Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun ya bayyana a yau 22 ga wannan wata cewa, a yayin da ake raya duniya bisa tsarin bai daya, musayar kwararru a tsakanin kasa da kasa ta sa kaimi ga raya fasahohi da tattalin arzikin kasashen duniya. Kasar Sin tana maraba da kwararru daga bangarori da sana’o’i daban daban na kasa da kasa su zo kasar ta Sin su gudanar da harkokinsu don sa kaimi ga raya zamantakewar al’ummar dan Adam da kuma samun ci gaban sha’aninsu baki daya.

(Zainab Zhang)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

উৎস: Leadership News Hausa

এছাড়াও পড়ুন:

An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa

A cewar ‘yansanda, “A ranar 10/10/25, an gayyato wani Mista Oke Emmanuel, dan NYSC kuma abokin dakin wanda ya bace, domin yi masa tambayoyi. Ya tabbatar cewa wanda ake nema ya kasance tare da iyalan George har zuwa 06/10/25.

“An samu karin bayani daga George cewa dan NYSC din ya koka da rashin lafiya, aka kai su Asibitin Kaiama Referral Hospital a ranar 04/10/25, kuma aka sallame shi ranar 05/10/25. Sai dai a ranar 06/10/25, dan NYSC din ya bace zuwa wani wurin da ba a sani ba.”

‘Yansanda kuma suna binciken zargin karbar kudin rashawa na Naira 100,000 daga iyayen wanda ya bace, da wasu fursunoni biyu da ke gidan gyaran hali na Igbara, Abeokuta, Jihar Ogun, wadanda suka yi suna kamar masu garkuwa da mutane.

“An bar wayar salula ta wanda ya bace a dakinsa. Jami’an bincike suka bi layin kira daga lambar 0906193291, inda aka gano tana hannun wani fursuna da ake tsare da shi a cibiyar gyaran hali ta Igbara, Abeokuta, saboda wani laifin garkuwa da mutane.

“Wanda ake zargin ya ce sun ga lambar wayar a kafafen sada zumunta, suka yi amfani da ita don cutar da mahaifin wanda ya bace, Mista Anyanwu Simon, mai shekara 56. An biya kudin Naira 100,000 zuwa asusun Opay mai lamba 7042793493 na wata Atinuke Oluwalose, abokiyar hadin bakin fursunan da ke gidan yarin Abeokuta.”

“Daga bayanan da jami’an bincike suka gano, akwai wasu abubuwan damuwa da ka iya kasancewa silar abin da ya faru. An gano wasu kalaman da wanda ya bace ya yi dangane da wasu sabbin dabi’u da sha’awowi da ba su dace da akidar addininsa ba,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta kammala da cewa ana ci gaba da daukar matakan bincike “domin tabbatar da sakamakon da jami’an bincike suka tattara, kasancewar binciken ya fito da abubuwa masu ban mamaki. Ba a samu wata alamar garkuwa da mutane a wannan lamari ba. Ana ci gaba da aiki domin samun cikakken bincike.”

PUNCH Metro ta ruwaito a watan Oktoba 2024 cewa an kama mutum hudu kan bacewar wani dan NYSC mai suna Yahya Faruk, wanda yake hidima a Ikuru, cikin Karamar Hukumar Andoni ta jihar.

ShareTweetSendShare MASU ALAKA Kotu Da Ɗansanda An Damke Mutum 11 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Matashi A Bauchi November 8, 2025 Kotu Da Ɗansanda Jami’an Tsaro Sun Kwato Wayoyi 45 Daga Hannun Wata Kungiyar Barayi October 4, 2025 Kotu Da Ɗansanda ‘Yansanda Sun Kama Mutum Hudu Da Ake Zargi Da Aikata Muggan Laifuka A Yobe October 4, 2025

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • NELFUND Ta Ce Dalibai Miliyan Daya Ne Suka Nemi Tallafin Kudin Karatu
  • An Fara Binciken Batan Dan Bautar Kasa A Bayelsa
  • Kasar Sin Ta Musanta Zargin Da Wakilin Amurka Ya Yi Game Da Batun Sauyin Yanayi
  • Batun Kawo Harin Soja: ‘Yan Nijeriya Sun Yi Watsi Da Barazanar Trump
  • A Karon Farko An Gabatar Da Ka’idar Kasa Da Kasa Ta Fasahar 5G Mai Amfani Ga Masana’antu
  • Araqchi Ya Ce: Harin Amurka Kan Kasar Venezuela Ya Bayyana Karara Duniya Tana Gani
  • NAJERIYA A YAU: Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Basir
  • Yanayi Mai Launin Zinare A Kasar Sin
  • Nazarin Cgtn: Kasashe Masu Tasowa Sun Yi Kira Da A Inganta Tsarin Tafiyar Da Harkokin Duniya
  • Firaministan Kasar Sin Ya Gabatar Da Jawabi A Bikin Bude CIIE