Kwanan baya, kafofin watsa labarai na kasa da kasa sun mai da matukar hankali kan bikin tunawa da cika shekaru 80 da cimma nasarar yakin da Sinawa suka yi da mamayar dakarun kasar Japan da yakin duniya na kin tafarkin murdiya, wanda aka yi a birnin Beijing na kasar Sin a ranar 3 ga wata. Kana, kafofin watsa labarai da dama na kasashe daban daban sun rika amfani da kalmar “Zaman lafiya” a lokacin da suke watsa labarai kan wannan gagarumin biki.

Yakin duniya na biyu ya bakanta ran bil Adama, kuma kasar Sin ta cimma nasarar yaki da mamayar dakarun kasar Japan bayan al’ummomin kasar sun shafe tsawon shekaru 14 suna yaki, lamarin da ya ba da muhimmiyar gudummawa ga cimma nasarar yakin duniya na kin tafarkin murdiya.

Bugu da kari, wani muhimmin darasi da aka koya daga yakin shi ne, dole ne a tsaya tsayin daka wajen neman ci gaba ta hanyar zaman lafiya. Haka kuma, a halin yanzu da ake fuskantar sauye-sauye a duniya, shugaba Xi Jinping ya gabatar da ra’ayin kiyaye dauwamammen yanayin tsaron duniya cikin hadin gwiwa, kuma bisa dukkan fannoni, wanda hakan ya ba da amsar kasar Sin game da yadda za a warware matsalar rashin tsaro daga tushe.

Dukkanin bil Adama na fuskantar makoma iri daya, ba za mu iya shimfida zaman lafiya a duniyarmu ba, har sai dukkanin kasashe da kabilu su girmama juna, da yi wa juna adalci da kuma taimakawa juna. Ya kamata mu kawar da harkokin da za su haddasa yake-yake daga tushe, domin magance faruwar abubuwa masu bakanta rai da suka taba aukuwa a tarihi. (Mai Fassara: Maryam Yang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa

A cewarsa, ta hanyar wadannan shirye-shirye, kasar Sin ta nuna goyon baya mai dorewa ga kasashe masu tasowa kuma tana ba da gudummawa mai ma’ana ga ci gaban duniya a karkashin tsarin hadin gwiwar kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)

 

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Daga Birnin Sin Xi: A Shirye Sin Take Ta Hada Hannu Da Canada Wajen Mayar Da Dangantakarsu Bisa Turbar Da Ta Dace October 31, 2025 Daga Birnin Sin Xi Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Kolin Shugabannin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC October 31, 2025 Daga Birnin Sin Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare October 31, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
  • An Bude Sabon Babin Huldar Sin Da Koriya Ta Kudu
  • Sin: Katsalandan Cikin Harkokin Kamfani Da Netherlands Ta Yi Ya Kawo Tsaiko Ga Tsarin Masana’antu Da Samar Da Kayayyaki Na Duniya
  • An Gudanar Da Taron Tattaunawa Na Duniya Kan Kirkire-Kirkire Da Bude Kofa Da Ci Gaba Na Bai Daya A Nijeriya
  • Gwamna Uba Sani Ya Bayyana Tsare-tsaren Ci Gaban Kaduna a Taron Duniya a Dubai.
  • Ministan Wajen Malawi: Tsarin Ci Gaban Kasar Sin Ya Samar Da Darussa Ga Kasashe Masu Tasowa
  • Ya Kamata Sin Da Amurka Su Zama Kawayen Juna Ba Abokan Gaba Ba
  • Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare
  • Sin Ta Fitar Da Jerin Sakamakon Tattaunawar Tattalin Arziki Da Cinikayya Da Tawagar Kasar Da Ta Amurka Suka Cimma 
  • Kasar Sin Ce Ke Da Sama Da Rabin Muhimman Makaloli Na Duniya