KAROTA za ta kashe N250m wajen gyaran motoci 5 a Kano
Published: 30th, January 2025 GMT
Hukumar Kula da Hanyoyi da Sufuri ta Jihar Kano (KAROTA), ta ware Naira miliyan 250 domin gyaran wasu motocin aiki guda biyar.
Haka kuma, hukumar ta kashe Naira miliyan 250 domin sayen sabbin motoci domin amfanin da su.
Ana biyan wasu kuɗi don kare gwamnatin Tinubu — El-Rufai An kashe mutumin da ya ƙone Al-Ƙur’ani a SwedenKwamishinan Tsare-Tsare da Kasafin Kuɗi na Jihar, Musa Sulaiman Shanono ne, ya bayyana hakan yayin da yake bayani kan kasafin kuɗin shekarar 2025 da aka amince da shi.
Ya bayyana cewa ingantaccen tsarin sufuri yana da matuƙar muhimmanci ga bunƙasa tattalin arziƙi da ci gaban al’umma.
Ya kuma ce gwamnatin jihar na ƙoƙarin inganta kayan sufuri domin sauƙaƙa zirga-zirgar jama’a da kayayyaki a faɗin jihar.
“Tsarin sufuri yana da matuƙar muhimmanci ga ci gaban ƙasa da bunƙasar tattalin arziƙi. Don haka, gwamnatin jiha tana ɗaukar matakan da suka dace don inganta kayayyakin sufuri domin sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki a ciki da wajen jihar,” in ji shi.
Shanono ya ƙara da cewa gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan 13.32 don aiwatar da wasu muhimman ayyuka a ɓangaren sufuri, ciki har da sayen sabbin motocin ofis da kuma gyaran motocin aiki na hukumar KAROTA.
Ya tabbatar da cewa Naira miliyan 250 za a yi amfani da su wajen sayen motocin ofis, yayin da sauran Naira miliyan 250 ɗin za a kashe su wajen gyaran wasu motocin aiki guda biyar.
Kwamishinan ya yi ƙarin haske kan yadda motocin da za a gyara za su laƙume kuɗaɗe daidai da kuɗaɗen sabbin motocin da za a siya.
“Waɗannan motocin aiki ne, kuma manyan motoci ne. Ba za a iya haɗa su da motocin ofis da shugaba ke amfani da su ba, domin suna da bambanci,” in ji shi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Gyaran Motoci Kwamishina Naira miliyan 250
এছাড়াও পড়ুন:
An Tsare Wani Mutum A Gidan Yari Kan Zargin Kashe Matarsa Saboda Ƙuli-Ƙuli A Kano
Mai shari’a Dahiru ya amince da buƙatar, ya kuma ɗage shari’ar zuwa ranar 12 ga watan Disamba, 2025, domin ci gaba da sauraron shari’ar.
Ƙuli-ƙuli dai nau’in abin ci ne mai taushi da ake yi da gyaɗa, ana soyawa har sai ya zama ƙura-ƙura ta yadda za a ci cikin nishaɗi.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA