Ɗan Majalisa ya nemi ɗaukar mataki kan dorinar ruwa a Gombe
Published: 10th, October 2025 GMT
A yayin da ake yawan samun ɓarnar dorinar ruwa a garuruwan Daɗin Kowa da Kupto da Malleri da Wade a yankunan Ƙananan hukumomin Kwami da Yamaltu Deba a Jihar Gombe ta kai ga samun asarar amfanin gona da rayuka.
Hakan ne ya sa Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar mazaɓar Yamaltu/ Deba a Jihar Gombe Inuwa Garba ya gabatar da ƙudiri a gaban zauren Majalisar Wakilai ta tarayya domin neman ɗaukar matakin gaggawa kan ɓarnar dorinar ruwa.
Inda ya ce dorinar na yi wa manoma ɓarna sosai da ke janyo asarar rayuka, dukiyoyi da lalacewar amfanin gona a yankunan da abin ya shafa.
Inuwa Garba ya bayyana hakan ne, a shafinsa na Facebook cewa, dorinar ruwan ta zama babbar matsala ga manoma da al’ummomin waɗannan yankuna inda ake samun girgizar tattalin arziki sakamakon lalacewar gonaki, lalata hanyoyi da kuma rasa muhallin zama.
Ya ce, wannan ƙudiri na da nufin kawo mafita ta dindindin domin kare rayukan mutane, kiyaye dukiyoyin su da kuma tabbatar da ci gaban noman rani da damina, wanda shi ne tushen rayuwar yawancin mazauna yankin.
Ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Gombe, tare da hukumomin kula da ruwa da su kai ɗauki cikin hanzari ta hanyar bayar da tallafi, gyaran madatsun ruwa da kuma samar da hanyoyin rage haɗarin dorinar a nan gaba.
A ƙarshe, ya miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalai da ‘yan uwa na waɗanda suka rasa rayukansu a ibtila’in dorinar ruwa yana roƙon Allah Ya jikan mamatan da rahama, tare da ba iyalansu haƙuri, juriya na rashin da suka yi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Daɗin Kowa Kwami da Yamaltu Deba a Jihar Gombe Wade dorinar ruwa
এছাড়াও পড়ুন:
Ambaliyar Ruwa Ta Yi Sanadin Mutuwar Mutane 236 A Jihohi 27 Da Birnin Tarayya
A cewar NEMA, mutane 135,764 ne suka rasa matsugunansu, yayin da 115 aka bayyana bacewarsu, yayin da wasu 826 suka samu raunuka sakamakon ambaliyar. Bugu da kari, gidaje 47,708 sun lalace, yayin da gonaki 62,653 suka lalace a fadin jihohin da abin ya shafa.
Hukumar ta kara da cewa, daga cikin wadanda abin ya shafa sun hada da yara 188,118, mata 125,307, maza 77,423, tsofaffi 18,866, da kuma nakasassu 2,418.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA