manyan alherai na Musulunci, sai suka zabi Muharram ta zama farkon shekarar tare da lakaba mata shekarar Hijirah. A makon da ya gabata mun yi bayani kan hikimar ware farkon shekarar daga watan Rabi’ul Auwal zuwa watan Muharram saboda girman haihuwar Manzon Allah (SAW). A yau kuma, za mu ci gaba da bayani a kan ware kirgen farkon shekarar daban da ranar da aka fara aiken Manzanci ga Annabi (SAW). Tun ana sauran shekara uku Manzon Allah (SAW) ya cika shekara 40 da...
An sami hatsarin tashin gobara a cikin wani rumbun ajiyar makamai a garin Mu’arrah dake gundumar Idlib ta Arewa, wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar mutane da dama. Majiyar lafiya ta kiwon kasar Syria ta bayyana cewa; Mutane 2 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 70 su ka jikkata sanadiyyar fashewar rumbun makamai a garin Mu’arrah Masrin. Hukumar agjin gaggawa ta kasar Syria ta ce; Har yanzu babu cikakken dalili akan abinda ya haddasa wannan gobarar ta Mu’arrah Msarin. Ma’aikatan kwana-kwana sun nufi wurin da gobarar ta tashi domin kashe wuta da kuma dauke mutanen da su ka jikkata.
Jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara ta zabi Hon. Kamilu Sa’idu (Wamban Kasuwar Daji) a matsayin dan takararta na Majalisar Dokokin Jihar Kaura Namoda ta Kudu da za a yi ranar 16 ga Agusta, 2025. A wata sanarwa da Sakataren Yada Labarai na Jam’iyyar APC na Jihar, Yusuf Idris Gusau ya fitar, ya ce Kamilu ya fito ne ba tare da hamayya ba bayan janyewar wasu ‘yan takara uku Bashir Muhammad Madaro (Walin Kurya), Anas S/Fada, da Alhaji Ashiru Hamisu Habibu—a lokacin zaben fidda gwani na jam’iyyar da aka gudanar a makarantar firamare ta Kasuwar Daji. Sanarwar ta ce, ‘yan takarar ukun sun sauka ne domin nuna goyon bayansu ga Kamilu Sa’idu inda suka yi alkawarin samun nasararsa da...
Ba laifi idan an yi murna ta shigar sabuwar shekarar Musulunci. Ba za a bi na wadanda za su bidi’antar da abin ba, domin hatta murnar haihuwar Manzon Allah (SAW) sun ce bidi’a ne. Har kai kanka ma za su iya ce maka bidi’a, saboda ba ka zo a zamaninsa ba. Masu wannan fahimtar Malamai sun ce ba wai suna nufin a koma wa Sunnar Manzon Allah ba ne, suna so ne a koma wa zamanin Annabi (SAW), ka ga ke nan sai mu ajiye su motoci da sauran kayan kere-kere na fasaha sda ake amfani da su yanzu har da su lantarki da su jirgin sama duk a ajiye, a koma amfani da su rakuma da dawaki da jakuna....
Shugaban Kungiyar Harka Islamia a tarayyar Najeriya Sheikh Irahim Zakzaky ya taya mutanen kasar murna saboda nasarar da suka samu kan HKI da kuma Amurka a yakin kwanaki 12 a cikin watan da ya gabata. Ya ce wannan nasarar bata takaita da mutanen kasar Iran kadai ba , hada har da al-ummar Musulmi da kuma da kuma masu sun yenci a ko ina suke. Ya kuma yaba da yadda gikuwan nmalamai na kasar Iran suka sami nasarar kare kasar daga mafi yawan hare-haren HKI a kan kasar. Ya bayyana cewa Iran ta sami nasara a kan kasashen yamma da makamai wadanda suka fi nasu karfi da inganci, har’ila yau sun sami nasara a kan ma;aikatan yahudawan da suke taimaka masu...
Maraba Da Shekarar Hijirah Ta 1447: Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar (1)
Lallai wannan kalanda ana ce mata ta Musulunci; gaskiya ne, ta Musulmi ce tsantsa sannan kuma ta duk halitta ce domi duk halitta suna amfani da wannan, ko sun sani ko ba su sani ba. Sai dai kawai, mu a cikin ibadojinmu Addininmu Balarabe ne kuma Larabawa da wata suke yin kirgensu, kuma shi ne ya dace da halittar Dan Adam, mun gode Allah. Muna kira ga daukacin al’ummar Musulmi kowa ya yi tanadi na musamman kar ya bari a bar shi a baya, a bana idan Allah ya kai mu watan Rabi’ul Auwal maulidin da za a yi shi ne zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa. Yadda abin yake shi ne, idan ka dauki...
Rundunar ’sanda ta jihar Delta ta ja kunnen matasan jihar a kan yin shigar banza, inda ta ce duk wanda aka kama za a iya cin shi tarar da ta kai ta naira 50,000. A cikin wata sanarwa da Kakakin rundunar a jihar, SP Bright Edafe ya fitar ranar Talata, ya ce yin shigar banzan ya saba da dokar hana cin zarafin mutane ta (VAPP). Ko ɗaya Buhari bai yi wa takarar Tinubu zagon ƙasa ba – Garba Shehu Za mu shige gaba idan aka dawo da tattauna shirin nukiliyar Iran — EU Kazalika sanarwar ’yan sandan ta nuna bacin rai game da shigar banza da matasa a jihar suka runguma. “Akwai wasu daga cikin dokokin da aka kafa da...
Sin Za Ta Gabatar Da Shagulgulan Al’adu Na Bikin Cika Shekaru 80 Da Samun Nasarar Yaki Da Zaluncin Japanawa
Ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin zai gudanar da taron manema labarai a ranar Alhamis mai zuwa, da misalin karfe 10 na safe domin yin bayani kan shagulgulan al’adu da za a yi na bikin cika shekaru 80 da samun nasarar yakin turjiyar jama’ar kasar Sin kan zaluncin Japanawa da kuma yakin duniya na biyu. Jami’ai daga ma’aikatar al’adu da yawon bude ido da na hukumar gidan rediyo da talabijin ta kasar, da mataimakin shugaban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG), da shugaban gidan adana kayan tarihi na yakin turjiyar jama’ar kasar Sin kan zaluncin Japanawa, za su halarci taron manema labarun. Za su yi wa manema labarai karin haske kan wani baje koli mai...