A cikin jahohin da aka lissafa, Kebbi ce ta fi kowacce yawan garuruwa a jerin sunayen, inda take da garuruwa kusan 10 da suka hada da Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, da Birnin Kebbi.

Gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwar gargadin samun ambaliyar ruwa ga jihohi 15 daga cikin 19 na Arewa.

Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, wacce ta yi wannan gargadin a madadin gwamnatin tarayya, ta bayyana cewa dole ne a dauki matakan da suka dace a cikin al’ummomin da abin ya shafa.

Sanarwar da Ma’aikatar Muhalli ta fitar ta ce, biyo bayan hasashen da ta yi na samun ruwan sama mai karfi a jihohin, za a iya samun ambaliyar ruwa tsakanin 10 ga Agusta zuwa 14 ga Agustan 2025.

Ma’aikatar ta yi wannan gargadin ne ta cibiyar gargadin ambaliya ta kasa (FEW), a wata takardar da Daraktanta na Sashen Kula da Ruwa, Malam Usman Abdullahi Bokani, ya sanyawa hannu jiya a Abuja, ta kuma yi hasashen cewa jihohin da ke fama da matsalar sun hada da Adamawa, Bauchi, Nasarawa, da Kaduna, Katsina da Kebbi.

Sauran jihohin Arewa da aka ja kunnen sun hada da Kano, Neja, Taraba, Jigawa, Yobe, Zamfara, Sokoto, Borno, da Kwara.

Sanarwar ta zayyana wasu fitattun garuruwa da al’ummomin da ka iya fuskantar mummunar ambaliyar ruwa da suka hada da Jimeta, Mubi, Keffi, Kafanchan, Birnin Kebbi, Minna, Gusau da Sakkwato.

A cikin jahohin da aka lissafa, Kebbi ce ta fi kowacce yawan garuruwa a jerin sunayen.

Fitattun garuruwa 10 ne aka ambata a jerin sunayen, wadanda suka hada da Kamba, Kangiwa, Kalgo, Ribah, Sakaba, Saminaka, Gwandu, Jega, da Birnin Kebbi.

Bokani ya bukaci mazauna yankin da hukumomin jihar da su dauki matakan kare rayuka da dukiyoyi cikin gaggawa. Ma’aikatar ta kuma bukaci masu ruwa da tsaki da a gaggauta mayar da mataki domin kai dauki cikin gaggawa kan aukuwar ambaliyar ruwa.

Idan dai ba a manta ba a watan da ya gabata ma’aikatar ta fitar da sanarwar gargadin afkuwar ambaliyar ruwa zuwa jihohi 11 tare da yin kira da a dauki matakan kariya daga ma’aikatun muhalli da masu ruwa da tsaki.

A halin yanzu dai manoma a fadin kasar na ci gaba da fafutukar ceto amfanin gonakinsu daga mummunar ambaliyar ruwa yayin da suke kara fargabar yiwuwar rashin amfanin gonakin sakamakon ambaliyar da ke shafar gonaki.

Buge da kari, gwamnatin tarayya ta sake jaddada cewa aikin sake ginawa da inganta madatsar ruwa ta Alau a Jihar Borno yana nan kan yadda aka tsara kuma ana sa ran zai samar da mafita ta dogon lokaci kan matsalar ambaliyar ruwa, samar da ruwan sha, da kuma bukatun noma a yankin Arewa maso Gabas.

Ministan albarkatun ruwa da tsaftar mahalli Farfesa Joseph Utseb ne ya bada wannan tabbacin yayin ziyarar aiki da ya kai yankin dam a Maiduguri, inda ya jagoranci tawagar manyan ma’aikatar domin duba aikin.

A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar, Farfesa Utseb ya bayyana cewa, kashi na farko na aikin, wanda ya mayar da hankali ne kan magance ambaliyar ruwa, an fara shi a watan Maris na shekarar 2025, kuma ana hasashen kammala shi a watan Satumba na shekarar 2025. Kashi na biyu, wanda ke da nufin inganta madatsar ruwa gaba daya, an shirya gudanar da shi daga watan Oktoba 2025 zuwa Maris 2027.

Ministan ya ba da labarin abin da ya faru a watan Satumbar 2024 a lokacin da madatsar ruwa ta Alau da ta haddasa mummunar ambaliya, da hasarar rayuka, da kuma lalata dukiyoyi da gonaki na biliyoyin Naira. Ya kuma jaddada cewa an tsara ayyukan sake ginawa ne domin hana afkuwar irin wannan bala’i.

