HausaTv:
2025-11-10@07:18:33 GMT

Iraki: Kashi 82.42% na Masu Kada Kuri’a ne Suka Fito Zaben ‘Yan Majalisa

Published: 10th, November 2025 GMT

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Iraki ta sanar a ranar Lahadi cewa adadin masu kaɗa ƙuri’a a zaɓen da aka gudanar ya kai kashi 82.42%, wanda ya tabbatar da sahihanci da kyakkyawan tsarin gudanar zaɓen, a cewar hukumar.

Shugaban Hukumar  Omar Ahmed, ya bayyana a yayin wani taron manema labarai cewa hukumar ta nuna daidaito da adalaci ga dukkan ‘yan Takara.

Ahmed ya bayyana cewa hukumar ta sa ido kan tsarin zaɓe a duk faɗin jihohin ƙasar ta hanyar ƙungiyoyin da ke aiki, yana mai jaddada cewa sakamakon ya nuna jajircewar masu kaɗa ƙuri’a da kuma tafiyar da harkokin zaɓe cikin sauƙi da kuma sahihin tsari.

A cikin wannan yanayi, mai ba da shawara kan harkokin shari’a na hukumar Hassan Salman, ya tabbatar da cewa tsarin zaɓen ya yi armashi kuma an gudanar da shi ba tare da wani cikas ko keta doka ba, yana mai nuna cewa fitowar jama’a a zaben ya zama abin buga misali, domin kuwa ba a taɓa yin irinsa ba.

Salman ya ƙara da cewa na’urori  suna aiki da inganci sosai a duk lokacin zaɓen, kuma ba a sami wata matsala ta fasaha ko katsewar layukan yanar gizo  ba, yana mai jaddada cewa hukumar ta ci gaba da ayyukanta don tabbatar da gaskiya da sahihancin tsarin zaɓen.

An fara gudanar da zaɓen ‘yan majalisar dokoki na musamman na shekarar 2025 a safiyar jiya Lahadi, a tsakiyar tsauraran matakan tsaro da kuma tsarin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (IHEC) ta tsara domin tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Maduro ya kirayi taron CELAC da ya yi tir da ayyukan tsokana na Amurka a yankin Caribbean November 10, 2025 Lebanon: Mutane 28 ne suka yi shahada a hare-haren Isra’ila tun daga watan da ya gabata November 10, 2025 Gwamnan Darfur: Babu zaman lafiya da masu yi wa al’ummar Sudan kisan gilla November 10, 2025 Araghchi : Iran na yunkurin warware rikicin Pakistan da Afghanistan November 9, 2025 Kasashen (AES) za su hanzarta kafa rundunar hadin gwiwa ta tsaro November 9, 2025 Najeriya: An yi zanga-zangar tir da barazanar Trump November 9, 2025 Sudan : MDD ta yi Allah wadai da ta’addancin El-Fasher November 9, 2025 Lebanon: Akalla mutane uku sun mutu a hare-haren Isra’ila November 9, 2025  An Kafa  Mutum-mutumin  Tarihi Na Sarkin Daular Roma Da Ya Durkusa A Gaban Sarkin Iran November 9, 2025  Kamfanonin Jiragen Sama Da Dama Na Amurka Sun Dakatar Da Jigilar Matafiya Saboda Rufe Ayyukan Gwamnati November 9, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

উৎস: HausaTv

কীওয়ার্ড: tabbatar da

এছাড়াও পড়ুন:

Iran Ta Yi Kira Da A Kafa Kwamitin Kasa Da Kasa Don Binciko Falasdiawan Da Suka Bace A Gaza

Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta yi kira da a kafa kwamitin kasa da kasa domin tantance makomar wadanda suka bata a Gaza

Shugaban Kwamitin Binciken Mutane da Suka Bace a tawagar Babban Hafsan Rundunar Sojin Iran, Birgediya Janar Seyyed Mohammad Baqirzadeh, ya gabatar da shawarar kafa kwamitin kasa da kasa don neman fiye shahidai 10,000 da suka bace a yankin Gaza.

