2025-11-10@07:18:33 GMT
إجمالي نتائج البحث: 560

«makarantun Tsangaya»:

(اخبار جدید در صفحه یک)
    A Italiya mutane da dama sun jikkata yayin arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu. Rahotanni sun ce kimanin mutane 10 ne suka jikkata yayin zanga-zangar ta nuna goyon bayan Falasdinu bayan da ‘yan sanda suka yi kokarin hana masu zanga-zangar da ruwan zafi da hayaki mai sa hawaye a ranar Asabar. Zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu, wacce ta fara ranar Juma’a a Rome, Milan, Naples, da Bologna, ta bazu a ranar Asabar zuwa Florence, Pisa, Ancona, Trieste, Bari, da Alessandria. Zanga-zangar ta nuna goyon baya ga Gaza da al’ummar Palasdinu na karuwa a tashoshin jiragen ruwa, jami’o’i, makarantu, da wuraren taruwar jama’a a Italiya gabanin zanga-zangar kasa da aka shirya yi a ranar 4 ga Oktoba...
    Shirin AGILE, ya raba kayan koyarwa da na sana’o’i ga cibiyoyin karatun boko na wucin gadi guda 54 a faɗin Jihar Gombe. Kwamishiniyar Ilimi ta jihar, Dakta Aishatu Umar Maigari, ce ta ƙaddamar da rabon kayan a cibiyar Community Education Resource Centre da ke Gombe. HOTUNA: An kai gawar Arase Benin domin yi mata jana’iza Mutum 7 sun rasu yayin da tirela ta murƙushe motoci a Madalla Ta ce manufar shirin shi ne bai wa ɗalibai damar koyon karatu, lissafi da kuma sana’o’i domin su samu rayuwa mai inganci. “Ba wai kawai karatu muke son su samu ba, har da ƙwarewar sana’a da za ta taimaka musu da iyalansu,” in ji ta. Shugabar shirin AGILE ta jihar, Dakta Amina Haruna...
    Gwamnatin Tarayya ta amince da sabuwar dokar haraji wadda za ta bai wa ’yan haya damar samun ragin har Naira dubu ɗari biyar. Dokar ta amince da yi wa ’yan haya ragin kashi 20% daga harajin kudin shiga a kan kuɗin hayar da suke biya a shekara. Sojoji sun kashe ’yan ta’adda tare da ƙwato makamai a Neja Babu wata jam’iyya dana ke shirin komawa — Kwankwaso Sai dai kuma, wannnan ragin ba zai haura haura Naira 500,000 ba. Kafa sabuwar dokar A watan Agustan shekarar 2023 Shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamitin sake fasalin haraji karkashin jagorancin Taiwo Oyedele. Bayan shekaru biyu, Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da sabbin dokoki guda hudu, wadanda shugaban kasar ya rattaba hannu...
    Tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce ba su da matsala da yunkurin da aka ce tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na yi na komawa jam’iyyar. Sai dai Ganduje ya ce suna da sharadin da dole sai Kwankwason ya amince da shi kafin ya shiga jam’iyyar. Aminiya ta rawaito yadda majijoyi masu tushe suka tabbatar da cewa tuni Kwankwaso ya fara tattaunawa da shugaban APC na kasa, Nentawe Yilwatda, a kan batun komawar. Kwankwaso ya fara tattaunawa da Nentawe kan maganar komawa APC Sauya Sheƙa: Kwankwaso ya gindaya sharuɗa kafin sake komawa APC Amma a cikin wata tattaunawarsa da Sashen Hausa na BBC, ranar Juma’a Ganduje ya ce jam’iyyar tana da dokoki da sharudda,...
    Dakarun Yaman sun sanar da cewa, sun kai wani harin soji mai inganci ta hanyar amfani da makami mai linzami na “Falasdinawa 2” mai dauke da kawuna da dama, kan wasu hare-hare da Isra’ila ta kai a yankin Jaffa da ta mamaye. A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta Birgediya Janar Yahya Saree ya karanta, rundunar sojin kasar ta Yemen ta tabbatar da cewa farmakin ya cimma manufofinta tare da dakatar da zirga-zirgar jiragen sama a filin jirgin sama na Lod (Filin jirgin sama na Ben Gurion). A gefe guda kuma, Dakarun Yaman sun jaddada cewa, dakarun tsaron sama sun kame wasu jerin hare-haren Isra’ila da makamai masu linzami na sama zuwa sama, lamarin da ya dakile wani...
    Dangin wata yarinya ’yar shekara 14 a unguwar Gangare da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, sun nemi a bi musu haƙƙi bisa zargin fyaɗen da wani mazaunin unguwar ya yi mata. Bayanai sun ce tun farko an cafke mutumin da ake zargi, Ibrahim Rawi, wanda da fi sani da Baban Siyama, amma daga bisani aka sake shi bayan wasu dattawan unguwar sun sa baki. Matashi ya kashe kakanninsa saboda abinci a Kano An kashe ’ya’yan magoya bayan Gwamna Zulum Budurwar da abin ya faru da ita da ke koyon sana’a a wajen mutumin da ake zargi, ta ce lamarin ya faru ne tsakanin ƙarfe 7 zuwa 8 na daren ranar Lahadi yayin da ake ruwan sama. A cewarta:...
    Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta kama wani matashi ɗan shekara 30 mai suna Mutawakilu Ibrahim da laifin daɓa wa kakanninsa wuwa har lahira bayan wata taƙaddama kan abinci a Ƙofar Dawanau Ƙuarters da ke cikin birnin Kano. A cewar wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ta ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 25 ga watan Satumba, 2025 da misalin ƙarfe 9:30 na safe. An kashe ’ya’yan magoya bayan Gwamna Zulum Zan kare muradun Yarbawa idan aka zaɓe ni a 2027 — Atiku Rahotannin ’yan sanda sun nuna cewa, wanda ake zargin ya yi zazzafar taƙaddama da kakansa, Muhammad Dansokoto mai shekara 75 da kuma kakarsa, Hadiza Tasidi...
    Darajar Naira ta ɗan ƙaru a kasuwanni, bayan Babban Bankin Najeriya (CBN), ya sanar da rage kuɗin ruwa daga kashi 27.5 zuwa kashi 27. Wannan mataki, a cewar masana tattalin arziƙi, na nufin gwamnati na ƙoƙarin rage matsin tattalin arziƙi da farashin kayayyaki ga ’yan ƙasa. ’Yan bindiga sun kashe mai juna biyu, sun sace mutum 8 a Kwara Mawaki Davido ya ba matarsa kyautar motar miliyan 240 A ranar Talata, an sayar da dala ɗaya kan Naira 1,487.36 a hukumance, inda hakan ya nuna samun sauyi idan aka kwatanta da Naira 1,488.60 da aka sayar da ita a baya. Hakazalika, farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ya tashi zuwa dala 67.82 a kan kowace ganga ɗaya, abin da ya...
    Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau 22 ga wannan wata cewa, a yayin da ake raya duniya bisa tsarin bai daya, musayar kwararru a tsakanin kasa da kasa ta sa kaimi ga raya fasahohi da tattalin arzikin kasashen duniya. Kasar Sin tana maraba da kwararru daga bangarori da sana’o’i daban daban na kasa da kasa su zo kasar ta Sin su gudanar da harkokinsu don sa kaimi ga raya zamantakewar al’ummar dan Adam da kuma samun ci gaban sha’aninsu baki daya. (Zainab Zhang) Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da...
    A halin yanzu, shugaba Bola Tinubu yana ganawa da gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a fadar shugaban kasa dake Abuja a yammacin yau Litinin. Ganawar na zuwa ne kwanaki kadan bayan Fubara ya koma ofis a ranar 19 ga watan Satumba bayan da Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da aka kafa a jihar Ribas tun farko. Tinubu ya bayyana matakin ne domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali bayan shafe watanni ana rikicin siyasa da ke barazana ga harkokin mulki da tsaro a jihar mai arzikin man fetur. Cikakken bayanai na nan tafe… Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu...
    Wani jariri ya rasu a bayan mahaifiyarsa a yayin da take guje wa harin ’yan bindiga a kauyen Allawa da ke Karamar Hukumar Shiroro a Jihar Neja. Sarkin yankin Bassa, Bagudu Amos, ne ya bayyana hakan a lokacin taron tattaunawa da mata kan zaman lafiya da kare su daga cin zarafi, mai taken: “Ƙarfafa kariya daga cin zarafin jima’i da na jinsi a Jihar Neja.” Kungiyar Tunani Initiative, tare da goyon bayan Dorothy Njemanze Foundation da Ford Foundation, ce ta shirya taron domin ƙarfafa mata wajen yaki da cin zarafi da ke ƙara ta’azzara a sakamakon rashin tsaro. Bagudu Amos ya bayyana cewa mahaifiyar ta yi tafiya mai nisa a kafa da jaririn a bayanta domin tserewa daga harin ’yan...
    Sanarwar ta ƙara da cewa, an bayar da ƙarin kayayyakin da za a raba a matsayin tallafin ne daga Hukumar Kula da Ilimi ta Duniya (UBEC) da UNICEF.   A jawabinsa a wajen taron, Gwamna Lawal ya sake nanata cewa gwamnatinsa ta zo ne da aikin ceto da sake gina jihar.   Ya ce: “Tun da farko mun gane cewa hanya mafi inganci wajen dawo da Zamfara kan turba ita ce saka hannun jari a zukatan al’ummarmu.   “A yau, a cikin wannan alƙawari, na yi farin cikin sanar da raba kayayyakin koyo da koyarwa 408,137 da gwamnatin jihar Zamfara ta sayo kai-tsaye.   “Wannan shi ne ɗaya daga cikin mafi girma na zuba jari a cikin albarkatun koyarwa da...