A wani bangare na ziyarar, ministan ya kuma duba gadar Ngada da ke da alaka da ruwa, daga bisani kuma ya ziyarci Gwamna Zulum a gidan gwamnati dake Maiduguri.

 

Neja

A Jihar Neja, gonaki, musamman gonakin shinkafa, a cikin al’ummomi sama da 30, ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da su.

Wani manomi a Karamar Hukumar Dere Lapai da ambaliyar ruwa ta shafa Gambo Mohammed ya ce lamarin ya sa akasarin su rayuwarsu ta tsaya cik.

Ya ce ambaliyar ruwa ta mamaye al’umma tare da lalata filayen noma da dama.

Shi ma da yake magana, wani babban manomi a Karamar Hukumar Mokwa, Isah Aliyu ya ce lamarin ya kamar wani zama taron shekara-shekara saboda haka sun koma gefe kafin lokacin noman rani.

Manoman Jihar ebonyi sun koka kan yiwuwar afkawa cikin talauci

 

Manoman Jihar Ebonyi Sun Koka Kan Yiwuwar Talauci

Duk da yawan ruwan sama da ake samu a jihar Ebonyi, har yanzu jihar ba ta samu wani babban bala’in ambaliyar ruwa ba, sakamakon fadakarwar da hukumomin gwamnati da abin ya shafa suka yi. Shuwagabannin kananan hukumomi da shugabannin al’umma da gwamnatin jihar sun fara gangamin wayar da kan jama’a, inda suka gargadi mazauna yankin da ke fama da ambaliyar ruwa da su kaura.

 

Kuros Riba

Gonaki masu dauke da amfanin gona da suka kai miliyoyin Nairori ba su tsira ba musamman a yankunan koguna na Karamar Hukumar Odukpani ta Jihar Kuros Riba.

 

KOGI

Tuni dai manoma a wasu al’ummomi a Jihar Kogi suka fara kuka. “Har yanzu amfanin gonakinmu bai isa girbi ba, duk da haka ruwan yana nan,” in ji Jimoh Amadu.

Sai dai gwamnatin jihar ta ce ana daukar matakan dakile bala’in ambaliya da ke tafe, biyo bayan karuwar ruwan da aka yi a kogin Neja da Binuwe.

Hasashen NIMET ya nuna cewa Jihar Kogi na daga cikin jihohin Arewa da ke fama da ambaliyar ruwa.

A makon da ya gabata ne dai Karamar Hukumar Idah a Kogi ta Gabas ta yanke gaba daya daga Lokoja, babban birnin jihar sakamakon ambaliyar ruwa da ya yi sanadin rugujewar wata gadar da ke hade da juna.

 

Filato

Ruwan sama ya lalata wasu gonaki a Jihar Filato, sai dai jihar ta yi kira da a yi taka tsantsan a tsakanin manoma da yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa.

A cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar, Misis Joy Ramnap, ya sanyawa hannu, jihar ta yi kira ga al’ummar da ke fama da ambaliyar ruwa musamman Karamar Hukumar Mangu da su kasance cikin shirin ko ta kwana tare da daukar matakan tabbatar da tsaron lafiyarsu da dukiyoyinsu.

 

BORNO

Biyo bayan rugujewar gine-gine guda takwas, tare da nutsewar makabarta tare da raba mazauna yankin bayan an shafe sa’o’i uku ana ruwan sama kamar da bakin kwarya a makonni biyu da suka gabata, manoman jihar sun roki gwamnatin Jihar Borno da ta kare su da gonakinsu daga bala’in ambaliyar ruwa.

A yayin da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a Bulumkutu, Damboa, Moduganari a cikin Maiduguri sun cika da ambaliyar ruwa, yayin da ruwan ya shafe wata makabarta da ke jajeri a Karamar Hukumar Jere ta jihar, lamarin da ya haifar da fargaba ga jama’a.

Idan za ku iya tunawa, a ranar 10 ga Satumba, 2024 bala’in ambaliya da ya yi sanadiyar rugujewar Dam na Alau ya lalata rayuka da dukiyoyi tare da raba mazauna yankin sama da miliyan guda da muhallinsu.

