Shugabar Cibiyar Nazarin Karatu da Ci Gaban Ilimi ta Najeriya (NCRRD) da ke Jami’ar Bayero Kano (BUK), Farfesa Amina Adamu, ta bayyana damuwa kan yadda dalibai ke ƙara gujewa amfani da dakunan karatu, tana danganta hakan da dogaro da kirkirarriyar fasaha ta AI. Da take jawabi a taron ƙasa da ƙasa karo na biyar kan nazarin karatu da nazari da aka gudanar a Jami’ar Bayero Kano, Farfesa Amina ta ce da dama daga cikin ɗalibai yanzu suna kammala karatun jami’a ba tare da sun taɓa shiga ɗakin karatu ko sau ɗaya ba.

Yadda zargin mallakar takardun bogi ya yi awon gaba da kujerar Ministan Tinubu Joash Amupitan na iya zama sabon shugaban INEC “Muna da daliban da ke yin rajista a shekarar farko kuma su kammala karatu ba tare da sun taɓa amfani da dakin karatu ko sau daya ba. Ba kamar da ba, lokacin da dalibai ke zuwa dakin karatu don neman bayanai da shiryawa jarrabawa, yanzu suna dogaro da fasajohin AI da sauran hanyoyin fasahar zamani,” in ji ta. Farfesa Amina ta yi gargadi cewa duk da amfanin da AI ke da shi, tana haifar da abin da ta kira “lalaci a fannin yin tunani” a tsakanin dalibai. “Suna saka duk aikin da aka ba su manhajar AI ta yi musu, sannan su miƙa amsar da suka samu ba tare da yin tunani da kansu ba. AI an ƙirƙire ta ne don taimakawa, ba don maye gurbin ƙirƙira da tunanin ɗan adam ba,” in ji ta. Ta bukaci malamai, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki da su rungumi AI da kansu, sannan su koya wa dalibai yadda za su yi amfani da ita cikin hikima. “Ba za mu iya kawar da fuskarmu daga samuwar AI ba. Duniya na tafiya da ita, dole mu ma mu bi. Amma dole ne mu koya wa dalibai yadda za su yi amfani da AI ta hanyar haɗa amsoshin da ta bayar da nasu tunanin, ta hanyar yin nazari da zurfin tunani,” in ji ta. Shi kuwa a nasa jawabin, Shugaban Jami’ar BUK, Farfesa Haruna Musa, ya bayyana cewa jami’ar na shirin kafa cibiyar nazari kan AI da da fasahar mutum-mutumi, inda ya ce nan ba da jimawa ba za a fara koyar da darussa kan fasahar zamani a cikin kundin karatun jami’ar. “BUK ta shirya yin amfani da wannan fasaha don sauya tsarin karatu da bincike. Ba wai koyar da ita a matsayin darasi kaɗai ba, mun kuduri aniyar kafa cibiyar zamani ta AI da da fasahar mutum-mutumi. Taron yau ya nuna mana tasirin AI a fannin karatu, bincike da nazari,” in ji shi. Ya kuma bukaci malamai da su yi amfani da fasahar don sauya tsarin koyarwa da koyo a makarantunsu, da nufin inganta ilimi ga yara da al’umma gaba ɗaya. A jawabinsa na buɗe taro, Shugaban Hukumar Sadarwa ta Najeriya (NCC), Dr Aminu Maida, ya bayyana rawar da hukumar ke takawa wajen samar da kayan aiki da za su ba da damar amfani da AI a faɗin Najeriya. Dr Aminu, wanda, Daraktan Bincike da Ci Gaban Fasaha a hukumar, Ismail Adedigba, ya wakilta, ya ce NCC a matsayin hukumar gwamnati da ke kula da harkar sadarwa a Najeriya, ta ƙaddamar da cibiyoyin fasahar zamani a Kano da Lumu don samar da ingantaccen yanayi ga ci gaban AI. Ya bayyana cewa hukumar ta tallafa wa manyan makarantu guda shida da ayyukan binciken kan AI a shekarar 2024. Adedigba ya kuma jaddada muhimmancin amfani da tsare bayanan masu amfani da intanet, inda ya ce NCC tare da Hukumar Kare Bayanai ta Najeriya suna aiki tare don tabbatar da tsaron bayanai a cikin tsarin AI. Ya kuma ce shirin 3MTT na gwamnatin tarayya, wanda ke da nufin horar da ’yan Najeriya miliyan uku a muhimman fannonin fasaha ciki har da AI da tsaron intanet, tuni ya riga ya horar da sama da mutum 60,000 a cikin rukuni na farko, yayin da wasu rukunan ke tafe a nan gaba.