    Rundunar Sojin Saman Najeriya, ta kashe ’yan ta’addan Boko Haram 32, a wani farmaki da ta kai garin Banki da ke Ƙaramar Hukumar Bama, a Jihar Borno. Rahoton ya bayyana cewa farmakin ya auku ne a ranar 18 ga watan Satumba da misalin ƙarfe 10:15 na safe. Bayan biyan N50m an sako ma’aurata da ’yarsu su da aka sace a Katsina Mutum 9 sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Sakkwato Wannan na zuwa ne bayan ’yan ta’addan sun kai hari hedikwatar ’yan sanda da ke Banki. A lokacin kai farmaki , sojoji biyu sun rasa rayukansu, haka kuma wani ƙaramin yaro mai shekara tara, Ismail Abubakar, ya rasu. Har ila yau, maharan sun ƙone motocin soja uku. Bayan kai...
    Ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta jihar Jigawa, ta shirya taron yini daya a birnin tarayya tare da hadin gwiwar ELIP kungiyar farar hula ta musamman, domin tattara kayan aiki na kasafin kudin 2026.   A nasa jawabin kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na jihar Alhaji Ibrahim Babangida Umar Gantsa ya bayyana mahimmancin taron, inda ya ce abubuwan da masu ruwa da tsaki suka yi na da matukar muhimmanci.   Babangida Gantsa wanda ya samu wakilcin Daraktan SDG na ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta jiha, Alhaji Basiru Nasoro ya bukaci masu ruwa da tsaki su samar da bayanai masu ma’ana.   A nasa jawabin, Alhaji Najibullah Ahmad wanda masanin kasafin kudi ne ya bayyana cewa, makasudin shi ne a...
    Shugaban kungiyar goyon bayan Sanata Marafa, Alhaji Surajo Garba Maikatako, ya ce ficewar Sanata Kabir Garba Marafa daga jam’iyyar APC ya kara karfafa masa siyasa tare da jaddada goyon bayansa ga magoya bayansa.   A wata sanarwa mai dauke da sa hannun sa da kan sa, Alhaji Maikatako ya bayyana cewa Sanata Marafa ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar APC ba wani yunkuri ne na kashin kai ba, sai dai an dauki matakin ne na gama-gari bayan tattaunawa da magoya bayan sa.   Ya ce tun bayan wannan sanarwar kungiyar ta fara samun sakonni da ziyarce-ziyarcen hadin kai daga fadin jihar Zamfara da Arewa maso Yamma da kuma wajenta, inda da yawa ke bayyana shirin tafiya da sabuwar alkiblar siyasa....
    Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya dawo bayan shafe tsawon lokaci baya jihar biyo bayan sanya dokar ta-ɓaci da  Shugaba Tinubu ya yi. A ranar Laraba ne Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci, wadda tsohon Hafsan sojan ruwa, Vice Admiral Ibok-Ekwe Ibas (rtd), ya jagoranta. ’Yan bindiga sun kai hari sakatariyar ’yan jarida ta jihar Yobe An dakatar da shugabannin sakandare 6 a Sakkwato kan zargin cin amanar aiki Magoya bayan gwamnan sun taru a gidan gwamnatin jihar da ke Fatakwal domin tarbarsa bayan dakatar da shi na tsawon watanni shida, amma daga baya suka watse bayan shafe lokaci suna jira ba tare da ganinsa ba. Da safiyar ranar Juma’a, magoya bayan suka koma Filin Jirgin Sama na Fatakwal. Jirgin...
    A cewar ma’aikatar, dakatarwar ta na nufin samar da damar ci gaba da tattaunawa da duk masu ruwa da tsaki da kuma yin cikakkiyar bitar tsarin harajin da tasirinsa na dogon lokaci ga tattalin arziki. A watan Afrilu 2025, Kwaturola Janar na Kwastom, Adeniyi, ya bayyana shirin sake gabatar da harajin kashi 4 bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, cewa wannan cajin, wanda ake lissafawa bisa Free on Board (FOB) na kayan da ake shigowa da su, an riga an sokƙ shi a baya daga al’umma masu kasuwanci saboda nauyinsa ga masu shigo da kaya. Nan da nan sanarwar ta jawo cece-kuce daga ƴ an kasuwa, kamfanonin jigilar kaya, da ƙungiyoyin masana’antu, waɗanda suka bayyana cewa matakin zai rage...
    Magoya bayan Gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara, sun yi dafifi a Gidan Gwamnati da ke Fatakwal domin tarbar shi da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, bayan dawowarsu ofis. Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Fubara na tsawon watanni shida a lokacin da rikicin siyasa ya yi ƙamari a jihar. Gwamnatin Tarayya ta raba wa talakawa N330bn — Ministan Kuɗi ’Yan bindiga sun sako ma’auratan da suka sace a Katsina bayan biyan N50m Sai dai a ranar Laraba, Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci tare da umartar gwamnan, mataimakiyarsa da ’yan majalisar dokokin jihar da su koma bakin aiki daga ranar Alhamis, 18 ga watan Satumba. A halin yanzu, tsohon shugaban riƙon ƙwarya na jihar, Rear Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya), ya miƙa mulki...
    Juventus za ta yi kokarin daukar dan wasan tsakiyar Portugal Bernardo Silva, mai shekara 31 a kyauta idan kwangilarsa da Manchester City ta kare a bazara mai zuwa. (Tuttosport) Ita ma Manchester City tana tunanin zawarcin dan wasan Manchester United Kobbie Mainoo, duk da cewa tana iya fuskantar gogayya daga Newcastle da kuma Chelsea kan dan wasan tsakiyar na Ingila mai shekara 20. (Teamtalk) Chelsea ta ci gaba da zawarcin Morgan Rogers duk da cewa Aston Villa ta sanya farashin fam miliyan 80 kan dan wasan gaban na Ingila mai shekara 23. (Sun) Karin kudin shiga da Manchester United ta samu a baya-bayan nan ya ba ta damar siyan dan wasan tsakiya na Brighton da Kamaru Carlos Baleba, mai shekara 21. (Mirror) Liverpool...
    Masu bincike a Turai sun yi amfani da fasahar ƙirƙirariyyar basira ta AI don yin hasashen matsalolin lafiya da ɗaiɗaikun mutane za su iya fuskanta cikin shekaru goma masu zuwa ko fiye na rayuwarsu. Sun ce fasahar na amfanin da bayanan rashin lafiyar da mutum ya yi a baya, domin hasashen cutuka fiye da dubu ɗaya da ke barazanar kama mutum, tun ma kafin soma bayyana. An wallafa cikakkun bayanan binciken – da suka bayyana da gagarumar nasara – a mujallar kiwon lafiya ta Nature. An horar da fasahar AI ɗin ta hanyar amfani da bayanan lafiyar mutane dubu ɗari huɗu – da ba a bayyana sunayensu ba – a Birtaniya da Denmark. Zuwa yanzu ba a soma amfani da...
    Babban sakataren kungiyar Hizbullah, Sheikh Naim Qassem, ya yi jawabi ga wadanda suka tsira daga kisan Pager a bikin cika shekara guda da aiwatar da wannan harin ta’addanci da Haramtacciyar Kasar Isra’ila ta yi a ranar 17 ga Satumba, 2024. “Ku ne masu gani na gaskiya, tushen begenmu, kuma sadaukarwar ku ga Allah ita ce ke ba wa rayuwa ma’anarta ta har abada, ku ne hasken da ke shiryar da mu domin bin hanya, kuma juriyarku ita ce zuciyar juriyarmu,” in ji Sheikh Qassem a cikin sakonsa ga mutanen da suka jikkata a harin. “Me zan iya ce muku? Don yanzu ku ne malamai, masu ba da shawara, ku ne jagorori, saboda kun yi sadaukarwa kuma kuna a kan yi,...
    More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba A yau ne Gwamna Siminalaye Fubara ke dawowa kujerarsa a matsayin gwamnan Jihar Ribas bayan dakatarwa da ayyana dokar ta baci na watanni shidda da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi a jihar.   Manazarta dai na hasashen wannan dawowar zata bude wani sabon babi a siyasar jihar Ribas. NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba DAGA LARABA: Dalilan Tashin Farashin Doya A Wasu Kasuwannin Najeriya Yayin da wasu ke ganin gwamna Fubara zai koma bakin aiki ne ya cigaba da gudanar da mulkin jihar kamar yadda ya barta, wasu kuwa gani sukeyi akwai babban kalubale dake gaban gwamnan. Domin sauke shirin, latsa nan
    A wani yunkuri na inganta kula da mata masu juna biyu da sauran ayyukan kiwon lafiya a jihar Jigawa, Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF tare da hadin gwiwar Karamar Hukumar Kirikasamma sun mika kayayyakin aiki da wasu muhimman kayayyaki ga cibiyar kiwon lafiya ta farko a Kirikasamma. Mai kula da cibiyar kiwon lafiya ta farko, Kabiru Musa, ya bayyana cewa kayayyakin sun haɗa da gadajen haihuwa, zannuwan gado, kayan aikin jinya, matashin kai da sauransu, kuma za a rarraba su zuwa wuraren kiwon lafiya a fadin karamar hukumar. A cewarsa, kayan da UNICEF da karamar hukumar suka samar za su inganta yadda ake gudanar da ayyukan kiwon lafiya a yankin. Yayin mika kayayyakin ga mai...
    Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yabawa Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta Jiha bisa ƙirƙirar Kyautar Malami Mafi Nagarta, yana mai bayyana hakan da ɗaya daga cikin manyan manufofin da za su ƙarfafa koyo da koyarwa a fadin jihar. A cikin wata sanarwa da Babban Jami’in Yaɗa Labaran sa, Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, gwamnan ya bayyana cewa bikin na farko na bada lambar yabo da aka gudanar a Dutse ya dace domin girmama malamai da suka yi fice ta hanyar jajircewa da sadaukar da kai. Ya ƙara da cewa wannan mataki zai ƙara kwarin gwiwa, ya samar da gasa mai kyau, tare da inganta darussa a makarantu. Namadi ya jaddada cewa ingancin ilimi bai tsaya kan gina...
    A bayan bayan nan, an aiwatar da jerin tattaunawa tsakanin Sin da Amurka karkashin jagorancin shugabanninsu, inda aka samu kyawawan sakamakon da ya kyautata alakarsu ta tattalin arziki da cinikayya. Wannan ya nuna shawarar da a kullum Sin ke bayarwa cewa, tattaunawa ita ce mafita ga dukkan rikice-rikice, maimakon amfani da karfi. Kasar Sin ta sha nanata cewa, babu mai samun nasara a yakin cinikayya ko haraji. Mun ga yadda aka samu hauhawar farashin kayayyaki da karuwar rashin aikin yi da faduwar darajar hannayen jari a Amurka, a lokacin da ta kaddamar da yakin haraji, wanda ya nuna cewa, maimakon cimma abun da take fata na samun fifiko, asara aka samu da lalacewar muradun kamfanoni da ’yan kasuwar kasar. Kowace...
    Gwamnatin Tarayya ta ce Najeriya na rasa sama da Dala Biliyan 10 duk shekara sakamakon asarar amfanin gona bayan girbi. Ministan Noma  Sanata Abubakar Kyari ne ya bayyana haka a wajen kaddamar da shirin Hanyar Inganta Noma da Kayayyakin Mire Rayuwa a Yankunan Karkara G.R.A.I.N a ƙaramar hukumar Birnin Kudu ta  Jihar Jigawa.   Ya ce asarar na faruwa ne saboda rashin ingantattun wuraren ajiya, karancin ababen more rayuwa, sauyin yanayi da kuma ambaliya. Kyari ya bayyana cewa noma na bada gudunmawar kashi 24 bisa 100 na Jimillar Darajar Kayayyaki da Ayyuka da Kasa ta Samar a Cikin Shekara GDP, inda ƙananan manoma ke samar da sama da kashi 70 bisa 100 na abincin da ake ci a ƙasa....
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Bayan kwashe makonni manyan ‘yan takara a jam’iyyun adawa da sauran jiga-jigan ‘yan siyasa na tuntubar juna domin ganin an fitar da dan takara daya tilo, da yammacin ranar Asabar 13 ga watan nan na Satumba, 6 daga ciki sun amince da tsohon minista kuma mafi kusanci ga gwamnati tsawon shekaru 16, wanda ya taba zama mai magana da yawun gwamnati a matsayin wanda zai fafata da Paul Biya na jam’iyyar RDPC wanda ya kwashe sama da shekaru 42 ya na mulkin kasar da ke tsakiyar Afirka. An zabe shi ne daga cikin ‘yan takara na jam’iyyun adawa 6 cikin 12 da hukumar zabe ta tabbatar da su a matsayin wadanda suka cancanci takara, karkashin inuwar gamayyar Union du Changement....
    An gano gawar Haneefa, yarinya ’yar shekara uku da ruwa ya tafi da ita lokacin da yayarta Fatima, ke goye da ita yayin ambaliyar da ta rutsa da su a Tudun Jukun da ke Zariya, a Jihar Kaduna. An tsinci gawar ne bayan kwanaki shida da aka kwashe ana nemanta, a gangaren ƙasan Kilaco, unguwar Gyallesu, da misalin ƙarfe 11 na safiyar ranar Lahadi. Ambaliya: NEDC ta raba wa mutum 2,200 kayan agaji a Yobe Likitoci sun janye yajin aikin da suka fara bayan kwana biyu Babban jami’in ƙungiyar Red Cross a Zariya, Abdulmumin Adamu ne, ya tabbatar da gano gawar, inda ya ce hakan ya kawo ƙarshen binciken neman mutanen da ruwa ya tafi da su. A ranar 8...
    Kamar yadda Oche, wadda ‘ya’yan ‘yar’uwarta suke zuwa makarantar Reno ta Oluwami da Firmare , da take Abuja inda shekarun baya suke biyan wajen Naira 600,000 ko wane zangon karatu, saboda wasu haraje- harajen da aka haɗa da su ciki. “Maganar gaskiya kowace shekara idan za’a shiga sabon zangon karatu, makarantu su kan ƙara kuɗin makaranta, su ƙara wasu sabbin abubuwa, kamar su kuɗin ICT, wasanni tsaro. Sai dai ƙarin da akwai matuƙar matsala.” A makarantar( Prime School ) da ke, Karu,inda aka ƙiyasta ana biyan kusan Naira 300, 000, kowane zangon karatu,wani Malamin da baya son a ambaci sunansa ya ce, akwai ƙarin kuɗin makaranta waɗanda suna da alaƙa ne da lamarin daya shafi kayn zuwa makaranta, bunƙasar makaranta,...
    Kungiyar Likitoci masu neman ƙwarewa (NARD) ta sanar da janye yajin aikin gargaɗi da ta fara bayan kwanaki biyu kacal. Sai dai ƙungiyar ta sake bai wa Gwamnati Tarayya mako biyu ta biya buƙatunta ko ta sake tsunduma yajin aiki. Shugaban ƙungiyar, Dakta Tope Osundara ne ya bayyana haka a ranar Asabar tare da umartar ɗaukacin mambobinsu da su koma aiki a yau Lahadi. Osundara, ya ce gwamnati ta biya musu wasu daga cikin buƙatunsu, tare kuma da alƙawarin duba sauran batutuwan da suke yajin aiki akan su. Tun a daren Juma’a ne likitocin masu neman ƙwarewa suka tsunduma yajin aikin na gargaɗi, bayan ƙarewar wa’adin da ƙungiyar ta ba Gwamnatin Tarayya kan batutuwan da suka shafi albashi, alawus, da...
    Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhakan, sharbin bayan labarammu a yau zasu yi magana dangane da ‘yiyuwar gwamnatin kasar Qatar ta nemi maye gurbim Amurka a bangaren tsaron kasarta, bayan cin amanan da Amurka ta yi a ranar talatan da ta gabata. Kamfanin dillancin labaran Parstoday, ta nakalto wani shafin labarai na yanar gizo a Amurka ‘Axios’. A ranar Alhamis da ta gabata ce, shafin yanar gizo na Acios na labarai ya nakalto Firay ministan kasar Qatar tana fadawa  fadar white House kan cewa, bayan saba alkawalin da Washington ta yi, dangane da hare-haren da HKI ta kaiwa birnin Doha, Qatar zata sake duba yarjeniyar tsaron da ke tsakaninta da Amurka ta kuma nemi sabon abokin aiki a wannan...
    Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tarbi tagwayen da aka haifa manne da juna, inda aka raba su da juna ta hanyar yi musu tiyata a Ƙasar Saudiyya. Tagwayen waɗanda ’yan asalin Najeriya ne, sun iso filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, inda tawagar Saudiyya ta tarbe su. Ambaliya: SEMA ta raba kayan tallafi ga gidaje 90 a Gombe ’Yan bindiga sun harbi fasinjoji 2, sun sace makiyaya a Neja An yi musu tiyata a Asibitin Ƙwararru na Yara King Abdullah da ke Riyadh, bisa umarnin Sarki Salman bin Abdulaziz Al-Saud da Yarima Mohammed bin Salman. Hassana da Husaina sun tafi Saudiyya tun a watan Oktoban 2023, inda likitoci suka gano cewa suna manne da juna ne ta...
    A yau da safe, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya gudanar da jerin tarukan manema labarai mai taken “Kammala shiri na 14 na shekaru biyar-biyar na raya kasa mai inganci”, inda aka yi karin haske kan ci gaban da aka samu a fannin kafa tsarin shari’a a kasar Sin a wa’adin gudanar da shirin.   An bayyana yayin taron cewa, a wa’adin shirin, hukumomin shari’a sun ci gaba da inganta tsarin kasuwanci bisa shari’a, da cibiyoyin kula da lafiyar jama’a a matakin gundumomi, kuma sun fara aiki gaba daya, kana an hukunta manyan laifuka bisa doka. Taron ya kuma bayyana kasar Sin a matsayin daya daga cikin kasashen da aka amince da su a duniya a...
