Kasashen Afirka ta Kudu da Sin sun kaddamar da wani sabon yunkuri na zurfafa dangantakar tattalin arziki, inda Beijing ta yi alkawarin zuba jari a fannin hakar ma’adinai, makamashi, da ababen more rayuwa. Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Pretoria ke fuskantar matsanancin  matsin lamba daga sabbin harajin da Amurka ta sanya mata wanda ke yin barazana ga damar da ta ke da ita a karkashin dokar bunkasar Afirka da damammaki (AGOA).

Taron bunkasa harkokin kasuwanci na kasashen Afirka ta Kudu da Sin karo na 9, wanda aka gudanar a ranar Talata, ya jaddada aniyar kasashen biyu na karfafa hadin gwiwar tattalin arziki.

A wajen taron, shugaban kungiyar tattalin arziki da cinikayya ta kasar Sin da Afirka ta Kudu Zhang Chaoyang, ya sanar da cewa, an samu babban ci gaba a fannin hakar zinare a yankin  Gauteng.

Kamfanin Gold One, mallakin kungiyar Baiyin Nonferrous ta kasar Sin, zai zuba hannun jari na rand biliyan 4 (dala miliyan 230) cikin ayyukan, wanda ke nuna kwarin gwiwa ga tattalin arzikin Afirka ta Kudu da ke dogaro da albarkatun kasa.

Asusun bunkasa harkokin tattalin arziki da kasuwancin Sin da Afirka ya kuma tabbatar da shirin shiga ayyukan kai wutar lantarki a gashin Afirka ta Kudu, wanda aka tsara don fadada karfin wutar lantarki tare da tallafin kamfanoni masu zaman kansu.

A halin da ake ciki, kamfanonin da ke da alaka da gwamnatin kasar Sin, irin su China State Construction, sun yi alkawarin kara yawan sayayya a cikin gida, da habaka sassan masana’antu da hidima na Afirka ta Kudu.

Mataimakin ministan kasuwanci Zuko Godlimpi ya bayyana haɗin gwiwar a matsayin wata dama ta samar da “makoma mai fa’ida ga bangarorin biyu,” yana mai jaddada muhimmancin  mayar da hankali ga saka hannun jari a ayyukan more rayuwa, ayyukan makamashi, da karfin masana’antu a Afirka ta kudu.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Sheikh Qassem: Ba za mu mika makamin gwagwarmaya ba September 28, 2025 Iran: Kisan Nasrallah ya saba wa kundin tsarin mulkin MDD September 28, 2025 Shugaban Argentina ya nemi jinkirta ziyarar Netanyahu a kasar saboda fargabar boren jama’a September 28, 2025 Sojojin Isra’ila Sun Kashe Sama Da Falasdinawa 77 A Gaza A Yau Kawai. September 27, 2025 An Gudanar Da Taron Cika Shekara 1 Da Shahadar  Sayyid Nasrullah September 27, 2025 Yunkurin Jinkirta Dawo Da Takunkumi Kan Kasar Iran Bai Yi Nasara ba. September 27, 2025 Shugaban Hukumar IAEA Ya Ce Shirin Nukiliyar Iran Na Zaman Lafiya Ne September 27, 2025 Shugaban Majalisar Tsaron Kasar Iran  Dr Ali Larijani  Ya Isa Birnin Berut . September 27, 2025 Iran ta kira jakadunta daga Birtaniya, Faransa, da Jamus domin tuntuba September 27, 2025 MDD : Isra’ila na kai harin bam a Gaza kowane minti 8 ko 9 September 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: tattalin arziki

এছাড়াও পড়ুন:

An Kara Zaburar Da ‘Yan Arewa Game Da Muhimmancin Mallakar Katin Zabe

An bayyana katin zabe a matsayin sheda da za a iya amfani da shi a muhimman wurare, kamar yadda ake amfani da fasfo da katin dan kasa a manyan kasashen duniya.

Tsohon wakilin mazabar tarayya ta Birnin Kudu da Buji, Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yi wannan tsokaci new a wata tattaunawa da manema labarai a Dutse.

Ya bayyana bukatar aiki tukuru a tsakanin masu ruwa da tsaki dan tabbatar da cewar dukkan wadanda su ka cancanta sun karbi katin zaben.

Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yabawa gwamnatin Malam Umar Namadi bisa kafa kwamati na musamman a karkashin mai bada shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Lawan Garba Bullet, domin zaburar da kananan hukumomi su bada gudummawar da za ta taimaka wajen samun nasarar shirin.

Ya lura cewar akwai abin damuwa bisa karancin fitowa wajen karbar katin zabe a Arewa, idan an kwatanta da alkaluman karbar katin zaben a ikko da sauran jihohin kudu maso kudu da kudu maso gabashin kasar nan duk da cewar Arewa ta fi yawan jama’a.

Magaji Da’u Aliyu ya ce yana da cikakken bayani kan gudummawar da shugabannin kananan hukumomin Birnin Kudu da Buji su ke bayarwa ga aikin bada Katin Zabe amma duk da haka akwai bukatar rubanya kokari domin cimma gagarumar nasara.

Daga nan sai ya yi kira ga matasan da su ka cika shekarun yin zabe da wadanda su ka canja wurin zama da wadanda katin zaben su ya lalace ko ya bata, da su je domin sake karbar wani katin zaben.

A cewar sa, yin haka shine zai basu damar zaben dan takarar da ya kwanta musu a rai ko kuma fidda baragurbin ‘yan siyasa daga madafun iko.

 

Usman Mohammed Zaria

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugaban Kasar Amurka Donal Trump Ya Isa HKI Kafin Taron Sharm Sheikh
  • An Kara Zaburar Da ‘Yan Arewa Game Da Muhimmancin Mallakar Katin Zabe
  • Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk
  • Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine
  • Amurka Da Masar Ne Zasu Jagoranci Taron Rattaba Hannu Tsakanin HKI Da Falasdin A Sharm Sheikh
  • China Ta Sha Alwashin Maida Martani Kan Harajin Trump A Kanta Na 100%
  • Afirka Ta Kudu Ta Ce Babu Wata Makarkashiya A Mutuwar Jakadanta A Kasar Faransa
  • Masana Sun Bayyana Yadda Za A Magance Ficewar Kamfanoni Da Masana’antu Daga Nijeriya
  • Wani Dan Majalisar Dokokin Kasar Iran Ya Ja Kunnen Amurka Kan Taba Jiragen Dakon Man Kasa
  • Venezuala Ta Bukaci Kwamitin Sulhun M.D.D Da Ya Tabbatar Da Cewa: Amurka Tana Barazana Ga Zaman Lafiya