Gwamnan Edo Ya Ziyarci Sanata Barau Kan Kisan Yan Arewa 16
Published: 31st, March 2025 GMT
Gwamnan Jihar Edo, Monday Okpebholo, ya kai ziyara ga Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, domin nuna alhini kan kisan gilla da aka yi wa matafiya dyan Arewa a Uromi. Harin da aka kai a ranar Alhamis ya haifar da mutuwar mafarauta da ke kan hanyar zuwa bikin Sallah. Gwamnan ya bayyana cewa an kama mutane 14 da ake zargi da hannu a kisan, kuma za a kai su Abuja domin ci gaba da bincike.
A yayin ziyarar, Gwamnan Okpebholo ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta taimaka wa iyalan wadanda aka kashe, yana mai nuni da cewa Shugaban kasa da Yansanda sun dauki matakai kan lamarin. “Za mu tabbatar an gurfanar da wadanda suka aikata wannan mugun aiki a gaban doka,” in ji Gwamnan. Sanata Barau ya amsa da yabon matakan gwamnatin Edo, yana mai cewa: “Dole ne a ci gaba da yin Adalci domin hana irin wannan bala’i a nan gaba.”
Yadda ‘Yan Banga A Edo Suka Yi Sanadin Kashe Matafiya Mafarauta 16 – Direban Motar YANZU-YANZU: Gwamnan Edo Ya Kai Ziyarar Jaje Kan Kisan Mafarauta A Uromi‘Yansandan sun kara da cewa za su ci gaba da yaki da duk wani yunkurin tayar da tarzoma a jihar. Gwamnan Edo ya kuma yi kira ga al’umma da su yi haƙuri, yana mai jaddada cewa jihar ba ta yarda da ‘yan daba ko dakar doka a hannu ba. “Edo ta kasance gida ne na zaman lafiya ga dukkan al’ummar Nijeriya, kuma za mu kiyaye wannan tarihi,” in ji Gwamnan
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano Ya Kammala Rahoton Aikinsa Na Wucin Gadi
Kwamitin Aikin Hajjin 2025 Na Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Sarkin Karaye, Mai Martaba Alhaji Muhammad Mahraz Karaye, ya kammala rahoton aikinsa na wucin gadi.
Darakta Janar na Hukumar, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya bayyana hakan a fadar Sarkin da ke Karaye.
Ya ce rahoton ya ƙunshi dukkan abubuwan da suka shafi aikin Hajji tun daga lokacin da aka ƙaddamar da kwamitin a birnin Makkah, ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf.
“Rahoton ya kunshi cikakken bayani kan ayyukan da kwamitin ya gudanar zuwa yanzu, kuma zai kasance muhimmin ɓangare na rahoton ƙarshe da za a miƙa ga Gwamna,” In ji shi.
Alhaji Lamin Rabi’u ya bayyana cewa Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano ta rigaya ta tattara nata cikakken rahoton, wanda za a mika wa Gwamnan nan ba da daɗewa ba.
A nasa jawabin, Sarkin Karaye ya nuna godiya ƙwarai ga Gwamnan Jihar bisa amincewa da baiwa kwamitin damar gudanar da wannan aiki mai muhimmanci.
Shugaban Hukumar gudanarwa na hukumar Alhaji Yusif Lawan, ya bayyana godiya ga Sarkin Karaye bisa sadaukarwa da haɗin kai da ya bayar, wanda ya taimaka wajen samun nasarar aikin kwamitin.
Abdullahi Jalaluddeen