    Ƙungiyar Likitocin Masu Neman Ƙwarewa a Nijeriya (NARD) ta tsunduma cikin yajin aikin ƙasa baki ɗaya, bayan gwamnatin tarayya ta kasa cika mafi ƙarancin bukatun da ƙungiyar ta gabatar cikin wa’adin sa’o’i 24 da ta sanya. Wannan mataki ya zo ne bayan kammala taron gaggawa na Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (E-NEC) ta yanar gizo a ranar Laraba, 10 ga Satumba, 2025. Shugaban ƙungiyar na ƙasa, Dakta Osundara Tope Zenith, ya tabbatar da hakan, inda ya ce yajin aikin ya zama dole bayan shiru daga bangaren gwamnati. Ƙungiyar ta jaddada cewa rashin biyan Kudaden Tallafin Koyan Aiki (MRTF) ga wasu asibitoci, tare da rashin biyan alawus na watanni biyar daga karin kaso 25% da 35%, da sauran hakkoki da aka dakatar...
    Kungiyar Likitocin Masu Neman Kwarewa ta Najeriya (NARD) ta umurci mambobinta da su dakatar da aiki a dukkan asibitocin gwamnati da ke fadin Najeriya daga yau Juma’a. Wannan mataki ya biyo bayan karewar wa’adin sa’o’i 24 da kungiyar ta bai wa Gwamnatin Tarayya don cika bukatunsu da ba a biya ba. Wa’adin ya biyo bayan karewar wani wa’adin na kwanaki 10 da ya kare a ranar 10 ga Satumba ba tare da an biya wa likitocin bukatun nasu ba. Ambaliyar ruwa ta tsayar da ababen hawa cak a tsakiyar birnin Abuja Jonathan ya tattauna da Peter Obi kan tsayawa takara a 2027 A ranar daya ga watan Satumba, NARD ta gargadi gwamnati cewa za ta fara yajin aikin sai baba...
    Ƙungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Najeriya (NARD) ta bai wa Gwamnatin Tarayya sabon wa’adin kwana ɗaya domin ta cika buƙatun da take nema. Hakan dai na zuwa ne bayan wa’adin farko na kwanaki 10 da suka bayar, wanda ya ƙare a ranar Talata, 10 ga Satumba. An saki fursunonin siyasa 52 a Belarus Daruruwan magoya bayan NNPP sun tarbi Kwankwaso a Kalaba Matakin da ƙungiyar ta ɗauka na zuwa ne a ƙarshen wani taron gaggawa da shugabanninta suka gudanar a ranar Laraba, domin nazarin ci gaban da aka samu tun bayan bayar da wa’adin farko. Shugaban ƙiungiyar Dr. Tope Osundara ya ce sun saurarin alƙawurran da gwamnatin Najeriya ta yi masu game da buƙatun nasu amma suna neman a...
    Rahotanni sun bayyana cea Shugaban nigeria Bola Tinubu ya umarci wani kwamiti na Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da ya dauki matakai don karya farashin abinci a fadin Nijeriya. Sanata Sabi Abdullahi, Ministan Noma ne, ya bayyana hakan a lokacin wani taron horaswa na kwana daya ga ‘yan jarida a Abuja ranar Laraba. Ya ce shirin rage farashin kayan abinci ya hada da tabbatar da cewa kayan noma suna tafiya cikin tsari da farashi mai sauki. Sanata Abdullahi ya kara da cewa, tsadar jigilar kayan amfanin gona shi ne daya daga cikin dalilan da ke sanya abinci ya yi tsada a kasuwanni. Ya ce kwamitin na FEC yana aiki don tabbatar da jigilar kayan amfanin gona sun zama masu sauki,...
    Ya ƙara da cewa wannan mataki yana cikin hangen nesan Shugaba Tinubu a kan abinci, wanda ke nufin samar da abinci mai sauƙi ga kowa. Ministan ya kuma ambaci shirye-shiryen da ake shirin aiwatarwa, kamar Shirin Lafiyar Ƙasa na Manoma, waɗanda ke nufin inganta rayuwar manoma. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Shugaban Kasa Bola Tinubu ya umarci Kwamitin Majalisar Zartarsa ta Kasa da ya dada aiwatar da matakan da za su kara karya farashin kayan abinci a fadin Najeriya. Karamin Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja. EFCC ta tsare Mele Kyari kan binciken matatun mai Macron ya karɓi baƙuncin Tinubu a Fadar Elysee Ya ce umarnin ya shafi tabbatar da cewa an rage farashin sufurin kayan amfanin gona ba tare da kashe makudan kudade ba. “Shugaban Kasa ya bayar da umarni ga Kwamitin Majalisar Zartarsa ta Kasa wanda dama yanzu haka yana nan yana kokarin ganin an saukaka hanyoyin sufurin amfanin gona a fadin kasar nan, da su dada...
    Wasu ’yan bindiga da ake zargin sun shigo cikin al’umma sanye da hijabai sun yi garkuwa da mutane 11 ciki har da masallata guda uku a Jihar Zamfara. Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Lahadin da ta gabata a garin Dansadau da ke Karamar Hukumar Maru, kamar yadda rahotanni daga shafin Zagazola Makama suka tabbatar. An cafke mace mai safarar wiwi da ’yan fashi 4 a Gombe An kama mutum biyu kan zargin yi wa ƙananan yara fyaɗe a Kebbi Makama wanda kwararren mai sharhi kan yaki da tayar da kayar baya ne ya ce ‘yan bindigar sun shiga garin ne sanye da hijabai da rigunan mata da suka yi basaja da su, inda suka yi awon gaba da...
    Kungiyoyin gwagwarmayar Falasdinawa da dama sun bayyana bacin ransu kan barazanar da ministan yakin Isra’ila ya yi na bude “kofofin jahannama” a zirin Gaza. Wannan martanin ya zo ne a ranar Juma’a bayan da Isra’ila Katz ya ayyana cewa gwamnatin sahyoniyawan na gab da maida yankin jahannama a gabar tekun. Katz, ya bayyana cewa sojojin Isra’ila za su zafafa kai hare-hare har sai kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas ta sako mutanen da aka kama. A nata bangaren, Hamas ta ayyana barazanar Katz a matsayin “kalubale da ba a taba ganin irinsa ba ga dokokin kasa da kasa da ka’idojin jin kai.” Kalaman na Katz na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar ta riga ta ba da damammaki don ba...
    Ya kuma sanar da ci gaba da bai wa shugabancin Dakta Dantsoho goyon baya, musaman domin kara samar da sauye-sauyen da za su kara bunkasa hada-hadar zirga-zirga, da kuma a bangaren kara bunkasa kasuwancin tatalin azrki na Teku. A nan kuma Kamfanin Rukunonin SIFAD, ya taya Dakta Dantsoho murnar zama Mataimakin Shugaban na kungiyar ta IAPH. Hakan na kunshe ne, a cikin wata wasika da Shugaban Kamfanin Dakta Taiwo Afolabi CON ya fitar ta taya murnar, inda ya danganta zabar Dantsoho kan mukamanin a matsyin abinda ya dace, musamman duba irin salon shugabanci na gari na Dakta Dantsoho, wanda hakan ya sanya ya samar da gagarumar gudunmawa a bangaren sufurin Jiragen Ruwa na kasar. Shugaban sashen samar da bayanai na...
      “Kowace ranar 12 ga watan Rabi’ul Auwal rana ce ta murnar zagayowar ranar haihuwar Manzonmu mai albarka (SAW).   “Wannan lokaci ne mai kyau da ya kamata dukkan Musulmi su yi koyi da rayuwar Manzon Allah (SAW).   “Musulunci ba addini kawai ba ne, hanya ce ta rayuwa, rayuwar Annabi (SAW), ta shiryar da mu zuwa ga kyawawan ɗabi’u, halaye da ayyuka.   “Ya kamata mu yi amfani da irin waɗannan muhimman lokuta na addini domin mu dage da addu’o’in samun zaman lafiya a Jihar Zamfara, Arewa maso Yamma, da ƙasa baki ɗaya.   “Allah (T) ya kawo mana ƙarshen ta’addanci da duk wani nau’in aikata laifuka a cikin al’ummarmu.” Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun...
    Siyasar Jihar Gombe ta ƙara ɗaukar zafi yayin da fitaccen ɗan siyasar nan, Umar Faruk FK, ya fice daga jam’iyyar PDP tare da dimbin magoya bayansa, tare da komawa APC. FK, ya bayyana cewa PDP ta gaza bayar da shugabanci nagari a jihar, shi ya sa ya yanke shawarar barin ta. 2027: ’Yan adawa na ƙoƙarin sanya APC fara kamfe da wuri — Tinubu Kwankwaso zai iya komawa APC – Abdulmumin Kofa Ya ce ya mara wa Gwamna Inuwa Yahaya baya bisa ayyukan ci gaba da ya ke gudanarwa. “Marar kishin Gombe ne kawai ba zai ga nasarorin da gwamnatin Inuwa Yahaya ke samu ba,” in ji Umar FK. Ya ƙara da cewa shi da magoya bayansa za su mara...
    A cewar wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya fitar, shugaban ya kuma umarci da a maido da babban daraktan yada labarai, Mista Ayo Adewuyi ya kammala wa’adinsa na ragowar shekaru uku, wanda zai kare a shekarar 2027.   Shugaba Tinubu ne ya nada Adewuyi a shekarar 2024. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Yanzu an fi wata biyu da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da taraktoci 2,000 da sauran kayan aikin gona domin haɓaka harkar noma, amma manoma sun ce har yanzu ba a raba musu su ba, abin da ke iya jawo asarar daminar bana. Ganin cewa a halin daminar tana gab da ƙarewa, manoma suna ganin lokaci ya riga ya ƙure. Ƙungiyoyin manoma sun soki jinkirin, suna gargaɗin cewa ana iya fuskantar ƙarancin abinci idan ba a hanzarta ba. Da yake ƙorafi kan lamarin, Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), Injiniya Kabiru Ibrahim ya ce, “Ina rokon gwamnati ta hanzarta. Wannan shekarar ce ta gwaji wajen tabbatar da tsaron abinci.” Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewa...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dakarun Operation Haɗin Kai (OPHK) tare da Civilian JTF, sun yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram da ISWAP 12 a Jihar Borno. A ranar 29 zuwa 30 ga watan Agusta, sojojin sun kai farmaki ƙauyukan Tamsu Ngamdu, Dalakaleri, Gaza da Loskori Kura, inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan. Tsohon Sufeto-Janar na ’yan sandan Nijeriya Solomon Arase ya rasu An ƙone wata mata ƙurmus kan yi wa Annabi ɓatanci a Neja A Loskori Kura, sojojin sun yi nasara, inda suka kashe ’yan ta’adda 12, suka kuma kwato8 bindiga ƙirar AK-47 guda shida, harsasai guda takwas da magunguna iri-iri. Majiyoyin tsaro sun ce wasu daga cikin ’yan ta’addan sun ji raunuka, bayan artabun da suka yi da sojojin. Wannan farmaki ya...
    Gwamnonin Jihohin Arewa maso Gabas, sun koka kan matsalolin da suka shafi ayyukan jin-ƙai da kuma gina muhimman ababen more rayuwa duk da ci gaban da aka samu a yaƙin da ta’addanci a yankin. Wannan bayani ya fito ne daga sanarwar ƙarshen taronsu karo na 12 da aka gudanar a Jalingo, Jihar Taraba. Ambaliya: NEMA ta raba kayan tallafi a Yobe  An kama direban mota da jabun kuɗin N1m a Oyo Taron ya gudana ne ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar, Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum. A yayin taron, gwamnonin sun nuna damuwa kan yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu jihohin yankin. Don haka sun buƙaci a ɗauki matakan gaggawa da kuma neman taimakon Gwamnatin Tarayya da hukumar NEDC domin...
    Ya bayyana cewa, “A ranar 16/08/2025, da misalin karfe 03:20 na dare, an samu kiran gaggawa daga wani da ba a bayyana sunansa ba, yana sanar da cewa tsakanin karfe 02:00 da 03:00 na dare, wata kungiyar ‘yan fashi kusan 20 dauke da makamai sun afka unguwar Madina da bayan tsohon makabarta a unguwar Fadaman Mada, inda suka shiga gidaje da dama suka yi wa mazauna sata tare da kwace musu kayayyaki masu daraja.”   Wakil ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda daga sashen C Dibision, karkashin jagorancin Dibisional Police Officer, sun hanzarta zuwa wurin tare da hadin gwiwar ‘yan sa-kai. Da zarar ‘yan fashin suka hango jami’an, sai suka tsere suka bar wasu daga cikin kayayyakin da suka sace.  ...
    Dantsoho ya sanar da cewa, tun lokacin da aka yi aikin Tashoshin Jiragen Ruwa na Tin Can Island shekaru 48 da kuma aikin Tashar Jiragen Ruwa ta and Apapa 103 a shekaru da suka gabata, babu wani yunkuri da aka yi, na gyransu ko kuma kara daga darajarsu.   Shugaban ya kuma koka kan yadda aka shafe wadannan shekarun masu yawan gaske, ba tare da an yi masu wani gyara ba.   Ya buga misali da kananan Tashoshin Jiragen Ruwa na kasasehe kamar na Togo, Côte d’Iboire da Ghana, wanda suka kasance, Tashoshin Jiragen Ruwa da manyan Jiragen Ruwa ke sauka. A cewar Shugaban irin lalacewar da kayan aiki a Tashoshin Jiragen Ruwan kasar suka yi, abu ne, da ya...
    Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Ƙasa ta Najeriya (NRC) ta fara aikin gyara layin dogon Abuja zuwa Kaduna da ya lalace sakamakon hatsarin jirgin kasa. A ranar Talata da ta gabata ce jirgin mai tarago 10 da ya tashi da misalin karfe 11:00 na safe daga tasharsu da ke Kubwa a Abuja da nufin zuwa Kaduna, rikito daga kan hanyarsa a wata ƙaramar tasha da ke kauyen Asham, ’yan mintoci kalilan bayan fara tafiyar. Hadimin Gwamnan Kano ya maka mawallafin Daily Nigerian a kotu saboda kiransa da ‘ɓarawo’ NAJERIYA A YAU: “Abin Da Ya Sa Muka Dawo Daga Rakiyar Kirifto” Injin jirgin da kuma tarago biyu da ke biye masa sun samu mummunar illa, a yayin da ragowar taragu shida...
    Shugaban gamayyar masu goyon bayan Gwagwarmaya a kasar Lebanon suna tare da kungiyar sannan wadanda suke nanata cewa sai an takaita makamai a hannun gwamnati sun aiki ne wa HKI da Amurka . Tashar talabijan ta Al-Manar ta kungiyar ta nakalto shugaban gamayyar Mohammad Ra’ad yana fadar haka ya kuma kara da cewa abinda ya faru a ranar 5 ga watan Augustan mai karewa wani kuskure ne wanda gwamnatin kasar Lebanon bata taba irinsa ba. Kuma yana dai da kamar abinda ya faru a karbala ne, inda wani sojan yazid ya fadawa yan uwansa kan cewa ku shaida mani wanin nYazid kann cewa ni na fara harban kibiya kan Al-Hussain. Abinda gwamnatin kasar Lebanon tayi na neman yardar Amurka da...
    Ya ƙara da cewa jam’iyyarsu ta ADC za ta iya fito da ‘yan takara daga kowace shiyya, duk da cewa APC da PDP sun nuna cewa daga Kudu za su fito da ɗan takara a 2027. Duk da cewa wasu na ganin tasirinsa ya ragu a Jihar Ribas saboda rikicin siyasa tsakaninsa da Nyesom Wike, Amaechi ya ce har yanzu yana da goyon baya sosai. Ya bayar da misalin yadda aka tarbe shi a Jihar a baya-bayan nan ba tare da ya biya kowa kuɗi ba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a...
    Majalisar ministocin Sudan ta yi taronta na farko a birnin Khartoum fadar mulkin kasar tun shekara ta 2023 da ta gabata Majalisar ministocin Sudan ta yi taronta na farko a birnin Khartoum fadar mulkin kasar a ranar Talata, tun bayan barkewar yaki a kasar a tsakiyar watan Afrilun shekarar 2023. Kamfanin dillancin labaran Sudan ya bayar da rahoton cewa, “Gwamnatin bege” karkashin jagorancin fira ministan kasar Kamil Idris, “ta tattauna, a zamanta na farko na hukuma a birnin Khartoum bayan kafuwarta, game da tsare-tsaren ma’aikatun na wannan shekara, inda suka mai da hankali kan ayyukan jama’a da rayuwar jama’a, tsaro na ‘yan kasa, sake gina kasa, da tabbatar da dawowar ‘yan kasar da suka yi gudun hijira bisa radin kansu....
    A yau Talata 26 ga wata ne, firaministan kasar Sin, Li Qiang, ya isar da sako zuwa ga Nestor Ntahontuye, don taya shi murnar zama sabon firaministan kasar Burundi. A sakon nasa, firaminista Li ya bayyana cewa, a ’yan shekarun nan, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, wato Xi Jinping da Evariste Ndayishimiye, an cimma manyan nasarori wajen inganta hadin-gwiwar kasashensu a fannoni daban-daban. A yayin taron kolin dandalin tattaunawa kan hadin-gwiwar Sin da Afirka wato FOCAC, wanda aka yi a watan Satumban bara a Beijing, shugabannin biyu sun cimma matsaya daya kan daga matsayin huldar kasashensu, zuwa huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare kuma daga dukkan fannoni, al’amarin da ya kafa alkibla ga ci gaban dangantakarsu. Firaminista Li ya ce yana fatan...
    Matashin, wanda yake yin atisaye a makarantar Mount Kelly ta Birtaniya, ya nuna cewa Nijeriya na da ƙwarewa a harkar ninkaya, duk da cewa har yanzu babu ɗan wasan ninkayar Nijeriya da ya taɓa kai wa gasar Olympics. Nijeriya dai ta taɓa lashe lambobin yabo 27 a wasannin Olympics amma ba ta taɓa yin nasara a fannin ninkaya ba. Hukumar wasanni ta kasa ta taya shi murna, tare da hukumar kula da wasannin ruwa ta Najeriya. Darakta Janar, Bukola Olopade, a cikin sanarwarsa a ranar Lahadi, ya ce wannan babbar nasara ce ga wasannin Najeriya baki ɗaya. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku....
      Wannan yana samar da lantarki da rage asarar makamashi da kuma samar da kaso 25 na bukatun makamshi na ginin. Haka kuma zai kai ga rage fitar hayakin Carbon tan 500 a shekara.   Baya ga haka, ginin na amfani da tsoffin baturan motoci masu amfani da lantarki, wajen adana makamashi. Ana amfani da irin wadannan batura guda 14 wajen adana rarar makamashin da ake samu daga bangon gilas mai zukar hasken rana da samar da makamashi mai tsafta a lokaci mafi samun hasken rana, a farashin yuan 0.22 kwatankwacin $0.031, kan kilowatt 1 a kowacce sa’a. Kuma za a yi amfani da makamashin da aka adana a lokacin da ake bukatar lantarki mai yawa ko kuma lokacin da...
    Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya murna ga waɗanda suka yi nasara a zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar a mazabu 16 a jihohi 12 na ƙasar nan. Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa shugaban ƙasa ya yaba wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) bisa gudanar da zaɓen lafiya ba tare da wata matsala ko tashin hankali ba. A cewar sakamakon da INEC ta bayyana, jam’iyyar APC ta lashe kujeru 12, yayin da jam’iyyar APGA ta samu biyu. Jam’iyyar PDP da jam’iyyar NNPP kowanne ya samu kujera ɗaya. Shugaba Tinubu ya taya sabon shugaban jam’iyyar APC na...
    A cikin jahohin da aka lissafa, Kebbi ce ta fi kowacce yawan garuruwa a jerin sunayen, inda take da garuruwa kusan 10 da suka hada da Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, da Birnin Kebbi. Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar gargadin samun ambaliyar ruwa ga jihohi 15 daga cikin 19 na Arewa. Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, wacce ta yi wannan gargadin a madadin gwamnatin tarayya, ta bayyana cewa dole ne a dauki matakan da suka dace a cikin al’ummomin da abin ya shafa. Sanarwar da Ma’aikatar Muhalli ta fitar ta ce, biyo bayan hasashen da ta yi na samun ruwan sama mai karfi a jihohin, za a iya samun ambaliyar ruwa tsakanin 10 ga Agusta zuwa 14...
    Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin. Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da aka yi fasa-ƙwaurin su zuwa Najeriya. Kwanturola Janar na Kwastam, Adewale Adeniyi, ya sanar da cewa an yi ƙarya wajen bayyana kayan da  kwantainonin suke ɗauke da su, inda aka ɓoye makamai, harsasai da magungunan da ba su da rajista. “A yau, muna sanar da kama kwantainoni 16 da shigowarsu ke karya dokokinmu kuma suna barazana ga tsaron ƙasa. Darajar harajin da za a biya...
    Rijistaran makarantar, Alhaji Kasimu Salihu, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa an rufe makaranta kuma an umarci ɗalibai su bar harabar makarantar har sai an bayar da sanarwa ta gaba. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dakarun Operation FANSAN Yamma (OPFY) sun yi nasarar fatattakar ‘yan ta’adda da dama a wani hari da suka kai ta sama da kasa a yankin Makakkari da ke dajin Gando a karamar hukumar Bukkuyum a jihar Zamfara.   Wannan farmakin wanda ya gudana a ranar 10 ga watan Agustan shekarar 2025, ya biyo bayan wasu bayanan sirri da suka samu cewa dimbin ‘yan ta’addan da ke biyayya ga marigayi Halilu Buzu da Alhaji Beti sun taru a cikin dajin inda suka shirya kai harin ramuwar gayya kan al’ummomin Addabka da Nasarawan Burkullu a garin Bukkuyum.   Jami’in yada labarai na rundunar ‘Operation Fansan Yamma OPFY’ Kyaftin David Adewusi, ya ce bayanan sirri sun nuna cewa, harin da suka shirya kai...
    Hukumar Kwastam Najeriya ta kama kwantainoni 16 ɗauke da makamai da miyagun ƙwayoyi da magungunan da wa’adin aikinsu ya ƙare da wasu haramtattun kaya na kimanin Naira 10 a Tashar Jiragen Ruwa ta Apapa da ke Jihar Legas a ranar Litinin. Hukumar ta bayyana cewa ta kama mutane shida dangane da wannan haramtattun kaya da aka yi fasa-ƙwaurin su zuwa Najeriya. Kwanturola Janar na Kwastam, Adewale Adeniyi, ya sanar da cewa an yi ƙarya wajen bayyana kayan da  kwantainonin suke ɗauke da su, inda aka ɓoye makamai, harsasai da magungunan da ba su da rajista. “A yau, muna sanar da kama kwantainoni 16 da shigowarsu ke karya dokokinmu kuma suna barazana ga tsaron ƙasa. Darajar harajin da za a biya...
    Sojoji sun samu nasarar kai wani gagarumin farmaki kan maboyar ’yan ta’addan da suka addabi manoma da mazauna wasu ƙauyuka a Jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Nijeriya. Bayanai sun ce dakarun sojin na sama da ta ƙasa, waɗanda ke ƙarƙashin rundunar Operation Fasan Yamma da ke sintiri a Arewa maso Yamma domin kawar da masu tayar da ƙayar baya, sun hallaka sama da ’yan ta’adda 400 a yayin wannan samamen. Za a gyara tarbiyar tubabbun ’yan daban Kano Direba ɗaya ya tsira a hatsarin tankokin dakon iskar gas a Zariya Majiyoyi sun bayyana cewa ’yan ta’addan, waɗanda ke fakewa a dajin Makakkari tare da shugabanninsu daban-daban, sun dauki haramar kai hari kan wani ƙauye ne kafin sojojin su...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Jami’an Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arziƙi Zagon Ƙasa (EFCC), sun kai samame a Ɗakin Karatun Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, a Jihar Ogun, inda suka kama wasu matasa da ake zargin ’yan damfara ne. Samamen ya faru ne da safiyar ranar Lahadi a sashen otal na ɗakin karatun. ’Yan bindiga sun kashe gomman mutane a ƙauyukan Sakkwato An ɗaure tsohon Firaminista Succes Masra shekaru 20 a Chadi Gidan Obasanjo na musamman yana cikin harabar ɗakin karatun. Wani faifan bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, ya nuna yadda wasu matasa ke gudu domin ka da EFCC ta kama su. Rahotanni sun ce jami’an EFCC sun ƙwace sama da motoci 20 tare da wasu kayayyaki masu daraja. Wani jami’in...
    Ali Akbar Velayati mashawarcin jagoran juyin juya halin Musulunci da Jamhuriyar Musulunci ta Iran kan harkokin kasa da kasa ya tabbatar da cewa “Jamhuriyar Musulunci tana adawa da shirin kwance damara na kungiyar Hizbullah” yana mai jaddada cewa Iran a ko da yaushe tana goyon bayan al’ummar kasar Labanon da kuma gwagwarmayarsu. Da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Tasnim na Iran a ranar Asabar, Velayati ya ce bijiro da batun kwance damarar Hizbullah ba sabon abu ba ne a Lebanon. “Kamar yadda wannan yunƙurin ya gaza a baya, wannan karon ma ba za iyi nasara ba, kuma ‘yan gwagwarmaya zasu ci gaba da yin tsayin daka a kan manufofinsu da kuma dakile wannan makirci,” in ji shi. Ya...
    Al’ummar Japan na gudanar da bikin tunawa da ranar harin Nagasaki da ya faru shekaru 80 da suka gabata, wani hari da ke zama irinsa na farko kuma mafi muni da duniya ta taba gani. Tarihi ya nuna cewa Amurka ce ta fara harba makamin Nukiliya a garin na Nagasaki kwanaki uku bayan na garin Hisroshima a wani ɓangare na dakatar da yaƙin duniya na biyu.! Harin na ranar 9 ga watan!!!!!!!mutane dubu 70 a take bayan mutane 140 da suka mutu kwanaki uku da suka gabata a harin na Hiroshima. An yi ittifakin cewa wannan shine harin da ya tilastawa Japan miƙa wuya a ranar 15 ga watan Agustan wannan shekarar, matakin da ya kawo ƙarshen yaƙin. Bayanai sun...
    Wata babbar kotu a Jihar Borno, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Aisha Kumaliya, ta yanke wa Kalthum Mustapha hukuncin ɗaurin shekara uku a gidan gyaran hali bayan samun ta da laifin aikata damfara. Hukumar EFCC ta bayyana cewa, an fara gurfanar da Kalthum a ranar 13 ga watan Mayu, 2024. Tsohon Ministan Noma Audu Ogbeh ya rasu Fashewar gurneti ya kashe yara uku a Borno  Ana tuhumarta da karɓar kuɗi Naira miliyan 1.35 daga hannun Muhammad Lawan Sani, Abubakar Umar, da Yusuf Jafar domin samar musu da kayan abinci da ake amfani da su wajen ciyar da yara masu fama da rashin abinci mai gina jiki. Sai dai ba ta kawo kayan ba kuma ba ta mayar musu da kuɗinsu ba. A...
    Cin zarafin Amurka ta hanyar haraji ya kuma lalata amincinta tsakanin sassan kasa da kasa. A halin yanzu, fannin shigar da kayayyaki na Amurka ya yi kasa zuwa kashi 13% kacal a kasuwannin duniya.   Har ila yau, a jiya Alhamis 7 ga wata, bayanai sun nuna cewa, a cikin watanni bakwai na farkon shekarar nan, cinikayyar kayayyaki ta Sin ta ci gaba da nuna kyakkyawan ci gaba, inda ta samu karuwa tsakaninta da kasashe membobin kungiyar ASEAN, da Tarayyar Turai, da Afirka, da Asiya ta Tsakiya, wanda ke nuna karfin juriya da kuzari. Hakan ya kuma tabbatar da cewa, cin zarafi ta hanyar haraji ba zai haifar da alfanu na dogon lokaci ba, maimakon haka, budadden tsarin hadin gwiwa...