উৎস: Aminiya

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ba Zata Halarci Zaman Taron Sharm El-Sheikh Ba Saboda Wasu Dalilai Da Ta Byyana

Ministan harkokin wajen Iran ya bayyana dalilin da ya sa Iran ba za ta halarci taron na Sharm el-Sheikh ba

Ministan harkokin wajen kasar Iran Abbas Araqchi ya bayyana dangane da rashin halartar jamhuriyar Musulunci ta Iran zuwa taron na Sharm el-Sheikh cewa, ba za su iya tunkarar wadanda suka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar Iran da kuma ci gaba da yi musu barazana da kuma sanya musu takunkumi ba.

Araqchi ya rubuta a shafinsa na yanar gizo a dandalin X da sanyin safiyar yau litinin cewa: “Iran ta nuna matukar jin dadin ta ga gayyatar da shugaba Sisi ya yi wa Iran na halartar taron na Sharm el-Sheikh. Duk da Muradin Iran din na tattaunawa ta diflomasiyya, Araqchi ya ce shi ko shugaba Pezeshkian ba za su iya tunkarar wadanda suka kai wa al’ummar Iran hari da kuma ci gaba da yi mata barazana da kuma sanya mata takunkumi.”

Ya kara da cewa: Duk da haka, Iran tana maraba da duk wani shiri da zai kawo karshen kisan kiyashin da gwamnatin mamayar Isra’ila ke yi a Gaza da kuma bukatar kai wa ga janye sojojin mamaya daga yankin.

Araqchi ya jaddada cewa: Falasdinawa suna da ‘yancin fahimtar ainihin hakkinsu na cin gashin kansu, kuma dukkan kasashe, fiye da kowane lokaci, suna da alhakin taimaka musu tare da goyon bayan wannan bukata ta doka da ta dace.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label Name* Email* Website Label Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Gayyaci Mukaddashin Jakadan Kasar Oman Zuwa Ma’aikatar Harkokin Wajenta October 13, 2025 Yemen Ta Gargadi Isra’ila Kan Fuskantar Hare-Hare Idan Ta Karya Yarjejeniyar Tsagaita Bude Wuta October 13, 2025 Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje October 13, 2025 Shugaban Amurka Ya Yi Barazanar Aikewa Ukraine Makamai Masu Linzami Kirar Tomahawk October 13, 2025 Trump, da Al’Sisi za su jagoranci taron zaman lafiya kan Gaza October 12, 2025 ‘Yan Kamaru na kada kuri’a a zaben shugaban kasar October 12, 2025 Wata Kotu a Faransa ta yi watsi da rufe wata makarantar musulmi a birnin Nice   October 12, 2025 Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine October 12, 2025 Arachi: HKI Ba Abar Amincewa Ba Ce, Falasdinawa Su Yi Hattara October 12, 2025 Iran Ta Yi Allawadai Da HKI Kan Hare-Haren Da Take Kaiwa Kudancin Lebanon October 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Iran Ta Ki Zuwa Masar Saboda Bata Son Haduwa Da Azzaluman Da Suka Kashe Falasdinwa A Gaza
  • Iran Ba Zata Halarci Zaman Taron Sharm El-Sheikh Ba Saboda Wasu Dalilai Da Ta Byyana
  • Yajin Aikin ASUU:  Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya
  • Kungiyar Malaman Jami’o’in Najeriya ASUU ta Shiga Yajin Aiki
  • Yanzu-Yanzu: ASUU Ta Tsunduma Yajin Aiki Na Tsawon Mako Biyu
  • Shugaban Kasar Najeriya Ya Yi  Afuwa Ga Wasu Mutanen Da Kotuna Su Ka Hukunta
  • Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina
  • Birnin Tarayya Zai Taimaka Da Tara Kudin Shiga Daga Fannin Da Bai Shafi Mai Ba — Dantsoho
  • Putin: Natanyahu Yan Son Warware Matsaloli Da Iran Cikin Lumana Ba Tare Da Yaki Ba
  • ’Yan Najeriya miliyan 60 na fama da taɓin hankali – Likita