Aminiya:
2025-10-13@13:33:07 GMT

Mutumin da ya sayar da ɗansa kan N1.5m ya shiga hannu a Ebonyi

Published: 12th, October 2025 GMT

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ebonyi, ta kama wani mutum mai suna Chukwuma Onwe, ɗan Ƙaramar Hukumar Izzi, bisa zargin sayar da ɗan da aka haifa masa kwanaki biyar kan Naira miliyan 1.5.

An gano cewa Onwe ya sayar wa wata mata mai suna Chinyere Ugochukwu jaririn, wacce ake zargin tana cikin ƙungiyar safarar yara zuwa ƙasashen waje.

ASUU za ta fara yajin aikin mako 2 daga ranar Litinin Egbetokun ya sauke kwamishinan ’yan sandan Abuja

Dukkaninsu suna hannun ’yan sanda.

Wata majiyar ’yan sanda ta bayyana cewa matar Onwe, mai suna Philomena Iroko, ce ta fallasa shi bayan ta samu labari daga maƙwabta cewa mijinta ya sayar da jaririn da suka haifa.

Da ta tabbatar da hakan, sai ta garzaya ta kai rahoto ofishin ’yan sanda, inda aka kama Onwe ba tare da ɓata lokaci ba.

Kakakin rundunar jihar Ebonyi, SP Joshua Ukandu, ya tabbatar da cewa an ceto jaririn daga hannun wacce ta saya shi.

Ya ce an kama Onwe da Chinyere Ugochukwu a ranar Juma’a a unguwar Azugwu, Ƙaramar Hukumar Abakaliki, kuma suna tsare a hannun ’yan sanda domin ci gaba da bincike.

Matar Onwe, Philomena, ta ce ta yi mamaki matuƙa cewa mijinta ya sayar da jaririn nasu.

Ta bayyana cewa tun bayan haihuwarta, Onwe, ya ce zai kai jaririn wajen ’yar uwarsa domin ta sa masa albarka, sai dai daga baya aka gano cewa ya sayar da shi.

Ta ce, “Yaronmu bai wuce kwanaki biyar da haihuwa ba, amma mijina ya sayar da shi.

“Ban taɓa tunanin zai yi haka ba. Ina roƙon jama’a da masu hannu da shuni su taimaka min a wannan hali da na tsinci kaina.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Yan Sanda Jariri Uwa ya sayar da

এছাড়াও পড়ুন:

Maryam Sanda na cikin waɗanda Tinubu ya yi wa afuwa

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wa Maryam Sanda afuwa, wadda aka yanke wa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa laifin kashe mijinta, Bilyaminu Bello, ɗan tsohon shugaban jam’iyyar PDP, Alhaji Haliru Bello.

Maryam,’ mai shekara 37, ta shafe shekaru shida da watanni takwas a gidan yarin Suleja kafin yi mata afuwa.

Talauci da tsangwama na hana yara mata karatu a Gombe — Kwamishina Gwamnan Kebbi ya bai wa sojoji kyautar motoci 6 da babura 30 don inganta tsaro

Rahotanni sun nuna cewar an yi mata afuwar ne bayan yin nadama da aikata kyakkyawan halaye.

Iyayen Maryam sun roƙi gwamnati da ta sake ta saboda ’ya’yanta biyu da ta ke da alhakin kula da su, tare da alƙawarin sauya halayenta.

Shugaba Tinubu, ya kuma yi wa wasu mutane afuwa da suka haɗa da Manjo Janar Mamman Vatsa, Ken Saro-Wiwa, da kuma Sir Herbert Macaulay.

Gaba ɗaya mutane 175 ne shugaban ya yi musu afuwa, ciki har da masu manyan laifuka, tsoffin fursunoni, da waɗanda suka yi kyakkyawan tuba.

Wannan shi ne karon farko da Shugaba Tinubu ya yi amfani da ikon yafe laifi don tausaya wa waɗanda suka aikata laifuka tun bayan hawansa mulki.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Cibiyar Lafiya Ta Nasser Ta Ce: Yaran Gaza 5,500 Suna Bukatar Agajin Gaggawa A Kasashen Waje
  • Yajin Aikin ASUU:  Ba za mu biya duk wanda bai yi aiki ba — Gwamnatin Tarayya
  • Gwamnatin Cuba ta yi watsi da zargin da Amurka ke yi na hannu a yakin Ukraine
  • Maryam Sanda na cikin waɗanda Tinubu ya yi wa afuwa
  • ’Yan sanda sun ceto mutum 10 daga hannun ’yan bindiga a Kaduna
  • Tinubu ya yi wa Maryam Sanda afuwa
  • Rashin wutar lantarki ta kassara kasuwanci a Kaduna, Kano da Katsina
  • Birnin Tarayya Zai Taimaka Da Tara Kudin Shiga Daga Fannin Da Bai Shafi Mai Ba — Dantsoho
  • An Zuba Jarin Dala Biliyan 5.2, An Sa Hannu Kan Yarjejeniyoyi 47 A Taron Tattalin Arziƙin Bauchi