    Shugaban Amurka ya aike da jakada zuwa Rasha tare da yin barazanar sanyawa Moscow takunkumi Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sanar da cewa: Manzonsa na musamman Steve Witkoff zai ziyarci kasar Rasha a mako mai zuwa, yayin da wa’adin da ya sanyawa Moscow na kawo karshen yakin da take yi da Ukraine ke gabatowa. A halin da ake ciki kuma, ana ci gaba da gwabza yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine, inda Moscow ta sanar da lalata jiragen Ukraine guda 18. Yakin da ake yi a Ukraine na kara kamari zuwa ci gaba mai hatsari a daidai lokacin da wa’adin da shugaban Amurka Donald Trump ya gindaya wa Rasha ke gabatowa, da kuma halayensa na tunzura jama’a,...
    Tawagar ƴan wasan kwando na matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon kwando ta Afirka karo biyar a jere, lamarin da ya sa ta kafar tarihin wannan bajinta a Afirka. Tawagar D’Tigress ta samu nasara ne a wasan ƙarshe bayan doke Mali da ci 78-64 domin ɗaukar kofin gasar karo na bakwai a tarihi. Ƴan wasan Najeriyar sun kankane gasar ƙwallon kwandon Afirka, inda suka yi nasara sau 29 a jere a duka wasan da suka buga ba tare da rashin nasara ba tun 2015. Nasarar D’Tigress na zuwa ne kimanin mako guda bayan da tawagar Super Falcons ta ƴan wasan ƙwallon kafar matan Najeriya ta lashe gasar ƙwallon ƙafar matan Afirka, karo na 10 a tarihi.
    Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta tarayya Kabiru Amadu (wanda aka fi sani da Mai Palace) ya shirya taron addu’a na musamman ga jihar Zamfara da Najeriya baki daya, domin neman zaman lafiya da cigaba mai dorewa.   Taron addu’o’in wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a na Tudun Wada da ke Gusau, ya hada malaman addinin Musulunci, da sarakunan gargajiya, da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, da kuma daruruwan al’ummar jihar baki daya, duk sun ba da hadin kai wajen ganin an samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.   A nasa jawabin, Kabiru Mai Palace, ya bayyana taron a matsayin wani shiri na ruhi da nufin neman taimakon Allah wajen magance matsalar rashin...
    Rundunar Sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar jami’an Hukumar DSS sun ceto Injiniya Joshua Saleh, wani malami a Jami’ar Taraba, wanda ’yan bindiga suka sace. An sace malamin ne a ranar 31 ga watan Yuli, 2025, a hanyar Chinkai–Kente zuwa Wukari, da ke Ƙaramar Hukumar Wukari a Jihar Taraba. Sai an samar da ’yantacciyar ƙasar Falasɗinu za mu ajiye makamai — Hamas An ƙara hakimai 6 a Masarautar Katsina Bayan samun sahihan bayanai, sojoji da DSS suka fara bincike tare da ƙoƙarin ceto shi a wurare da dama, ciki har da Kente, Sondi 1 da 2, Yaku, da Warawa. A cewar Laftanar Umar Muhammed, mai magana da yawun rundunar, sojojin sun yi arangama da ’yan bindigar, inda suka yi musayar...
    Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya ta Najeriya (NANNM), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ta fara a faɗin ƙasar nan. Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata takarda da shugabanta ƙasa, Haruna Mamman, da sakatarenta, T.A. Shettima, suka sanya wa hannu. Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Jami’ar Umaru Yar’adua ta kori ɗalibai 57 kan satar jarabawa Sun fara yajin aikin ya fara ne a ranar Laraba tare da niyyar shafe kwanaki bakwai suna yin sa. Ma’aikatan jinyar sun shiga yajin aikin ne saboda ƙarancin albashi, ƙarancin ma’aikata, da kuma rashin ingantattun wuraren aiki. Wannan yajin aiki na zuwa ne a daidai lokacin da likitoci ke takun saƙa da gwamnati kan batutuwan suka shafi jin...
    Shugaban kasar Iran Masuod Pezeshkiya ya yi juyayin shahadar Isma’ila Haniyya marigayi shugaban kungiyar Hamasa a nan Tehran shekara guda kenen. Ya kuma jaddada cewa JMI ba za ta taba manta da shi ba. Tashar talabijin ta Presstv ta nakalto shugaban yana bayyana wannan juyayin a ranar da  Haniya yake cika shekara guda da shahada, sannan shahadarsa ya zo dai dai da ranar da Pezeshkiyan ya fara shugabancin kasar. Labarin ya kara da cewa shugaba Pezeshkiyan ya bayyana haka ne a shafinsa na X ya kuma kara da cewa a ranar da na fara aiki a matsayin shugaban kasa kenen, makiya HKI da kuma Amurka suka sanyamu cikin bakin ciki tare da kashe bakommu wanda ya zo ya taya mu...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da iska mai karfi da aka tafka a kwanan nan ya yi sanadin mutuwar mutane 44, yayin da wasu tara suka bace a birnin Beijing, kamar yadda aka bayyana a wani taron manema labarai da ya gudana a yau Alhamis. A yayin taron manema labarai da gwamnatin birnin Beijing ta gudanar a yau game da rigakafin ambaliyar ruwa da bayar da agajin gaggawa, an bayyana cewa, bala’in ambaliyar ruwan da ya auku kwanan nan ya shafi mutane sama da 300,000 tare da lalata gidaje 24,000 a birnin Beijing. Sai dai, yanzu haka birnin na Beijing na kara kokarin farfado da wutar lantarki, da share tituna, da kai muhimman kayayyaki ga mazauna yankin da...
    Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta sanar da cewa, a halin yanzu ana iya  bayyana kadarorin ma’aikatan ta hanyar yanar gizo, wani mataki da aka tsara domin saukaka aikin da kuma kara yin lissafi.   Daraktan ofishin na jihar Jigawa Abubakar Bello ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri a ofishin sa.   Abubakar Bello ya jaddada cewa sabon shirin na da nufin rage dinbin aikin dake gaban ma’aiakata da kuma saukaka tantance kadarorin domin yaki da cin hanci da rashawa a cikin tsarin.   “Mun sauya dabara zuwa rajista ta yanar gizo don bayyana kadarorin, muna ba wa mutane damar kammala aikin daga gidajensu. Duk da haka, muna neman goyon...
    Ministan ya kuma ce ƙasarsa na shirin sanya hannu a wata takarda don neman goyon bayan sauran ƙasashe wajen ganin an kafa ƙasar Falasɗinu da Isra’ila. A taron Majalisar Ɗinkin Duniya da aka gudanar na kwana biyu, ƙasashe 125 sun amince cewa hanyar warware rikicin Gaza ita ce kafa ƙasashe biyu, wato Falasɗinu da Isra’ila. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Dakarun Operation Haɗin Kai da ke Arewa maso Gabas, sun ɗakile wani sabon hari da mayaƙan Boko Haram suka kai a Jihar Borno. Sun kai harin ne yankunan Konduga, Bama da Gwoza. Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu Adadin Falasdinawan da Isra’ila take kashewa a Gaza yanzu ya haura 60,000 ’Yan ta’addan sun yi yunƙurin tarwatsa gadar da ke kan hanyar Marte zuwa Dikwa ta hanyar dasa bama-bamai. Amma sojoji sun gano abubuwan fashewa guda 17 da suka dasa a ƙarƙashin gadar kuma suka cire su. A yayin daƙile harin, sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram guda tara, sannan sun ƙwato bindigogi ciki har da AK-47 da bindigar PKT. Kakakin rundunar sojin a Maiduguri, Kyaftin Reuben Kovangiya,...
    Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta taya sabon mai martaba Sarkin Katsinar Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, murnar hawansa karagar mulki a matsayin Sarkin Katsinan Gusau na 16.   Jam’iyyar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaranta, Yusuf Idris Gusau, ta bayyana sabon sarkin a matsayin mai tarihi da kuma nadin sarautar Allah, wanda ya zo ne jim kadan bayan rasuwar mahaifinsa, marigayi sarki, Alhaji Ibrahim Bello.   Sanarwar ta nuna cewa Alhaji Abdulkadir kyawawan halaye na gaskiya, kwazonsa, sadaukarwa, biyayya ga mahaifinsa da ya rasu, da kuma mutunta al’umma ta kowane hali, sun nuna shi ne wanda ya cancanta.   A cewar sanarwar, wannan shi ne karo na farko a tarihin masarautar da wani...
    Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da zagayen farko na makon lafiyar mata da jarirai da jarirai (MNCHW) na shekarar 2025 tare da raba fakiti 6,000 na kayan haihuwa da na’urar (C/S) 500 ga cibiyoyin lafiya a fadin jihar.   Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta shi ne ya jagoranci bikin kaddamar da shirin a hukumance da aka gudanar a cibiyar lafiya matakin farko na Birji da ke karamar hukumar Madobi.   Ya yi nuni da cewa, wannan aikin ya hada da na rigakafi na yau da kullun ga yara, karin sinadarin Vitamin A, Rarraba gidajen sauro masu maganin kwari ga mata masu juna biyu.   Gwamna Yusuf ya jaddada kudirin gwamnatin sa na karfafa...
