’Yan sanda sun kama ɗan bindiga a kan iyakar Najeriya da Kamaru
Published: 8th, October 2025 GMT
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe, ta kama wani mutum da ake zargin ɗan bindiga ne da ke aiki tsakanin iyakar Najeriya da Kamaru.
Rundunar ta kuma ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biyu, harsasai 80 da wasu tarin makamai.
Gwamnatin Gombe ta kafa hukumar bunkasa fasahar zamani da tattalin arziƙi Yadda Obasanjo ya ƙaddamar da cibiyar taron ƙasa da ƙasa a BauchiKakakin rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya bayyana cewa wanda aka kama, Adamu Adamu, mai shekaru 30, ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Song a Jihar Adamawa.
Amma wanda aka kama mazaunin unguwar Jauro Jatau da ke Akko, Jihar Gombe.
An kama shi ne ranar 4 ga watan Oktoba, 2025, bayan samun sahihan bayanai da suka nuna cewa yana tare da wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane da ke aiki a tsakanin Najeriya da Kamaru.
A yayin wani samame da CSP Ali Madaki ya jagoranta a ƙarƙashin Operation Hattara, rundunar ta gano inda suka ɓoye makamai a wani tsauni da ke kusa da ƙauyen Wuro Biriji a Jihar Adamawa.
Rundunar ta ƙwato bindigogi ƙirar AK-47 guda biy, harsasai 80, gidan harsasai bakwai, sarƙoƙi, makulli, wuƙa da ƙananan jakunkuna huɗu.
Kwamishinan ’yan sandan Jihar, CP Bello Yahaya, ya yaba wa jami’in wajen kama wanda ake zargin.
Ya kuma jaddada ƙudirin rundunar na ci gaba da yaƙi da masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.
Ya buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa hukumomin tsaro bayanai domin tabbatar da zaman lafiya a Gombe da sauran maƙwabtan jihohi.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Yan Sanda Ɗan Bindiga
এছাড়াও পড়ুন:
NAJERIYA A YAU: Amafani Da Karfin Soji Ko Tattaunawa Ne Zai Kawo Matsalar Tsaro A Najeriya?
More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba
A cikin shekarun nan, matsalolin tsaro a Najeriya—kamar ta’addanci, da garkuwa da mutane, da rikicin manoma da makiyaya, da kuma ayyukan ’yan bindiga—suna kara ta’azzara, lamarin da ya sanya al’umma da masana tsaro ke tambayar wace hanya ta fi dacewa gwamatani ta yi amfani da shi wajen kawo karshen wadannan matsaloli da suka ki ci suka ki cinyewa tsawon shekaru.
Yayin da wasu ke ganin amfani da karfin soji ne kadai hanyar da zai kawo karshen wannan matsala, wasu na ganin tattaunawa ne kadai mafita, wasu har ila yau na ganin idan aka yi amfani da gaurayen biyun zai fi dacewa.
NAJERIYA A YAU: Irin Radadin Da Masu Cutar Amosanin Jini Ke Fuskanta DAGA LARABA: Shin Ya Kamata A Biya Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane?Ko wanne daga cikin wadannan hanyoyi ne idan gwamnati ta yi amfai dashi ko da su don magance wannan matsala?
Wannan shine batun da shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi duba a kai.
Domin sauke shirin, latsa nan