Gwamnatin Jihar Jigawa ta bukaci manoman shinkafa da su hanzarta gyaran gonakinsu domin samun damar shiga shirin noman shinkafa da Gwamna Umar Namadi ya bullo da shi domin samar da abinci da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar.

Mai bai wa Gwamna shawara kan shirin Noma Dan Riba, Alhaji Muhammad Idris Danzomo ya bada wannan shawara a zantawarsa da manema labarai a Dutse.

Ya ce bukatar ta zama wajibi domin bai wa manoman damar amfana da tsare tsaren gwamnati na bunkasa noman shinkafa da samar da ayyukan yi ga al’umma.

Alhaji Muhammad Idris Danzomo ya kuma shawarci manoman na shinkafa da su tabbatar sun tona rijiya a gonakinsu.

A cewar sa, za a tura malaman gona zuwa lungu da sako domin zakulo manoman shinkafar da suka shirya domin cin gajiyar sharin.

Bunkasa aikin gona dai na daya daga cikin kudirori 12 na Gwamna Umar Namadi na bunkasa tattalin arzikin al’umma da na gwamnati.

 

Usman Mohammed Zarian

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: Jigawa

এছাড়াও পড়ুন:

Gwamnatin Bauchi Ta Cire Shugaban Makaranta Kan Satar Kayan Gwamnati

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Kaddamar Da Dashen Itatuwa Na Bana
  • Yadda Masu Bukata Ta Musamman Suka Rungumi Sabbin Dabarun Noma Domin Ciyar Da Kansu
  • Asusun NADF, OCP Da Gwamnatin Katsina Sun Kaddamar Da Noman Hekta 50
  • Gwamnatin Tarayya Na Shirin Dakatar Da Shigo Da Kifi Daga Ketare
  • Gwamnatin Jigawa Za Ta Kashe Naira Biliyan 3.5 Wajen Gina Shaguna A Farm Centre
  • Jihar Jigawa Na Kara Bullo Da Shirye-shiryen Inganta Rayuwar Masu Bukata Ta Musamman
  • Gwamnan Jigawa Ya Rattaba Hannu Kan Kudirin Dokar Tabbatar Da Hisbah
  • Matsalar Tsaro: Sarakuna Sun Bukaci Gwamnati Ta Canza Salo
  • IMF na Shirin aikewa da wata tawaga zuwa Senegal domin tattauna batun basussukan kaaar
  • Gwamnatin Bauchi Ta Cire Shugaban Makaranta Kan Satar Kayan Gwamnati