Aminiya:
2025-11-02@19:37:44 GMT

Tinubu ya bayar da umarnin a sake karya farashin kayan abinci

Published: 11th, September 2025 GMT

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya umarci Kwamitin Majalisar Zartarsa ta Kasa da ya dada aiwatar da matakan da za su kara karya farashin kayan abinci a fadin Najeriya.

Karamin Ministan Noma da Samar da Abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja.

EFCC ta tsare Mele Kyari kan binciken matatun mai Macron ya karɓi baƙuncin Tinubu a Fadar Elysee

Ya ce umarnin ya shafi tabbatar da cewa an rage farashin sufurin kayan amfanin gona ba tare da kashe makudan kudade ba.

“Shugaban Kasa ya bayar da umarni ga Kwamitin Majalisar Zartarsa ta Kasa wanda dama yanzu haka yana nan yana kokarin ganin an saukaka hanyoyin sufurin amfanin gona a fadin kasar nan, da su dada karya farashin kasa da yadda yake yanzu haka a kasuwa,” in ji ministan, kamar yadda ya fada yayin wani taron kara wa juna sani da aka shirya wa ’yan jaridar Fadar Shugaban Kasa.

Najeriya, wacce ita ce kasa mafi yawan jama’a a nahiyar Afirka dai na fama da matsalar abinci, wacce ta ta’azzara tun bayan cire tallafin man fetur da tsadar sufuri da kuma matsalolin tsaro a kan manyan hanyoyi da ya kawo cikas ga jigilar kayan amfanin gona.

Duk da matakan da gwamnati ta ce tana dauka dai, har yanzu miliyoyin ’yan Najeriya ba sa iya samun wadataccen abinci.

Sai dai ministan ya ce umarnin na Tinubu wani bangare ne na burin shi na tabbatar da samar da isasshe kuma lafiyayyen abinci da kowa zai iya saye a Najeriya.

Ministan ya kuma ce nan ba da jimawa ba gwamnati za ta fito da wani sabon shiri na bunkasa kasar noma da zai bunkasa amfanin da ake samu sannan ya samar wa da manoma rance domin tallafa wa manoman da ke yankunan karkara.

Ko a watan Yunin da ya gabata, sai da Shugaba Tinubu ya jaddada cewa Najeriya na kan hanyar tsayawa da kafarta a harkar samar da abinci, la’akari da manufofin da gwamnatinsa ta bullo da su.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: Karya farashi Kayan abinci

এছাড়াও পড়ুন:

Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya mayar wa da Shugaban Amurka, Donald Trump martani cewa Najeriya ba ta yadda da duk wani nau’in zarafin addini.

Tinubu, ya yi wannan bayani ne bayan Trump ya sake sanya Najeriya cikin jerin ƙasashen da ake kiran “Ƙasashen da ke da Babbar Matsala wajen ’Yancin Addini.”

PDP ta dakatar da Anyanwu da wasu ’yan tsagin Wike Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa

Trump ya yi iƙirarin cewa Kiristoci a Najeriya na fuskantar barazana, amma ya sha alwashin cewa Amurka za ta kare su.

A cikin wani saƙo da ya wallafa a kafafen sada zumunta, Trump ya rubuta cewa: “Addinin Kirista yana fuskantar babbar barazana a Najeriya. Ana kashe dubban Kiristoci.”

A ranar Asabar, Tinubu ya mayar da martani ta kafar sada zumunta, inda ya ce Najeriya ƙasa ce mai dimokuraɗiyya wadda kundinta ya tabbatar da ’yancin yin addini.

“Najeriya tana da cikakken tanadi a kundinta da ya tabbatar da ’yancin yin addini,” in ji Tinubu.

“Tun daga shekarar 2023, gwamnatina na aiki tare da shugabannin Kiristoci da Musulmai don magance matsalolin tsaro da ke shafar jama’a daga kowane ɓangare da addini.”

Ya ƙara da cewa, kiran Najeriya ƙasa mai matsala wajen gudanar addini ba gaskiya ba ne.

“Za mu ci gaba da kare ’yancin kowane ɗan ƙasa na yin addininsa cikin walwala. Najeriya ba ta goyon bayan zaluncin addini ko kaɗan,” in ji Tinubu.

Ya kuma ce Najeriya za ta ci gaba da haɗa kai da Amurka da sauran ƙasashe domin inganta zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai daban-daban.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya yanke hulɗa da Amurka kawai — Sheikh Gumi
  • A Kan Wa Trump Ke Son Kaddamar Da Hari a Najeriya?
  • Hamas ta musanta zargin Amurka na cewa tana sace kayan agaji a Gaza
  • Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini ba — Tinubu
  • Zargin Kisan Kiristoci: Najeriya ba ta yadda da cin zarafin addini — Tinubu
  • Sharrin son auren Mai Wushirya aka yi min — Mansura Isa
  • Zaben 2027 Zai Kasance Ne Tsakanin Mulkin Tinubu Da Zabin Ƴan Nijeriya —Atiku Abubakar
  • Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Ƙulla Alaƙa Ta Kut-da-kut Tsakanin Hukumar Shige Da Fice Da Kwastam – Babandede
  • An sake kama shi a cikin ’yan fashi kwana 5 da fitowa daga kurkuku
  • Babu wani uzuri da za a yi wa sabbin hafsoshi kan matsalar tsaron Nijeriya — Tinubu