Hisbah ta kama mai safarar mutane da mata 12
Published: 4th, September 2025 GMT
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wani da ake zargi da safarar mutane (wanda aka sakaya sunansa) a wani wurin garejin motoci tare da wasu mata 12 da ake zargi da safarar mutane da ke shirin tafiya Legas.
Bayanin hakan ya fito ne daga bakin mataimakin Kwamandan Hukumar ta Hisbah, Sheikh Mujahideen Aminuddeen.
Sanarwar ta bayyana cewa, jami’an rundunar sun kama mutumin ne a wani garejin motoci da ke kan titin Zariya.
Hukumar ta bakin mataimakin ta bayyana cewa, jami’an Hisbah ƙarƙashin jagorancin OC Muhammad Bashir na garejin motoci sun kama wakilin safarar wanda aka ce ya fito daga Jihar Borno, ya hau mota zuwa Legas tare da waɗanda ake zargin.
Aminuddeen ya bayyana cewa, bayanan farko sun nuna cewa, mutumin yana safarar matan ne, kowannensu yana da fasfo na ƙasa da ƙasa zuwa ƙasar Saliyo ta hanyar Legas, Jamhuriyar Benin da Ghana, inda ya ƙara da cewa mutumin yana da shirin yin biza ga waɗanda ya yi safarar don tafiya ƙasar Saudiyya don neman aiki.
Aminuddeen ya kuma bayyana cewa, a yayin da ake yi musu tambayoyi, matan sun sanar da jami’an Hisbah cewa kowaccen su ta biya Naira miliyan 1,500,000 a karon farko tare da yarjejeniyar biyan cikon sauran kuɗi idan sun samu aiki a inda za su.
A cewar hukumar, ɗaya daga cikin matan akwai mai shekara 50 sauran biyu kuma akwai mai shekara 23 da mai shekara 20, yayin da ragowar kuma ’yan shekara 15 ne.
Ya bayyana cewa a cikin waɗanda aka yi safarar, uku sun fito daga Katsina, biyu daga Kano, ɗaya daga jihohin Borno, Jigawa da Zamfara.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Hukumar Hisbah Jigawa bayyana cewa
এছাড়াও পড়ুন:
Dalilin Da Ya Sa Hukumar NIWA Ta Fara Gyaran Hanyoyin Ruwa A Jihar Legsa
Manajar ofishin na NIWA, da ke a jihar ta Legas Injiniya Sarat Braimah ta bayyana cewa, tura ma’ikatan hukumar domin yin aikin, zai taimaka wajen gudanar da aikin a cikin inganci.
Kazalika, ya sanar da cewa, hakan zai kuma bayar da damar yin safarar kaya a cikin sauki da kuma safarar matafiya da ke bin hanyar ruwa ta yankin na Ikorodu.
“Mun yi nazari a cikin kwanciyar hankali kan yadda za a tabbatar da an cire fulawar da ke a cikin kasan ruwan ba tare da wata miskila ba tare da kuma bai wa jiragen ruwan damar yin zirga-zirgarsu a hanyoyin ruwan, ba tare da wata matsala ba, “ Inji Injiya Braimah.
“ Aikin ya wuce batun fannin samar da saukin yin sufurin jiragen ruwan har da tabbatar da an kiyaye janyo matsala ga ayyukan kamun Kifi a hanyoyin na ruwan, “ A cewar Inji Manajar.
Ta kara da cewa, babban shugabanmu na hukumar ta NIWA, Bola Oyebamiji, ne tuni ya riga ya bayar da kwangilar yin aikin, ba wai a jihar Legas kawai ba, har da a sauran hanyoyin ruwa da ke a sassan kasar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA