Janar Mousawi: Karfafa tsaron sararin samaniyar Iran zai dakile barazanar makiya a kanta
Published: 1st, September 2025 GMT
Babban hafsan hafsoshin sojojin kasar Iran Manjo Janar Abdolrahim Mousavi ya bayyana cewa, rundunar sojin saman kasar Iran a matsayinta na bangaren da ke sahun gaba na kare ikon sararin samaniyar kasar, ya rataya a kansu wajen ci gaba da kara kokarinsu na bunkasa tsaon sararin samaniyar kasar, domin tabbatar da cewa an dakile duk wata barazana ta makiya a kan akasar.
A cikin sakon da ya aike na ranar tsaron sararin sama ta kasa, Janar Mousavi ya yi tsokaci kan yadda yanayin tsaro na yanki da na duniya ke ciki, inda ya bayar da misali da irin abubuwan da al’ummar Iran suka samu a tsawon shekaru 8 a bangaren ayyukan tsaro da kariya, wanda kuma ya tabata a yakin kwanaki 12 da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da Amurka suka kaddar a kanta. Wannan ci gaban, na nuna bukatar gaggauta sabunta tsarin, da karfafa shi, da kuma bunkasa shirye-shiryen aikin tsaron a dukkanin fagage na sararin samaniya.
Ya kara da cewa, babu shakka, tsaron sararin samaniyar kasar Iran, dole ne ya ci gaba da kasancewa a kan gaba a cikin dukkanin ayyukan tsaro na kasar, sannan kuma dole ne hakn ya kasance daidai da irn barazanar da kasar take fuskanta.
Bugu da kari kan hakan, aiwatar da ayyuka na hadin gwiwa a tsarin tsaron sararin samaniya na kasa, da inganta hadin gwiwa a dukkanin sauran ayyuka na tsaron kasa, wanda hakan ne zai kara tabbatar da haduwar karfin soji da sauran bangarorin tsaro wuri guda.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Al-Houthi: Kisan jami’an fararen hula manuniya ce kan gazawar Isra’ila September 1, 2025 GCC: Batun Kafa Isra’ila Babba Hadari Ne Mai Girma Ga Kasashen Larabawa September 1, 2025 Jagora: Yarjejeniyar Da Iran Ta Cimma Da China Tana Da Muhimmanci Don Haka A Hanzarta Aiwatar Da Ita August 31, 2025 Pezeshkian: Taron Kolin Shanghai Wata Muhimmiyar Dama Ce Ta Bunkasa Alakar Bangarori Da Dama Na Yankin August 31, 2025 Mataimakin Babban Kwamandan “IRGC”: Makiya Sun Kasa Cimma Munanan Manufofinsu Kan Iran August 31, 2025 Jagoran Kungiyar Ansarullah Ta Kasar Yemen Ya Ce: Dakarunsa Zasu Ci Gaba Da Yaki Da Isra’ila August 31, 2025 Gwamnatin Kenya Ta Ci Gaba Da Tono Gawarwakin Da Masu Tsaurin Addinin Kirista Da Suka Kashe Kansu A Kenya August 31, 2025 Kissoshin Rayuwa: Siratuh Imam Al-Hassan (a) 135 August 31, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 137 August 31, 2025 Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Al-Hassan (a) 136 August 31, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: sararin samaniyar tsaron sararin
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta
Iran ta yi ikirarin cewa Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya “san”sarai da cewa shirin nukiliyar kasar na lumana ne, don haka ya kamata ya guji yin “kalamai marasa tushe” kan lamarin.
A wata hira da ya yi da tashar Al Jazeera, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya bayyana cewa kalaman da Rafael Grossi ya yi a baya sun share fagen ayyukan ta’addanci da Amurka da gwamnatin Isra’ila suka yi wa Iran a watan Yunin da ya gabata.
Ya kamata Darakta Janar na IAEA ya guji yin kalamai marasa tushe game da shirin nukiliya na Iran, in ji shi.
Rafael Grossi ya bayyana a ranar Laraba cewa IAEA ta gano kwanan nan da sake dawowa da ayyuka a wuraren nukiliya na Iran,” bayan ya amince cewa kasar ba ta nuna alamun kara wadatar da uranium ba.
A cikin wani rahoto na sirri da aka gabatar wa Kwamitin Gwamnonin IAEA a ranar 31 ga Mayu, 2025, Babban Daraktan IAEA ya yi iƙirarin cewa “Iran ta gaza bayyana ayyukanta na nukiliya a wurare uku da ba a bayyana ba” kuma ta bayyana damuwa game da tarin sinadarin uranium da ta wadatar zuwa kashi 60%.
A cewar jami’an Iran, rahoton Grossi game da shirin nukiliya na Tehran ya share fagen kai hari ga Isra’ila kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
A karshen watan Yuni ne, Majalisar Tsaron Iran ta amince da wani kudiri da majalisar dokokin kasar ta zartar wanda ya dakatar da haɗin gwiwa da hukumar ta IAEA.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci