Tattalin arzikin Najeriya ya ƙara haɓaka — NBS
Published: 22nd, September 2025 GMT
Hukumar Ƙididdigar a Najeriya, NBS ta ce arzikin cikin gida da ƙasar ke samu ya ƙaru da kashi 4.23 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2025 da muke ciki.
Sabbin alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa an samu ƙarin kashi 3.48, idan aka kwatanta da daidai wannan lokacin a 2024, lamarin da hukumar ta ce alamu ne na bunƙasar tattalin arzikin ƙasar.
NBS ta ce fannin aikin gona ne kan gaba wajen samar da ƙaruwar arzikin ƙasar, wanda ya ƙaru zuwa kashi 2.82 saɓanin kashi 2.60 a 2024.
Sauran fannonin da hukumar ta ce an samu ci gaba sun hada da fannin masana’antu da, da man fetur da kuma fannin ma’adinai.
NBS ta ce a rubu’i na biyu na shekarar 2025, arzikin cikin gida da Najeriya ta samu ya kai naira tiriliyan 100.73, ƙari kan naira tiriliyan 84.48 da aka samu a 2024 daidai wannan lokacin, abin da ke nuna ƙarin kashi 19.23 cikin 100.
A watan jiya na Agusta ne Majalisar Ƙoli ta tattalin arziki a Najeriya, ta sanar da amincewa da sabon tsarin ci gaban tattalin arziki zango na biyu na tsawon shekaru 5 wato 2026-2030, bayan ƙarewar zangon farko wato daga 2021 zuwa 2025.
Sabon tsarin da majalisar ta ƙaddamar wadda ke ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shetima ci gaban tattalin arziki zai yi la’akari da sauye-sauyen da aka samu kamar cire tallafin man fetur, sabbin dokokin haraji da makamatansu.
Ƙarƙashin sabon tsari ne kuma gwamnatin ke son cimma ƙarfin tattalin arziƙi na Dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030, abinda ya dace da manufofin ƙasar har zuwa shekarar 2050.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Tattalin Arziki
এছাড়াও পড়ুন:
Gavi Zai Yi Jinyar Watanni 5 Bayan Yi Masa Tiyata
Gavi dai ba zai dawo ba sai a farkon shekarar 2026, shekarar da ake ganin kasar Sifaniya za ta kasance cikin kasashen da suka fi damar lashe gasar cin kofin duniya da za a buga a kasashen Amurka, Mexico da kuma Canada.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp