Tinubu Ya Taya Wadanda Suka Yi Nasara A Zaben Cike Gurbi Murna
Published: 18th, August 2025 GMT
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taya murna ga waɗanda suka yi nasara a zaɓukan cike gurbi da aka gudanar a ranar Asabar a mazabu 16 a jihohi 12 na ƙasar nan.
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa shugaban ƙasa ya yaba wa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) bisa gudanar da zaɓen lafiya ba tare da wata matsala ko tashin hankali ba.
A cewar sakamakon da INEC ta bayyana, jam’iyyar APC ta lashe kujeru 12, yayin da jam’iyyar APGA ta samu biyu. Jam’iyyar PDP da jam’iyyar NNPP kowanne ya samu kujera ɗaya.
Shugaba Tinubu ya taya sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda murna, yana bayyana nasarorin a matsayin babban ci gaba na farko a ƙarƙashin jagorancinsa.
Haka kuma ya yaba wa gwamnoni da shugabannin jam’iyyar APC bisa rawar da suka taka wajen samun wannan nasara.
Da yake nakalto shugaban ƙasa, Onanuga ya ce: “Shugaba Nentawe Yilwatda ya nuna ƙarfin jagoranci, ya kuma tabbatar da abin da za a iya cimmawa idan aka tsayar da ‘yan takara da jama’a suka yarda da su tare da haɗin kai tsakanin shugabannin jam’iyya.”
Shugaba Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki don cika manufofin Renewed Hope Agenda.
Shugaban ƙasa ya kuma yaba wa dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da suka shiga zaɓen, yana roƙon su da su ci gaba da rungumar akidar siyasa bisa gaskiya ba da gaba ba domin dorewar dimokuraɗiyya.
Daga Bello Wakilo
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
এছাড়াও পড়ুন:
An Kara Zaburar Da ‘Yan Arewa Game Da Muhimmancin Mallakar Katin Zabe
An bayyana katin zabe a matsayin sheda da za a iya amfani da shi a muhimman wurare, kamar yadda ake amfani da fasfo da katin dan kasa a manyan kasashen duniya.
Tsohon wakilin mazabar tarayya ta Birnin Kudu da Buji, Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yi wannan tsokaci new a wata tattaunawa da manema labarai a Dutse.
Ya bayyana bukatar aiki tukuru a tsakanin masu ruwa da tsaki dan tabbatar da cewar dukkan wadanda su ka cancanta sun karbi katin zaben.
Engineer Magaji Da’u Aliyu ya yabawa gwamnatin Malam Umar Namadi bisa kafa kwamati na musamman a karkashin mai bada shawara kan harkokin siyasa, Alhaji Lawan Garba Bullet, domin zaburar da kananan hukumomi su bada gudummawar da za ta taimaka wajen samun nasarar shirin.
Ya lura cewar akwai abin damuwa bisa karancin fitowa wajen karbar katin zabe a Arewa, idan an kwatanta da alkaluman karbar katin zaben a ikko da sauran jihohin kudu maso kudu da kudu maso gabashin kasar nan duk da cewar Arewa ta fi yawan jama’a.
Magaji Da’u Aliyu ya ce yana da cikakken bayani kan gudummawar da shugabannin kananan hukumomin Birnin Kudu da Buji su ke bayarwa ga aikin bada Katin Zabe amma duk da haka akwai bukatar rubanya kokari domin cimma gagarumar nasara.
Daga nan sai ya yi kira ga matasan da su ka cika shekarun yin zabe da wadanda su ka canja wurin zama da wadanda katin zaben su ya lalace ko ya bata, da su je domin sake karbar wani katin zaben.
A cewar sa, yin haka shine zai basu damar zaben dan takarar da ya kwanta musu a rai ko kuma fidda baragurbin ‘yan siyasa daga madafun iko.
Usman Mohammed Zaria