Birgediya Janar Baqirzadeh ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro na bangarori uku wanda ya hada da Iran, Iraki, da Kwamitin Kungiyar Red Cross ta Duniya (ICRC), da nufin tantance makomar shahidai da suka bace da kuma mayar da gawarwakinsu ga iyalansu. Ya jaddada muhimmancin rawar da Kungiyar Red Cross take takawa wajen bin wannan batu na jin kai.

Birgediya Janar Baqirzadeh ya kuma ba da shawarar a bi diddigin mayar da gawar shugaban kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas da ya yi shahada Yahya Sinwar ga iyalansa a Gaza, domin dawo da martabar shahidai.

Zirin Gaza ya sha fama da kisan gilla da ake a cikinsa tsawon shekaru, wanda ya haifar da dubban shahidai da mutanen da suka bace, ciki har da fararen hula marasa laifi, mata, da yara, wanda ya bar makomar mutane masu yawa ba a sani ba.

Share

0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Babban Matsalar Jin Kai A Falasdinu, Inda Falasdinawa Miliyan 1.5 Suke Cikin Halin Bala’i November 7, 2025 Kwamitin Tsaro Ya Dage Takunkumi Kan Manyan Jami’an Gwamnatin Kasar Siriya November 7, 2025 Karuwar Matsalar Jin Kai Mafi Girma A Duniya A Sudan Saboda Ci Gaba Da Masifar Yaki A Kasar November 7, 2025 An Rantsar Da Paul Biya A Matsayin Shugaban Kamaru Karo Na Takwas November 7, 2025 Dakarun Sojin Kasar Sudan Sun yi Watsi Da Batun Dakatar Da Bude Wuta Da Amurka Ta Gabatar November 7, 2025 Zanga zanga Ta Barke A Birmingham Ta Nuna Kin Jinin Isra’ila . November 7, 2025 Pezeshkiyan: Masu Kawo Rarraba Tsakanin Musulmi Suna yi wa Yan Sahayuniya Aiki Ne November 7, 2025 Shugaban Najeriya Bola Tinubu Ya yi Alwashin Kawo Karshen Ta’addanci A Kasar November 7, 2025 Araqchi Ya Ce: Harin Amurka Kan Kasar Venezuela Ya Bayyana Karara Duniya Tana Gani November 6, 2025 Qalibaf: Iran Da Pakistan Zasu Aiwatar Dukkan Yarjejeniyar Da Suka Cimma A Tsakaninsu November 6, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci About Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS News Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Explore Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS Ka’idojin Amfani Hakkin Mallaka Ku Tuntube Mu Jaridu Sitemap RSS

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnan Darfur: Babu zaman lafiya da masu yi wa al’ummar Sudan kisan gilla
  • ’Yan bindiga sun kashe kansila yayin Zaɓen Gwamnan Anambra
  • Iraki Na Samu Zaman Lafiya Kuma Tana Kokarin Kawo Karshen Zaman Sojojin Ketare A Kasar
  • Hamas Ta Goyi Bayan Matakin shari’ar Turkiyya Kan Neman kama Masu Take Hakkin Bil’Adama A Isra’ila
  • Tarayyar Afirka Ta Yi Kiran Da A Girmama ‘Yancin Kai Na Najeriya Da Rashin Tsoma Baki A Harkokin Gidanta
  • Limamin Juma’ar Tehran: Tsayin Dakan ‘Yan Gwagwarmaya Daga Koyi Ne Da Alkur’ani Mai Girma
  • Zaben Kananan Hukumomi A Neja Ya Bar Baya Da Kura
  • Iran Ta Yi Kira Da A Kafa Kwamitin Kasa Da Kasa Don Binciko Falasdiawan Da Suka Bace A Gaza
  • Kwamitin Tsaro Ya Dage Takunkumi Kan Manyan Jami’an Gwamnatin Kasar Siriya