Sharhin Bayan Labarai: Qatar Zata Sauya Amurka A Matsayin Abokiyar Tsaron
Published: 13th, September 2025 GMT
Assalamu alaikum masu sauraro barkammu da warhakan, sharbin bayan labarammu a yau zasu yi magana dangane da ‘yiyuwar gwamnatin kasar Qatar ta nemi maye gurbim Amurka a bangaren tsaron kasarta, bayan cin amanan da Amurka ta yi a ranar talatan da ta gabata.
Kamfanin dillancin labaran Parstoday, ta nakalto wani shafin labarai na yanar gizo a Amurka ‘Axios’.
Axious ta kara da cewa, tunda Benyamin Natanyaho bai tuntubi Washington ko Trump ko kuma wani babban Jami’an gwamnatinsa kafin ya kai hare-haren da ya kai kan doha,!, al-amarin ya fi hatsari idan ya zo kan kasashen duniya, wadanda suka dogara da Amurka don tsaron kasashensu. Anan Amurka zata rasa aminci da yardar da take da shi take da shi daga wasu kasashenata.
Labarin ya kara da cewa Firay ministan kasar ta Qatar Muhammad bin Abdurrahman bin Jassim Al-thani, ya fadawa fadar whitehouse, bayan wannan yaudarar kasarsa zata nemi wani amintacce wanda zai maye gurbin Amurka.
Al-thani ya fadawa tashar talabijan ta CNN kan cewa a halin yanzu kasashen larabawa na yankin tekun farisa suna tattauna yadda zasu maida martani ga wannan al-amarin saboda wasu kasashen yankin da dama suna dogaro da Amurka don tabbatar da tsaron kasashensu. Don haka hare-hare kan Doha ya shafi dukkan wadan nan kasashe.
Har’ila yau rahoton ya bayyana cewa, bayan hare-haren da JMI ta kaiwa Al-udait ‘Air Base” a cikin yakin kwanaki 12 wanda Amurka ta jefa boma-bomai kan cibiyar makamashin nukliya na kasar, da kuma hare-haren da HKI kan Doha, Qatar tana ganin dole ta sake lalen harkokin tsaron kasar.
Rahoton ya ce, Al Thani ya fadawa Steve Witkoff, jakadan Amurka na musamman a gabas ta tsakiya kan cewa, Qatar zata sake duba harkokin tsaron kasar , musamman tare da Amurka saboda samun cikekken tsaro ga kasar.
Dangane da wannan shafin yanar gizo na labarai ‘Axios ta sami wani bayani da ke cewa shugaban Trump ya bukuci Natanyahu ya dauki alkali ba zai sake kaiwa kasar Qatar hare-hare ba.
Sannan bayan haka, Natanyahu bai nemi Afwar kasar Qatar ba, kuma ya ma yi alkawalin zai sake kai wasu hare-haren a kan doha idan bukatar haka ta kama.
Qatar dai itace kasar Larabawa ta 7 wacce HKI ta yiwa ruwan boma bomai tun bayana fara yaki a gaza a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta, banda Gaza da yankin yamma da kogin Jordan, yahudawan sun kai hare-hare kan Lebanon, Syriya Iraki, Iran da kuma ita Qatar
Axios ya bayyana cewa a ranar Talatan da Natanyahu ya kai hare-hare kan Doha, shugaba Trump ya kira Natanyahu ta wayar tarho, har sau biyu, da farko yay a bayyana rashin aqmincewa da kai hare-haren, sannan tare da tambayarsa menene amfani na dogon zangon da HKI zata samu,
Wani tsohon jami’in gwamnatin Amurka ya bayyana cewa, Firay ministan kasar Qatar ya na daukar hare-haren a matsayin yaudara daga Tel’viv da kuma washingtong gaba daya.
Banda haka Benyamin Natanyahu ya fito a ranar Laraba yana fadar cewa yayi dai dai a hare-haren da ya kai Doha, sannan idan yan kungiyar Hamas sun ci gaba da kasancewa a kasar Qatar zai sake kai masu hare-hare.
Sannan ya kara da cewa hare-harensa a kan doha yana dai dai da hare-haren Amurka a kan Afganistan da Pakistan a lokacinda take neman kungiyar Al-Qaeda bayan ga watan Satumba.
Al-thani ya fadawa CNN kan cewa dole a hukunta Natanyahu, saboda keta hurumin kasa mai cikekken yanzi, wanda yin hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa tare da kiranta Yar ta’adda.
Daga karshe Althani ya bayyana cewa, a halin yanzu tana tattaunawa da sauran kasashen larabawa na yankin tekun farisa, inda zasu iya maida martanin da zai sanya yankin shiga hatsari.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Adadin wadanda sukayi shahada sakamakon kisan kare dangi na Isra’ila ya kai 64,756 September 13, 2025 Unicef : Yara na cikin ukuba sanadin shingen Isra’ila a Gaza September 13, 2025 Araqchi: Babu Dalilin Jin Tsoron Tattaunawa September 12, 2025 Welayati: Abin Kunya Ne Yadda Duniya Ta Yi Shiru Kan Laifukan Isra’ila September 12, 2025 Ayatullah Khatami Ya Ja Hankalin Kasashen Larabawa Kan Hare-Haren Isra’ila September 12, 2025 Gaza: Falastinawa 48 Suka Yi Shahada A Hare-Haren Isra’ila September 12, 2025 Jagororin Hamas Sun Kubuta Daga Kisan Gillar Isra’ila Ne A Lokacin Da Suka Tafi Yin Sallah September 12, 2025 Qatar : shugabannin Isra’ila na kishirwar jefa duniya cikin rikici September 12, 2025 Guteress ya tattauna da Araghchi kan shirin shurin nukiliyar Iran September 12, 2025 Netanyahu, ya sha alwashin dakile kafa kasar falasdinawa September 12, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: ya bayyana cewa kai hare hare hare haren da a hare haren kasar Qatar
এছাড়াও পড়ুন:
Yadda Ta Gudana A Taron Karɓar Ƴan Majalisa Shida Da Suka Koma APC
ShareTweetSendShare MASU ALAKA Manyan Labarai Majalisar Dattawa Ta Tabbatar Da Bernard Doro A Matsayin Ministan Harkokin Jin Ƙai October 30, 2025
Manyan Labarai Wata 3 Da Naɗin Shugaban APC, Sunan Yilwatda Har Yanzu Na Nan A Matsayin Minista A Shafin Ma’aikatar October 30, 2025
Manyan Labarai Tinubu Ya Amince Da Ƙara Harajin Shigo Da Man Fetur Da Dizal Zuwa Kashi 15 October 30, 2025