Gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi Ta Tura Ɗalibai 117 Karatu Ƙasar Algeria
Published: 15th, October 2025 GMT
Sayyidi Aliyu ya shaida hakan ne yayin jawabin bankwana da wayar da kan ɗaliban da suka samu gurbin karatun zuwa ƙasar Algeria na shekarar 2025, da ya gudana a cibiyar Sheikh Dahiru da ke Bauchi a ranar Litinin 13 ga watan Oktoba.
Ya ce an ɗauki tsawon lokaci ana wayar da kan ɗaliban na tsawon shekara guda kan yadda za su kyautata rayuwarsu a can ƙasar da kuma samun ilimin da ake tsammani a garesu ba tare da matsaloli ba tare da koyar musu harsunan Farsanci da Larabci domin sauƙaƙa musu fara rayuwa a ƙasar Algeria.
Ya yaba wa Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad bisa biyan kuɗin jirgi wa dukkani ɗaliban jihar su 50 daga cikin waɗanda za su tafi ƙasar neman ilimi.
Kazalika, ya kuma gode wa gwamnan bisa roƙa musu da ya yi na cewar a bai wa ‘yan Nijeriya damar koyon ilimin likitanci, “A lokacin da tawaga daga Algeriya suka zo jihar Bauchi, gwamna Bala Muhammad ya yi roƙo na cewar a ake amincewa ɗaliban Nijeriya samun ilimin likitanci a ƙasar Algeriya, wanda a da baya ba su bai wa kowa damar samun wannan sai ‘yan ƙasar amma suka amince, lallai wannan abun yabo ne sosai,” ya shaida.
Ya ce bayan kuɗin ticket komai na hidimar karatun kyauta ne wanda gwamnatin ƙasar Algeria ta ɗauki nauyi ga waɗanda suka samu nasarar samun guraben, wanda suke da damar yin karatu daga digiri har digiri na biyu (masters), sai ya yi bayanin cewa suna kan ƙoƙarin neman damar samar wa ɗalibai guraren digirin digirgir (PhD).
Ya ƙara da cewa wannan shi ne karo na biyu domin a farko gidauniya ta tura ɗalibai 66 zuwa ƙasar Algeriya wanda zuwa yanzu wasu ma har sun kammala digiri a fannonin ilimi daban-daban.
Jagoran ya nuna kwarin guiwar cewa idan ɗaliban suka kammala karatun nasu, ƙasar Nijeriya za ta moresu matuƙa gaya. Ya hori ɗaliban da suka samu tallafin karatun da su maida hankali wajen yin abun da ya kamata domin samun ilimi mai inganci tare da nemansu da su zama jakadu na kwarai ga Nigeria.
Kazalika, ya jinjina wa Sheikh Dahiru Usman Bauchi bisa gayar gudunmawar da yake bayarwa wajen kyautata harkokin ilimin addini da na zamani, ya ce, bayan gudunmawar da yake bayarwa wajen samar da mahaddata yanzu haka ana samun masu karatu a ɓangarori daban-daban na ilimi sakamakon ƙoƙarinsa.
Sadiyya Auwal wacce ta samu gurbin karatu domin karanta ilimin likitanci, ta gode wa Sheikh Dahiru da daraktan ilimin gidauniyar bisa kokarinsu da ya kai su ga samun damar karatun tare da tabbatar da cewa za ta maida hankali domin samun nasarar abun da za ta je yi can ƙasar Algeria.
Shi ma Mukhtar Ahmed wanda ya samu gurbin ƙaratun ilimin kimiyyar na’ura mai ƙwaƙwalwa (Computer Science) ya nuna godiya wa gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi kan damar da ta samar musu, ya ce tsawon shekara ana faɗi tashi don nema musu tafiya karatun.
Ya bada tabbacin maida hankali domin samun ilimi mai inganci tare da dawowa Nijeriya domin bayar da nasa gudunmawar.
ShareTweetSendShare MASU ALAKAকীওয়ার্ড: ƙasar Algeria
এছাড়াও পড়ুন:
PDP Ta Ɗage Babban Taronta Biyo Bayan Ficewar Wasu Manyan Jiga-jigai
Wannan ci gaban ya zo ne a daidai lokacin da PDP ke shirin gudanar da babban taronta na ƙasa da za a yi a Ibadan, a Jihar Oyo, daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Nuwamba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA