2025-11-27@23:35:42 GMT
إجمالي نتائج البحث: 205
«carar zakaran»:
(اخبار جدید در صفحه یک)
Rundunar ’yan sandan Nijeriya ta samu nasarar cafke gungun wasu masu yi wa mayaƙan Boko Haram da ’yan bindiga safarar babura a jihohin Neja da Kaduna. Galibai dai ’yan ta’adda a Arewacin Nijeriya sukan yi amfani da babura wajen gudanar da harkokin sufuri domin sheƙe ayarsu ta garkuwa da satar mutane da kai wa al’ummomi hare-hare. Sojoji sun ƙwato tarin makamai a Zamfara Tankar mai ta sake fashewa a Neja Da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar ’yan sanda da ke Abuja a ranar Talatar nan, mai magana da yawun rundunar, Benneth Igweh, ya ce sun samu nasarar ce ta hanyar bayanan sirri, inda suka cafke wasu mutum uku a Ƙaramar Hukumar Suleja ta Jihar Neja. Igweh ya bayyana...
Babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin CMG, ya fitar da jerin shirye-shiryen shagalin murnar bikin bazara na bana a yau Talata. Shagalin na bana zai kunshi nau’o’in shirye-shirye daban-daban, kamar wake-wake da raye-raye da wasannin kokawa na gargajiya da na siddabaru da sauransu, domin murnar zuwan sabuwar shekarar gargajiya ta Sin tare da masu kallo dake fadin duniya. A lokaci guda, wasu kafafen yada labarai 2,900 a kasashe da yankuna sama da 200 dake fadin duniya, za su kama tashoshin talabijin na CGTN na kasar Sin na harsunan Ingilishi da Spaniyanci da Faransanci da Rashanci da sauran dandamali dake amfani da harsunan waje har 82, wajen watsawa tare da bayar da rahotannin shagalin bikin bazara na bana....
A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da katin murnar sabuwar shekara bisa kalandar gargajiya ta kasar Sin, a matsayin martani ga abokai a jihar Iowa ta kasar Amurka, inda ya ce, Sin da Amurka na da manyan muradun bai daya, da damar yin hadin gwiwa, kuma suna iya zama abokan hulda da aminai. Ya yi fatan jama’ar kasashen biyu za su kara cudanya da juna, da kara yin mu’amala da juna, da yin aiki tare wajen rubuta labarin abokantaka a tsakanin jama’ar kasashen biyu, da ba da sabbin gudummawa ga ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Amurka. (Mohammed Yahaya)
Daga cikin yara ‘yan makaranta miliyan 242 da matsanancin yanayi ya raba da muhallansu a kasashe 85 a shekarar 2024, dalibai miliyan 2 da dubu 200 ne a Najeriya suka rabu da muhallansu, lamarin da ya kawo cikas ga harkokin ilimi a shekarar. Rahoton wanda Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya fitar a daidai lokacin da duniya ke bikin ranar ilimi ta duniya ta shekarar 2025, ya nuna cewa a Najeriya baki daya dalibai miliyan 2,200,200 ne suka daina makaranta sakamakon ambaliyar ruwa. Da take gabatar da jawabi kan tasirin da sauyin yanayi ke da shi ga ilimin yara, shugaban ofishin UNICEF na Kano, Mista Rahama Farah ya bayyana cewa, ambaliyar ruwa da ta...
Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci ya bayyana cewa: Atisayen soji na “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara Babban kwamandan sojojin ruwa na dakarun kare juyin juya halin Musulunci na Iran Admiral Ali Reza Tangsiri ya sanar da cewa: Atisayen soji mai take “Manzon Allah Mai Girma na 19” ya cimma gagarumar nasara da burin da ake son kai wa bayan samun nasarar gwada sabbin na’urori da gudanar da ayyuka daban-daban, tare da samun nasarar gwajin kai hari kan wuraren abokan gaba. A wata hira da ya yi da manema labarai a yau Lahadi, Admiral Tangsiri ya bayyana cewa: A rana ta biyu ta atisayen “Manzon Allah Mai Girma na 19”...
