Kwana 70 da ƙaddamar da taraktoci 2,000 na gwamnati har yanzu manoma ba su ga komai ba
Published: 1st, September 2025 GMT
Yanzu an fi wata biyu da Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da taraktoci 2,000 da sauran kayan aikin gona domin haɓaka harkar noma, amma manoma sun ce har yanzu ba a raba musu su ba, abin da ke iya jawo asarar daminar bana.
Ganin cewa a halin daminar tana gab da ƙarewa, manoma suna ganin lokaci ya riga ya ƙure.
Da yake ƙorafi kan lamarin, Shugaban Ƙungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), Injiniya Kabiru Ibrahim ya ce, “Ina rokon gwamnati ta hanzarta. Wannan shekarar ce ta gwaji wajen tabbatar da tsaron abinci.”
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Ƙungiyar Gwamnonin jihohin Arewa maso Gabas (NEGF) ta buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara tallafin kayayyakin noman damina da na rani.
NAJERIYA A YAU: Me Sakamakon Zaben Ribas Ke Nunawa Game Da Sulhun Wike Da Fubara? Rushe Kasuwar Alaba Rago: ‘A biya ’yan Arewa diyya’Taron ƙungiyar da ya gudana a Jalingo, Jihar Taraba a ƙarshen makon jiya, ya bayyana cewa tsadar kayayyakin noma da matsalar jinƙai na ƙara tsananta barazanar ƙarancin abinci.
Gwamnonin sun buƙaci Gwamnatin Tarayya ta ƙara tallafin noman rani tare da tabbatar da kayan aikin sun isa ga manoma ba tare da jinkiri ba.
Yadda aka ƙaddamar da kayan aikin nomanA ranar 24 ga watan Yuni, 2025, Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da shirin injinan noma a ƙarƙashin Shirin Fata Sabon Gobe, inda aka kawo taraktoci 2,000 daga ƙasar Belarus tare da kayan gyara, injinan girbi da sauransu.
Gwamnati ta ce za a yi amfani da taraktocin wajen noma hekta 550,000 da samar da ayyukan yi 16,000 da kuma taimaka wa iyalan manoma fiye da dubu 550.
Sai dai bincikenmu ya gano cewa har yanzu taraktocin suna an a ajiye a Cibiyar Hukumar Inganta Irin Noma ta Kasa (NASC) da ke Abuja.
Manoma na ƙorafi
Shugaban Kungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN), Injiniya Kabiru Ibrahim, ya ce: “Abin mamaki ne har yanzu ba a raba taraktocin ba. Muna riƙon gwamnati ta hanzarta raba su ta hanyar da ta dace domin kada daminar bana ta wuce.”
Haka ma Dakta Ogbo Douglas, shugaban Kungiyar Manoma Maso Rajin Ci-gaban (AFPA), ya bayyana jinkirin a matsayin “abin takaici.”
Izinin Fadar Shugaban Ƙasa muke jira — MinistaWasu manyan jami’an Ma’aikatar Aikin Gona ta Tarayya sun shaida wa Wakilinmu cewa an gama tsara yadda za a raba taraktocin jiha-jiha, amma ana jiran sahalewar Fadar Shugaban Ƙasa.
Ministan Aikin Gona, Sanata Abubakar Kyari, ya ce, “Za mu tabbatar da cewa taraktocin za su yi aiki sosai ba wai a ajiye kawai ba. Da zarar mun samu izini, za mu fitar da tsarin farashin da zai zama mai sauƙi ga manoma,” in ji shi.
A baya ma an sha yi wa manoma irin wannan alƙawarin amma ba tare da an cika ba.
A 2018, an yi alƙawarin kawo taraktoci 10,000 daga kamfanin John Deere, sannan a 2021 aka ce za a kawo taraktoci 60,000, amma ba a aiwatar ba.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Noman rani taraktoci
এছাড়াও পড়ুন:
Gidauniyar IRM Da KADCHMA, Ta Ƙaddamar Da Inshorar Lafiya Kyauta Ga Mutane 200 A Kaduna
Da yake kaddamar da shirin, Darakta Janar na IRM, Alhaji Anas Muhammad, ya ce an kirkiro da shirin ne domin karfafa zaman lafiya da hadin kai ta hanyar tallafa wa Musulmai da Kiristoci ta bangaren samar da kiwon lafiya da bayar da tallafin kayan abinci da jari.
Ya ce: “Kalubalen lafiya ba sa bambance addini ko kabila, don haka bama bambantawa wajen bayar da tallafin. in sha Allah zamu ci gaba da aiwatar da irin wannan shiri a fadin jihar Kaduna baki daya.”
A nasa jawabin, Shugaban hukumar KADCHMA, Malam Abubakar Hassan, ya bayyana cewa wannan hadin gwiwa tana nuna muhimmancin dangantaka tsakanin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu wajen cimma dorewar tsarin inshorar lafiya ga kowa.
Ya kara da cewa kaddamar da inshorar lafiya kyauta na shekara guda babban ci gaba ne a cikin gyaran fannin lafiya da ake gudanarwa a jihar, inda ya yaba da kokarin gidauniyar IRM wajen tallafawa rayuwar al’ummar Kaduna – Musulmai da Kiristoci.
Wasu daga cikin wadanda suka amfana da shirin daga Kungiyar Kiristoci ta Nijeriya (CAN) reshen Kaduna da kuma kungiyar ci gaba ta Darikar Tijjaniyya ta jihar Kaduna sun bayyana farin ciki da godiya ga gidauniyar da kuma gwamnatin jihar, inda suka ce inshorar lafiya kyauta za ta rage musu nauyin kashe kudin magani tare da karfafa hadin kai a tsakanin al’umma da samar da zaman lafiya.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA