An kashe ɗan shekara 13 da shanu 36 a wani sabon hari a Filato
Published: 8th, October 2025 GMT
An kashe wani yaro ɗan shekara 13 mai suna Abubakar Wada da shanu 36, yayin da wasu ’yan bindiga sun kai wa makiyaya hari a kusa da ƙauyen Inzon da ke yankin Fan, a Ƙaramar Hukumar Barkin Ladi a Jihar Filato.
Aƙalla shanu 49 kuma sun ɓace ba tare da sanin inda suka shiga ba.
’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru Kamfanonin rarraba lantarki sun tafka asarar biliyan 358 a cikin wata uku – NERCShugaban ƙungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN), a Jihar Filato, Ibrahim Yusuf Babayo, ya bayyana cewa harin ya faru ne da yammacin ranar Talata lokacin da wasu makiyaya uku ke dawowa daga kiwo.
Ya ce ’yan bindigar sun buɗe wa dabbobin wuta, tare da kashe yaron wanda makiyayi ne, yayin da sauran biyun suka tsallake rijiya da baya.
Babayo ya ce: “Mun yi asarar sama da shanu 80, saboda 36 an kashe su, yayin da 49 suka ɓace. Mun gano cewa maharan Berom ne daga yankin Fan.
“Wannan abu ne mai ban tsoro da rashin imani. Makiyayan suna tafiya lafiya ba tare da sun tayar da hankali ba.”
Ya buƙaci makiyaya a faɗin jihar su kwantar da hankalinsu, su bar jami’an tsaro su gudanar da bincike, inda ya yi gargaɗin ɗaukar doka a hannu.
Sakataren MACBAN a Barkin Ladi ya tabbatar da cewa dukkanin hukumomin tsaro sun samu rahoton harin, inda jami’an Operation Enduring Peace, DPO na Barkin Ladi suka ziyarci wajen da harin ya auku.
Ya ƙara da cewa a ranar Lahadin da ta gabata, an kashe shanu guda biyar a wannan yankin kuma matasan Berom ake zargi.
Matasan Berom sun musanta zarginShugaban ƙungiyar matasan Berom (BYM), Barista Solomon Dalyop, ya musanta zargin, inda ya bayyana cewa mutanen Berom masu ƙauanar zaman lafiya ne.
Ya ce: “Waɗannan zarge-zargen kawai wata hanya ce ta neman dalilin kai wa mutanenmu hari.
“A gaskiya, an kai hare-hare guda biyu ta hannun wasu da ake zargin Fulani ne a ranar 6 ga watan Oktoba, 2025 da misalin ƙarfe 7:30 na yamma, inda aka kashe wani mutum mai suna Timothy Ishaku Chollom.”
Dalyop, ya ƙara da cewa ci gaba da kiwo a gonaki da wuraren zama yana tayar da hankali, kuma yana barazana ga rayuka a yankin Fan.
Sojoji sun fara bincikeMataimakin Daraktan Hulɗa da Jama’a na Rundunar Sojojin Najeriya Sashe na 3, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya ce rundunar sojin ta fara bincike kan lamarin.
Ya ƙara da cewa sun tuntuɓi kwamandan sashen da ke yankin domin tabbatar da bayanai game da harin.
উৎস: Aminiya
এছাড়াও পড়ুন:
Matsalar Tsaro: Gwamnonin Arewa sun shirya taron gaggawa
Gwamnonin jihohin Arewa 19 za su gudanar da muhimmin taro a ranar Asabar, 29 ga Nuwamba, domin tattauna matsalolin tsaro da suka addabi yankin.
Mai bai wa Gwamnan Nasarawa shawara na musamman kan harkokin jama’a, Peter Ahemba, ne ya sanar cewa, taron gwamnonin Arewa da aka shirya a Kaduna zai samu halartar manyan sarakunan gargajiya.
“Manufar taron ita ce samar da matsaya ɗaya wajen fuskantar matsalolin tsaro da ke damun yankin, tare da tsara hanyar magance su,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, za a yanke muhimman shawarwari a taron domin tabbatar da tsaron yankin.
’Yan Majalisar Kudu sun roƙi Tinubu ya yi wa Nnamdi Kanu Afuwa Amarya ta yi wa angonta yankan rago bayan kwana 3 da aurensu a KatsinaAhemba ya bayyana cewa, sakamakon ƙalubalen tsaro da wasu jihohin Arewa ke fuskanta, gwamnatin Nasarawa ta ɗauki matakan gaggawa ta hanyar shirya taron tsaro na musamman, inda za a yanke shawarar da za ta kare jihar daga duk wata barazanar tsaro.
“Ya zama wajibi ga ’yan ƙasa su taka rawa wajen magance barazanar tsaro a ƙasarmu da jihohinmu. Don haka, dole ne jama’a su riƙa ba wa hukumomin tsaro bayanai kan mutanen da ke da halin aikata laifi,” in ji shi.