Wani Dan Siyasa Ya Shirya Addu’o’i Na Musamman Domin Samun Zaman Lafiya A Zamfara
Published: 4th, August 2025 GMT
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gusau/Tsafe ta tarayya Kabiru Amadu (wanda aka fi sani da Mai Palace) ya shirya taron addu’a na musamman ga jihar Zamfara da Najeriya baki daya, domin neman zaman lafiya da cigaba mai dorewa.
Taron addu’o’in wanda ya gudana a babban masallacin Juma’a na Tudun Wada da ke Gusau, ya hada malaman addinin Musulunci, da sarakunan gargajiya, da masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, da kuma daruruwan al’ummar jihar baki daya, duk sun ba da hadin kai wajen ganin an samar da zaman lafiya mai dorewa a jihar.
A nasa jawabin, Kabiru Mai Palace, ya bayyana taron a matsayin wani shiri na ruhi da nufin neman taimakon Allah wajen magance matsalar rashin tsaro da zamantakewar al’umma da ke addabar Zamfara da sauran sassan kasar nan.
Ya kara da cewa, idan aka ajiye siyasa a gefe, kowane dan majalisa daga jihar Zamfara yana yin kokari na gaske don ganin an magance rikicin.
Manyan Malaman addinin Musulunci daga sassa daban-daban na jihar ne suka jagoranci addu’o’i na musamman, da karatuttukan Alkur’ani mai girma, tare da gabatar da addu’o’in neman zaman lafiya, hadin kai, da ci gaban Zamfara da Najeriya baki daya.
Sun kuma yi addu’ar Allah ya baiwa shugabanni a dukkan matakai da hikima da jagoranci.
Babban Limamin Masallacin Juma’a na Tudun Wada, wanda ya jagoranci zaman addu’ar, ya bayyana muhimmancin Ikhlasi, Adalci, da kokarin hadin gwiwa wajen ganin an samu dawwamammen zaman lafiya.
Sauran sun bukaci al’umma da su rungumi afuwa, hakuri, da hadin kai, tare da jaddada cewa zaman lafiya da tsaro yana farawa ne daga jama’a da kansu.
Mahalarta taron sun nuna jin dadinsu ga Alhaji Kabiru Amadu bisa kaddamar da taron addu’ar, inda suka bayyana shi a matsayin wanda ya dace kuma a yaba masa.
Shima da yake jawabi a wajen taron, mai martaba Sarkin Anka, Alhaji Attahiru Ahmad ya yi kira ga sauran ‘yan majalisar tarayya da su yi koyi da irin wannan kokari da Mai Palace ya yi, yana mai cewa sa hannun Allah shi ne ginshikin magance matsalar tsaro a jihar.
An kammala taron addu’o’in ne da yin kira ga al’umma baki daya da su bayar da gudunmawarsu wajen ganin an dawo da zaman lafiya da zaman lafiya da adalci a jihar Zamfara da Najeriya baki daya.
AMINU DALHATU
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: zaman lafiya da
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Sakkwato Za Ta Kashe fiye da Naira Miliyan 200 Wajen Gyara Tashar Talabijin Ta Kasa NTA
Majalisar zartaswar jihar Sokoto a karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta amince da kashe kudade wajen ayyuka a sassa daban daban nufin tabbatar da amana da aka dora wa gwamnati.
Da yake karin haske ga manema labarai yayin taron da ya saba gudanarwa, kwamishinan yada labarai Alh. Sambo Bello Danchadi ya ce majalisar ta amince da bayar da kwangilar gina dakin kwanan dalibai mai hawa daya a jami’ar Usmanu Danfodiyo da ke Sakkwato, da za a kasha naira miliyan dari hudu da tamanin da bakwai.
Alhaji Sambo Bello Danchadi ya ce majalisar ta kuma amince da gyaran sashen da aka kona na gidan talabijin ta Najeriya NTA Sokoto wanda kudinsa ya kai naira miliyan dari biyu da casa’in.
Danchadi, wanda ke tare da Kwamishinan Muhalli, Hon. Nura Dalhatu Tangaza, da kwamishinan ilimi mai zurfi, Farfesa Hamza Isa Maishanu, ya ce majalisar ta amince da naira miliyan dari tara da tamanin da biyar domin gyara titin Forces Avenue a wani yunkuri na sake fasalin hanyoyin jihar a jihar.
An kuma amince da naira miliyan dari biyu da ashirin da takwas don maye gurbin bututun ruwa dake karkashin kasa a kan hanyar Sultan Atiku-Aliyu Jedo don magance matsalar magudanar ruwa da ambaliyar ruwa.
Kwamishinan ya ci gaba da cewa, an ware naira miliyan dari da ashirin da biyu domin saye da rarraba itatuwa a fadin jihar da nufin yaki da kwararowar hamada da sauyin yanayi.
A bangaren addini kuma an amince da wasu naira miliyan dari da ashirin da biyu domin gyaran masallacin Juma’a na Minannata haka kuma an tsara kammala aikin nan da watanni shida tare da sauran amincewa.
NASIR MALALI