Yadda ’yan haya za su samu ragin N500,000 a shekara
Published: 26th, September 2025 GMT
Gwamnatin Tarayya ta amince da sabuwar dokar haraji wadda za ta bai wa ’yan haya damar samun ragin har Naira dubu ɗari biyar.
Dokar ta amince da yi wa ’yan haya ragin kashi 20% daga harajin kudin shiga a kan kuɗin hayar da suke biya a shekara.
Sojoji sun kashe ’yan ta’adda tare da ƙwato makamai a Neja Babu wata jam’iyya dana ke shirin komawa — KwankwasoSai dai kuma, wannnan ragin ba zai haura haura Naira 500,000 ba.
A watan Agustan shekarar 2023 Shugaba Bola Tinubu ya kafa kwamitin sake fasalin haraji karkashin jagorancin Taiwo Oyedele.
Bayan shekaru biyu, Majalisar Dokoki ta Kasa ta amince da sabbin dokoki guda hudu, wadanda shugaban kasar ya rattaba hannu kuma aka buga a kundin gwamnati a ranar 10 ga Satumba, 2025.
Wadannan sabbin dokokin haraji za su fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026.
Sabbin dokokin sun hada da:
1- Dokar Haraji ta Nijeriya (NTA)
2- Dokagar Gudanar da Haraji
3- Dokar Hukumar Haraji ta Nijeria (NRS)Nigeria
4- Dokar Hukuamr Haraji ta Bai-daya
Sababbin dokoki sun maye gurbin dokoki fiye da guda 12 da suka dade suna aiki a bangaren harajin Nijeiya.
Ragin kudin hararji ga ’yan hayaSashe na 30 (26) na Dokar Haraji ta Kasa (NTA), ya amince wa ’yan haya samun ragin haraji ta hanyar cire kashi 20 cikin 100 na kudin hayarsu na shekara daga abin da za su biya. Sai dai wannan rangwamen ba zai wuce Naira 500,000 ba.
Misali:
Idan kudin hayarka ta shekara Naira miliyan daya da dubu dari biyar ne, za ka iya samun ragin N300,000 (20%) daga haraji.
Idan kuma kudin hayarka ya kai N3,000,000, to N500,000 kawai za ka iya ragewa, duk da cewa 20% ya fi haka.
Wani hanzari ba gudu ba! Mutum ba zai ci gajiyar wannan rangwamen ba, sai idan ya bayyana kudin hayarsa daidai tare da gabatar da takardun da ke tabbatar da hakan.
Haka kuma, masu gidaje da kuma wadanda ke zaune a gidajen da ba sa biyan haya ba sa cikin masu cin gajiyar wannan rangwamen.
Wadanda dokar ta shafa su ne:
– Masu haya da ke da yarjejeniyar kwangilar haya a rubuce.
– Ba ta shafi masu gidaje da masu zama a gidajen gwamnati ko na kamfani ba tare da biyan haya ba.
Wani Karin sauki a dokar shi ne:
– An soke biyan harajin BAT a kan kayan abinci da ilimi.
– Masu karbar albashin kasa da Naira 800,000 a shekara ba za su biya harajin kudin shiga ba.
– Kananan ’yan kasuwa da cinikinsu a shekara bai fi Naira miliyan 100 ba, za su ci gaba da aiki ba tare da biyan harajin kamfani ba, amma dole su yi rajista da Hukumar Rajisar Kamfanoni (CAC) tare da amfani da tsarin e-inboicing.
– Sa’annan, an soke harajin tambari daga yarjejeniyar haya da kudinta bai fi Naira miliyan 10 ba a kowane wata.
Haka kuma;
– Masu saka hannun jari a harkar gidaje za su ci gajiyar rangwamen haraji ta hanyar REITs.
– Harajin rikon kudi (withholdin tad) a kan haya ya sauka zuwa kashi 2 cikin 100 ga ’yan kasa, yayin da ’yan kasashen waje za su biya kashi 5 cikin 100.
Wasu karin dokoki su ne:
– Masu samun kudaden shiga sama da Naira miliyan 50 za su biya haraji har na kimanin kashi 25 cikin 100.
– Wannan sabon tsarin ya hada da dukiyar da ake samu daga kasashen waje, ribar jarin da aka samu (har da kadarorin crypto), da kuma fa’idodin da ba a ba da su kai tsaye ba.
– Manyan kamfanoni za su ci gaba da biyan harajin kamfani na kashi 30 cikin 100, duk da cewa wasu muhimman sassa na tattalin arziki na iya samun rangwame zuwa kashi 25 cikin 100.
– Kamfanonin kasa da kasa za su fara biyan mafi karancin haraji na kashi 15 cikin 100, tare da karin haraji a kan ribar da ba a raba ba da ke waje.
Sabon tsarin harajin ya nufi karfafa gaskiya da bin doka a cikin tsarin kudi na kasa.
Masana irin su Barista Festus Adebayo, daraktan cibiyar kare hakkokin gidaje (HDAN), na ganin sabuwar dokar na da na da amfani sosai.
“Babban sauki ne ga masu haya saboda mun shawarci kwamitin haraji da a yi doka dam za ta kawo mana sauki mana a fannin gidaje, kuma sun yi abin da muka roka.
“Mun fi son a dora wa masu kudi nauyi, a yi wa talakawa rangwame,” in ji shi.
Ya kuma yi kira da a fara dora haraji kan gidajen da aka gina amma aka bar su ba a amfani da su domin tilasta masu su yin amfani da su yadda ya dace.
Ku mene ne ra’ayinku?
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Dokar Haraji Gwamnatin tarayya haya Naira miliyan
এছাড়াও পড়ুন:
Juyin mulki ya rutsa da Jonathan a Guinea-Bissau
Tsohon Shugaban Ƙasa, Goodluck Jonathan, ya maƙale a Guinea-Bissau bayan da sojoji suka yi juyin mulki tare da karɓe ragamar mulkin ƙasar.
Jonathan da sauran baƙi baƙi masu sanya ido kan zaɓen da aka gudanar, ba za su iya barin ƙasar ba domin sojoji sun rufe iyakokin ƙasar baki ɗaya, tare da dakatar da zaɓen gaba ɗaya.
Ɗan bindiga ya harbe sojoji 2 a fadar shugaban Amurka Andrea Thompson ta zama mace mafi ƙarfi a duniyaLamarin ya samo asali ne bayan manyan ’yan takara biyu sun yi iƙirarin samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana.
Ba jimawa wasu dakarun sojin ƙasar suka hamɓarar da gwamnatin farar hula ta ƙasar.
Sun kuma sanar da dokar hana fita da kuma kama manyan jami’an da ke da alaƙa da zaɓen.
“An hamɓarar da gwamnatina,” in ji Shugaba Umaro Sissoco Embalo cikin wata tattaunawa ta waya da gidan talabijin na ƙasashen waje.
Jonathan ya je Guinea-Bissau ne a matsayin shugaban tawagar West African Elders Forum (WAEF) domin sanya ido kan zaɓen.
Ya ziyarci wasu rumfunan zaɓe a ƙasar kuma ya wallafa bayanai a kafafen sada zumunta kafin juyin mulkin.
Mutanen da ke tare da shi sun ce yana cikin ƙoshin lafiya, amma ba shi da damar barin ƙasar.
Sojojin suna kuma ƙoƙarin katse Intanet, lamarin da ya sa ake samun tangarɗa wajen sadarwa a ƙasar.
Hakan ya sa ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa suka fara nuna damuwa kan tsaron manyan ’yan siyasa da jami’an zaɓe.
A cikin wata sanarwa, Jonathan da wasu shugabannin Afirka sun yi Allah-wadai da juyin mulkin.
“Mun yi Allah-wadai da wannan yunƙuri na daƙile tsarin dimokuraɗiyya, kuma muna kira ga Tarayyar Afirka da ECOWAS su ɗauki matakin dawo da tsarin mulki,” in ji su.
Sun buƙaci mutanen Guinea-Bissau su kwantar da hankalinsu, tare da kira ga sojoji su saki dukkanin jami’an da suka kama domin a ci gaba da gudanar da zaɓe cikin lumana.