Masu Goyon Bayan Hizbullah Su ce Suna Nan Daram Tare Da Kungiyar
Published: 28th, August 2025 GMT
Shugaban gamayyar masu goyon bayan Gwagwarmaya a kasar Lebanon suna tare da kungiyar sannan wadanda suke nanata cewa sai an takaita makamai a hannun gwamnati sun aiki ne wa HKI da Amurka .
Tashar talabijan ta Al-Manar ta kungiyar ta nakalto shugaban gamayyar Mohammad Ra’ad yana fadar haka ya kuma kara da cewa abinda ya faru a ranar 5 ga watan Augustan mai karewa wani kuskure ne wanda gwamnatin kasar Lebanon bata taba irinsa ba.
Kuma yana dai da kamar abinda ya faru a karbala ne, inda wani sojan yazid ya fadawa yan uwansa kan cewa ku shaida mani wanin nYazid kann cewa ni na fara harban kibiya kan Al-Hussain.
Abinda gwamnatin kasar Lebanon tayi na neman yardar Amurka da HKI, shi ne su suka fara daukar mataki a kan masu gwagwarmayar don mika kasar Lebanon ga makiyanra.
Muhammad Ra’ad ya kara da cewa kungiyoyi masu gwagwarmaya a cikin kasar Lebanon suna alfakhari da cewa zamu kasance kaywa ga tafarkin Muhammad (s) da iyalan gidansa Tsarkaka.
Ra’ad ya kammala da cewa jinanen shahidammu sun shaida kan abinda muke kira a kai.,
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran Ta Yi Gargadin Cewa: Shirin Dawo Da Takunkumi Kanta Zai Shafi Mu’amalarta Da Hukumar IAEA August 28, 2025 Wakilin Kasar Rasha A Vienna Ya Sanar Da Sake Dawo Da Ayyukan Hukumar IAEA A Cibiyar Busharhr Na Iran August 28, 2025 Kwamitin Sulhu Ya Kadu Da Ganin Yadda Kananan Yara Ke Mutuwa Saboda Yunwa A Gaza August 28, 2025 Rahoton Isra’ila Ya Bayyana Yadda Dakarun Yemen Suka Kasance Gagara Ba Dau Ga Gwamnatin Isra’ila August 28, 2025 Dakarun Kai Daukin Gaggawa Na Sudan Sun Kashe Fararen Hula 24 Tare Da Raunata Wasu 55 A El-Fasher August 28, 2025 Kwamitn Tsaron MDD ya amince da bullar yunwa a zirin Gaza August 28, 2025 Wata babbar tawagar jami’an tsaron Sudan ta ziyarci Somaliya August 28, 2025 E3 na shirin gabatar da bukatar dawo da takunkuman MDD a kan Iran August 28, 2025 Shugaban Rwanda ya musunta zargin sojojin kasarsa da hannu a rikicin Congo August 28, 2025 ASUU: Gwamnatin Najeriya ba ta aiwatar da ko daya daga cikin bukatunmu ba August 28, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kasar Lebanon
এছাড়াও পড়ুন:
Manoma a Jigawa Sun Jinjinwa Kungiyar Sasakawa Africa Bisa Bada Tallafi a Harkar Noma
Daga Usman Muhammad Zaria
Kananan manoma a jihar Jigawa sun yabawa kungiyar Sasakawa Africa dangane da tallafin da take samarwa a fannin inganta noma.
Yayin tattaunawa da wasu daga cikin wadanda suka ci moriyar shirin musamman manoman shinkafa a garin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, sun bayyana cewa tallafin Sasakawa ya habaka noman shinkafar su tare da samun karin kudade.
Manoman sun bayyana cewar shirin ya taimaka masu wajen bunkasa harkokin noma tare da tallafawa al’ummomin su.
Daya daga cikin wadanda suka amfana da shirin a yankin Chandam dake karamar hukumar Birnin Kudu, Buhari Nafi’u, yace Sassakawa Africa ta samar masu da tallafin noma daban daban.
A cewar sa tallafin sun hada da horo wanda ya taimakawa kananan manoma wajen ganin sun kara samun kudade tare da inganta rayuwar maza da mata a yankin.
Yace a wannan shekarar sun noma amfanin gona mai yawa sakamakon horon da suka samu karkashin shirin, inda suka hadu sukayi noman a kungiyance a yankin Birnin Kudu.
Buhari ya kara da cewar, a shekarun baya suna daukan kwanaki casa’in kafin su girbe shinkafa amma zuwan Sassakawa ya sa sun yi noma tare da girbe amfanin gonan su a cikin kwanaki saba’in saboda irin da kungiyar ta basu.
Yace yanzu haka sun fara amfani da shinkafar da suka noma a gidajen su.
Yace an basu takin zamani kyauta tare da sauran kayayyakin feshi.
Ya godewa tallafin na Sassakawa, yana mai cewar zai cigaba da amfani da irin da aka basu tare da koyar da mazauna yankin abubuwan da aka horar da su akai.
Shi ma Malam Rufai Nasiru daga yankin na Chandam yace sun kara samun ilimi akan sabbin dubarun noma wanda suka samu daga kungiyar ta Sassakawa.
Yace a bana ya noma buhun shinkafa 8 ba kamar a baya ba da yake noma buhu biyar, yana mai cewa shirin yana da inganci kuma zai cigaba da amfani da irin da kungiyar ta basu.
A garin Chuwasu dake karamar hukumar Taura, Aminu Babanyara ya bayyana cewar sun ci moriyar shirin ta hanyar samun iri masu inganci da takin zamani da kuma horo akan sabbin dubarun noma.
Yace wasu daga cikin abubuwan da suka koya sun hada da amfani da shara wajen yin taki a gida inda suka ce hakan yasa sun samu karin shinkafa da geron da suke nomawa idan aka kwatanta da shekarun baya.
Babanyara, yace sabbin dubarun da suka koya da kuma irin da Sassakawa suka basu, ya basu damar ninka abin da suka saba nomawa a damina sau uku.
Yace da farko suna da shakku akan amfani da sabbin irin da sabbin dubarun noman, amma kuma bayan sun gwada a shekaru biyu na farko sun ga alfanun hakan wajen bunkasa amfanin gonan da suke nomawa.
Manoman sun kuma yi kira ga kunyiyar ta Sassakawa ta samar masu da injinan casa domin saukaka masu al’amura.
Malama Amina Abdulrahman wacce tayi jawabi a madadin kungiyar mata manoma a Karamar Hukumar Taura, tace shirin tallafin Sassakawa ya kawo sauyi a rayuwar su musamman a fannin samun kasuwanci da amfanin gonar da ake sarrafawa don yin abinci mai gina jiki na yara.
A cewar ta an horar da su akan yadda za su samar da abinci mai gina jiki a yankuna tare da yadda za su yi aiki a kungiyance don inganta noma.
A don haka, tayi kira ga kungiyar Sassakawa ta samar masu da injinan sarrafa amfanin gona na zamani.
Yankunan da aka ziyarta sun hada da Chandan dake Birnin Kudu da kuma Sabon Gari shi ma a karamar hukumar Birnin Kudu.
Sauran sun hada da Baranda dake Dutse da kuma Chuwasu dake karamar hukumar Taura.