A ba mu damar ɗaukar makamai don kare kanmu daga ’yan bindiga —Sakkwatawa
Published: 7th, October 2025 GMT
Al’ummar Ƙaramar Hukumar Kebbe da ke Jihar Sakkwato sun roƙi gwamnati ta ba su dama su riƙa ɗaukar makamai domin kare kansu daga hare-haren ’yan bindiga da suka addabi yankinsu.
Mutanen sun ce sun gaji da kashe-kashe, sace-sace, da kona gidaje da gonakinsu da ’yan bindiga ke yi, wanda ke jefa su cikin tsananin wahala da asara.
Mazauna yankin sun ce daga cikin garuruwa 17 da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kebbe, an riga an raba mazauna akalla 11 da gidajensu saboda yawan hare-hare.
Wani shugaban al’umma a yankin, Tukur Muhammad Fakum, ya shaida wa BBC cewa halin da suke ciki ya sa suka fara tunanin yadda za su kare kansu da kansu.
Ya kamata a karɓe ikon naɗa Shugaban INEC daga hannun Shugaban ƙasa — IPAC Jerin ministocin da zargin takardun bogi ya tabaibaye su“Yanzu muna tattaunawa. Waɗanda ke da ƙanana gonaki sun riga sun sayar, haka ma waɗanda ke da ƙananan gidaje. Idan muka iya siyan bindiga, za mu bai wa matasanmu su kare mu,” in ji shi.
Ya ce: “Gwamnati ce ya kamata ta kare mu, amma idan ba za ta iya ba, to ta bar mu mu mallaki makamai don matasanmu su kare rayukansu da garuruwansu.”
Fakum ya ƙara da cewa halin da ake ciki ya durƙusa da tattalin arzikin yankin gaba ɗaya.
“Babu abinci. Mutane da ba su taɓa kwana a masallaci ba yanzu suna kwana a can. Ka farka a yau, ka gudu zuwa wani wuri da ba ka taɓa zuwa ba, saboda neman tsira. Lamarin ya kai matuƙar muni,” in ji shi.
Ƙoƙarin da BBC ta yi na jin ta bakin jami’an gwamnati da hukumomin tsaro bai yi nasara ba, domin babu wanda ya amsa kira har zuwa lokacin da aka wallafa rahoton.
Jihar Sakkwato na daga cikin jihohin da suka fi fama da hare-haren ’yan bindiga a ’yan shekarun nan, musamman a ƙananan hukumomin Isa, Sabon Birni, da Kebbe.
Baya ga ’yan bindigar Bello Turji da ke da sansanoni a sassan jihar, mayaƙan Lakurawa sun ɓulla a yankin a ’yan baya-bayan nan.
Masana tsaro sun yi gargaɗi cewa ƙungiyar na iya zama sabon barazana ga jihar da ma yankin Arewa maso Yamma gaba ɗaya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Bindiga hare hare yan bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
Kasar Sin Ta Kare Matakinta Na Takaita Fitar Da Ma’adanan Farin Karfe Na Rare Earth
Ya ce barazanar kakaba karin haraji ba hanya ce da ta dace ta hulda da Sin ba, yana mai nanata cewa, kasar Sin ba ta sauya matsayarta kan batun yakin cinikayya ba, wato ba ta son hakan, amma kuma ba ta tsoro. (Fa’iza Mustapha)
ShareTweetSendShare MASU ALAKA