    Sauran sun haɗa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu, tsoffin gwamnoni, ministoci da hafsoshin tsaro. Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Mahara sun kashe akalla mutane biyar a Dajin Madam da ke yankin Karamar Hukumar Alkaleri ta Jihar Bauchi. Wannan na zuwa ne bayan a makon jiya ’yan bindiga sun kutsa kauyukan da ke kusa da garin Mansur a karamar hukumar, inda suka kashe mutane hudu, suka kwashe kayayyaki a shagunansu. Daga bisani ’yan sanda sun sun bi su, inda suka fatattake su suka gudu zuwa cikin kungurmin Dajin Madam. Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed ne ya sanar da mutuwar mutanen a yayin taron zaman lafiya da aka gudanar a garin Nahutan Darazo a kokarinsa na sasanta rikicin baya-bayan nan tsakanin manoma da makiyaya da ya yi sanadin jikkatar wassu mutane a Darazo. Gwamnan ya kuma nuna matuqar damuwarsa kan...
    An fara shigar da kayyakin agaji zuwa Zirin Gaza wadanda galibi ta sararin samaniya aka rika jefawa da jirage daga kasashen Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa. Arshiyan Kohen, kakakin ma’aikatar tsaron Isra’ila ya ce, za a dakatar da farmakin soji na tsawon sa’o’i 10 a kowace rana a wasu sassan Gaza tare da ba da damar samun sabbin hanyoyin ba da agaji. DW ya ruwaito cewa ana ci gaba danka kayayyakin tallafin a hannun kungiyoyin agaji na kasa da kasa da suke ci gaba da ayyukan rarrabasu. Tinubu ya bai wa ’yan ƙwallon Nijeriya mata kyautar kuɗi da gida da lambar yabo An kashe ’yan ta’adda 45 a Neja Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteress ya siffanta wannan matakin da...
    Ma’aikatar kula da sashen ayyukan jigilar kayayyaki ta kasar Sin ta ba da rahoton cewa, a cikin rabin farkon bana, an samu ci gaba mai yawa a bangaren, kamar yadda alkaluman hukuma suka nuna a jiya Lahadi. Hukumar raya ci gaban kasa da gudanar da gyare-gyare, wacce take da alhakin tsara tsare-tsaren tattalin arzikin kasa ta yi bayanin cewa, kudin da ake kashewa a ayyukan jigilar kaya ya kai kaso 14 cikin dari na GDPn kasar a watanni shida na farkon shekarar, inda ya ragu da kaso 0.1 cikin dari idan aka misalta da na rubu’in farko, kuma ya ragu da kashi 0.2 bisa dari a mizanin shekara-shekara. A cewar hukumar, wannan na nuni ne da sakamakon farko da aka...
    A ƙoƙarinta na daƙile cin zarafin mata da yara, Ma’aikatar Harkokin Mata ta Jihar Gombe, ƙarƙashin jagorancin Kwamishina Asma’u Mohammed Iganus, ta gabatar da kundin dokar hana cin zarafi mata (GBV) ga Mai Martaba Sarkin Gombe, Alhaji Dokta Abubakar Shehu Abubakar III, domin samun goyon bayan sarakunan gargajiya wajen aiwatar da dokar a matakin ƙasa. Taron da aka gudanar a zauren Ƙaramar Hukumar Gombe ya samu halartar manyan jami’ai, sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma. LP za ta ceto Nijeriya daga halin da APC ta jefa ta — Nenadi Usman Rashin abinci mai gina jiki ya kashe yara 650 a Katsina — MSF A wajen taron, Kwamishinar ta jaddada cewa dokar na buƙatar goyon bayan al’umma gaba ɗaya, musamman sarakunan gargajiya,...
    Shuwagabannin kungiyoyin musulmi a kasar Amurka sun fara daukar matakan tsaro a masallatai da wuraren taro da kuma makarantun musulci saboda yawan samun wasu magoya bayan yahudawa suna yawaita shiga irin wadannan wurare suna lalatasu. Shafin yanar gizo na labarai ‘ArabaNews” ya bayyana cewa a jihohin Texas da Califonia, masu goyon bayan yahudawan sun lalata masallatai da dama sun kuma sace abubuwa da dama a cikinsu. Edward Ahmed Mitchell, mataimakin sakataren kungiyar ‘ Council on American-Islamic Relations’ wata kungiyar kare hakkin musulmi a Amurka ya shaidawa Arabnew kan cewa tun bayan fara yaki a Gaza shekaru kimani biyu da suka gabata, musulmi a Amurka suka fara fuskantar sabon kiyayya daga wadanda basa son musulmi a kasar. Edword yace abu mafi...
    A wani lamari makamancin haka da ya faru a Jihar Taraba, a watan Yuli, 2025, da misalin karfe 11:45 na rana, jami’an ‘yansanda sun amsa kiran da aka yi musu na satar mutane a hanyar Wukari, jim kadan a bayan jami’ar tarayya ta Wukari. Wata farar mota kirar Toyota bas dauke da fasinjoji 17 daga Enugu zuwa Yola, wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun yi musu kwanton bauna. Jami’an ‘yansanda tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun yi gaggawar kai farmaki inda lamarin ya faru. Da ganin tawagar jami’an tsaro na zuwa, sai masu garkuwar suka yi bar wadanda abin ya shafa suka gudu cikin daji. An ceto dukkan fasinjoji 17 ba...
    A jiya Juma’a ne dai wanda ya isa birnin Beirut ya yi kira ga al’ummar kasar da su yi riko da hadin kan kasa da dukkanin bangarorinsu, sannan kuma su ci gaba da zage damtse wajen kalubalantar makiyar kasar Lebanon,musamman ‘yan sahayoniya. Goerge Ibrahim Abdullah wanda kuma  ya gabatar da taron manema labaru a garinsu na “Qubyat’ ya kara da cewa; Kamar yadda mu ka kasance garkuwa mai bayar da kariya ga kasa, za mu ci gaba da zama haka’ sannan kuma ya kara da cewa: Saboda jinanen Shahidai kasar Lebanon za ta iya kalubalantar dukkanin hatsurran da take fuskanta.” Har ila yau, ya bayyana cewa;sojojin kasar Lebanon suna da mazajen da za su iya kare kasa,illa iyaka abinda ya...
    Kungiyar da ke sa ido kan kare hakkin bil adama ta Siriya ta tattara bayanan mutuwar mutane 1,400 a loardin Sweida na Siriya Siriya, Faransa da Amurka sun sanar da wata taswirar hadin gwiwa don tabbatar da zaman lafiya a Siriya, bayan tattaunawar da ba a taba ganin irinta ba a birnin Paris na Faransa, wadda ta hada ministan harkokin wajen gwamnatin rikon kwarya na Siriya Asaad al-Sheibani, da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot da manzon Amurka na musamman a Siriya Tom Barrack. Sanarwar ta hadin gwiwa da aka fitar bayan taron na bangarorin uku, ta tabbatar da goyon bayan shirin mika mulki ga gwamnatin kasar Siriya da karfafa hadin kan al’umma, musamman a birnin Sweida da ke arewa maso...
    Kwanan nan jam’iyyar PDP ta gudanar da taron kwamitin zartarwa karo na 100 da aka gudanar ranar 30 ga Yuni, PDP ta warware rikicin da ya dade yana ci mata tuwo a kwarya na batun mukamin sakataren jam’iyyar na kasa wanda ta tabbatar da Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar. Duk da wannan warware batun, Atiku da wasu magoya bayansa sun fice daga jam’iyyar sakamakon rashin warware rikicin gida na jam’iyyar. A ranar 1 ga Yuli, Atiku da Peter Obi da Rotimi Amaechi da Nasir El-Rufai, da wasu sun kulla hadaka a karkashin jam’iyyar ADC, sun ce sun yi wannan hadakar ne domin kalubalantar APC a zaben 2027. A matsayin wani bangare na wannan yunkurin hadin gwiwa, sun nada...
    Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp
    Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya fara tattauna masifar da ta faru a Gaza tare da jaddada kawo karshen kisan kiyashi  yanki Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da wani sabon zama domin tattauna batutuwan da suke faruwa a Gaza da kuma tabarbarewar al’amuran jin kai a yankin, inda ake ci gaba da yin kiraye-kirayen gaggauwa da kuma kira ga kasashen duniya da su dauki kwararan matakai na kawo karshen bala’in da ya biyo bayan yakin kisan kare dangi a yankin. Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira da a hanzarta dakatar da tilastawa al’ummar Gaza gudun hijira kamar yadda ta bukaci gwamnatin mamayar Isra’ila da ta ba da damar kai agajin jin kai ga al’ummar Zirin Gaza. Mataimakin babban...
    Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC) a ranar Laraba ta ce ta gano wani dakin ajiye kayayyaki da aka makare da lita 88,560 na sinadaran hada bama-bamai a Kano. Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana hakan lokacin da take yi wa manema labarai jawabi a kofar rumbun da ke unguwar Kwakwaci a karamar hukumar Fagge da ke jihar. Mojisola, wacce Daraktan Bincike da Tabbatar da Bin Doka na hukumar, Dokta Martins Iluyumade ya wakilta, ta ce dakin na dauke ne da lita 60,000 na sinadarin sulphuric acid, sai kuma lita 28,560 na nitric acid da kuma wasu jarkoki 330 da aka riga aka rabar wa mutanen da ba a san ko su...
    Yar wasan gaba ta Nijeriya, Chinwendu Alozie, ce ta tabbatar da nasara da kwallon da ta jefa kafin tashi daga wasan. Wannan nasara ta ba wa tawagar ta Justin Madugu damar kaiwa wasan ƙarshe na gasar.   Yanzu haka, Super Falcons za su kara da ƙasar da za ta yi nasara tsakanin Moroko, wacce ke masaukin baki, da Ghana, a wasan da za a buga daga baya a yau Talata.   Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe Shiga zaurenmu na WhatsApp