Haka zalika ya share gonaki da amfanin gonaki a lokacin da lamarin ya faru, don haka manoma da mazauna garin ke yin kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da daukar kwararan matakan dakile sake afkuwar lamarin, musamman ganin cewa ana ci gaba da gyaran madatsar ruwa ta Alau watanni 10 bayan afkuwar lamarin.

Wani manomin shinkafa a garin Zabarmari da ke Karamar Hukumar Jere, Malam Ali Usman ya nuna damuwarsa kan yadda ambaliyar ruwa ta afku a cikin kankanin lokacin damina ta bana, inda ya bayyana cewa matakan da za a dauka kamar magudanan ruwa da samar da abinci daban-daban za su kasance kalubale a bana.

Gwamnan Jihar, Babagana Zulum, ya kawar da fargabar mazauna Kananan Hukumomin Maiduguri da Jere kan yiwuwar ambaliyar ruwa da filayen gonakinsu ta dam din Alau.

 

BENUWAI

Biyo bayan hasashen da Hukumar Kula da Yanayi ta Nijeriya (NiMet) ta yi na cewa za a yi ambaliyar ruwa a Binuwai, gwamnatin jihar ta shawarci mazauna yankunan da ke fama da ambaliyar ruwa da su koma wuraren da ke da tsaro.

Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da manoman jihar musamman na Makurdi da kewaye ke ci gaba da yaba wa Gwamna Hyacinth Alia a fannin yaki da zaizayar kasa.

Wasu daga cikin manoman Makurdi kamar Lydia Awua, wani manomin kabewa da aka fi sani da ‘ugwu’, Terdzugwe Asar, manomin shinkafa da masara da Mdebaan Saaior, sun ce suna fatan samun girbi mai kyau a bana sabanin a baya lokacin da ko da yaushe ambaliyar ruwa ke kwashe gonakinsu.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

কীওয়ার্ড: Ambaliyar Ruwa da ke fama da ambaliyar ruwa a Karamar Hukumar ambaliyar ruwa ta ambaliyar ruwa da bala in ambaliya gwamnatin jihar gwamnatin Jihar mazauna yankin madatsar ruwa Ma aikatar ta ma aikatar ta

এছাড়াও পড়ুন:

‘Yansanda Sun Fara Bincike Kan Rasuwar Wani Dan NYSC A Bauchi

Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga LEADERSHIP a ranar Talata, Kakakin Rundunar ’Yansandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Wakil, ya ce rundunar ‘yansandan ta samu kiran waya da misalin karfe 9:20 na safe daga CLO, inda ya ce Chukwuebuka mai lambar jiha BA/25A/2069 bai farka ba daga barcinsa, yayin da sauran ’yan uwansa Kiristocin ke shirin tafiya wurin bauta a ranar Lahadi.

 

“CLO ya je don ya tayar da shi daga barci amma sai ya gano cewa, ba ya numfashi, nan take ya kai rahoton lamarin ga hedikwatar ‘yansanda ta Dambam,” in ji Wakil.

 

Biyo bayan umarnin kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Sani Omolori-Aliyu, jami’in ‘yansanda na sashen ya jagoranci tawagarsa zuwa wurin.

 

An garzaya da Chukwuebuka zuwa wani asibiti da ke kusa, inda wani likita ya tabbatar da mutuwarsa.

 

Daga bisani, aka akai gawarsa zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Azare, kamar yadda doka ta tanada.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Gwamnatin Tarayya Ta Amince Da Gina Asibitin Dabbobi A Jihar Kwara
  • Kissoshin Rayuwa: Sirar Imam Hassan (a) 125
  • Ranar Matasa: Ciyaman ya jinjina wa gwamnatin Gombe kan ɗaukar matasa aiki
  • Wani Bangaren Majalisar Dokokin Jihar Zamfara Ta Bukaci Gwamnatin Tarayya Da Ta Karbe Mulkin Jihar
  • ‘Yansanda Sun Fara Bincike Kan Rasuwar Wani Dan NYSC A Bauchi
  • Babu Neman Afuwa Kan Nuna Goyan Bayan Tinubu Da Na Yi – Soludo
  • Sin Ta Ware Yuan Miliyan 170 Domin Ayyukan Tallafi Ga Sassan Da Ambaliyar Ruwa Ta Shafa
  • Dasuki: Kotu ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kammala shari’ar kuɗin makamai
  • Rundunar ‘Yan Sandan Kano Ta Yi Gargadi Game Da Sabawa Dokokin Fitillun Bada Hannu A Titinan Jihar