Italiya : Mutane da dama sun jikkata yayin arangama da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu
Published: 28th, September 2025 GMT
A Italiya mutane da dama sun jikkata yayin arangama tsakanin ‘yan sanda da masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinu.
Rahotanni sun ce kimanin mutane 10 ne suka jikkata yayin zanga-zangar ta nuna goyon bayan Falasdinu bayan da ‘yan sanda suka yi kokarin hana masu zanga-zangar da ruwan zafi da hayaki mai sa hawaye a ranar Asabar.
Zanga-zangar nuna goyon bayan Falasdinu, wacce ta fara ranar Juma’a a Rome, Milan, Naples, da Bologna, ta bazu a ranar Asabar zuwa Florence, Pisa, Ancona, Trieste, Bari, da Alessandria.
Zanga-zangar ta nuna goyon baya ga Gaza da al’ummar Palasdinu na karuwa a tashoshin jiragen ruwa, jami’o’i, makarantu, da wuraren taruwar jama’a a Italiya gabanin zanga-zangar kasa da aka shirya yi a ranar 4 ga Oktoba a birnin Rome.
A ranar 22 ga watan Satumba, an gudanar da wani yajin aikin gama-gari na sa’o’i 24 da kungiyoyin kwadago da dama suka kira a fadin kasar Italiya domin nuna adawa da hadin kan kasar a kisan kiyashin da aka yi a Gaza.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Isra’ila ta kashe Falasdinawa kusan 100 a hare-haren da ta kai a Gaza September 28, 2025 Pezeshkian: Iran za ta dauki matakan da suka dace domin shawo kan takunkumi September 28, 2025 Afirka ta Kudu da Sin sun kara habaka huldar tattalin arziki don tukarar harajin Amurka September 28, 2025 Sheikh Qassem: Ba za mu mika makamin gwagwarmaya ba September 28, 2025 Iran: Kisan Nasrallah ya saba wa kundin tsarin mulkin MDD September 28, 2025 Argentina ta nemi jinkirta ziyarar Netanyahu a kasar saboda fargabar boren jama’a September 28, 2025 Sojojin Isra’ila Sun Kashe Sama Da Falasdinawa 77 A Gaza A Yau Kawai. September 27, 2025 An Gudanar Da Taron Cika Shekara 1 Da Shahadar Sayyid Nasrullah September 27, 2025 Yunkurin Jinkirta Dawo Da Takunkumi Kan Kasar Iran Bai Yi Nasara ba. September 27, 2025 Shugaban Hukumar IAEA Ya Ce Shirin Nukiliyar Iran Na Zaman Lafiya Ne September 27, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: goyon bayan Falasdinu zanga zangar
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan sanda sun kama masu laifi da 34 a Kaduna
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kaduna, ta bayyana sabbin nasarorin da ta samu wajen yaƙi da laifuka a jihar, ta hanyar holen mutum 34 da ta kama da aikata laifuka daban-daban.
Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Rabi’u Muhammad, ya ce wannan ci gaba ya samu ne saboda sabbin dabarun aiki da kuma bayanan sirri da aka samu daga al’umma da hukumomin tsaro.
Jami’an tsaro sun ƙaddamar da shirin murƙushe ’yan bindiga a Kaduna Zulum ya ba kowanne ɗalibin Borno da ke karatu a Indiya tallafin N500,000A Anguwar Barnawa da wasu wurare a Kaduna, rundunar Operation Fushin Kada ta kama mutane 13 da ake zargi da aikata fashi da makami da satar wayoyi a otel-otel da gidaje.
An ruwaito sun taɓa kashe ɗan sanda a shekarar 2024, kuma suna samun bayanai daga dilolin miyagun ƙwayoyi a wuraren shaƙatawa. A
An ƙwato bindiga ƙirar gida, gatari da adduna 13, mota, kwamfuta huɗu, wayoyi 13 da talabijin huɗu.
Haka kuma, a Nunbu Bashayi da ke Sanga, an kama mutane bakwai da ake zargi da garkuwa da mutane tare da neman kuɗin fansa.
Dukkanimsu sun amsa laifinsu kuma ana neman ragowar waɗanda suke tsere.
A wani samame daban, ’yan sanda sun kama wasu mutane huɗu da ake zargi da aikata fashi, fyaɗe da damfara.
Sun saba kai hari gidajen mutane, ɗaukar kuɗaɗen mutane, aikata fyaɗe sannan su riƙa ɗaukar bidiyo tsoratar da mutane.
A Zariya kuwa, an kama wasu mutane tara da suka haɗa da maza da mata waɗanda ake zargi da yi wa direban Adaidaita sahu fashi ta hanyar zuba masa magani a abin sha.
Rundunar ta kuma kama wani likitan bogi mai suna Adamu Abubakar Muhammed wanda ya yi wa mutane tiyata ba tare da shaidar karatun likitanci ba.
Ya yi amfani da takardun bogi wajen yin aiki na tsawon wata guda kafin a gano shi.
Kwamishinan, ya ce duk waɗanda aka kama suna hannun rundunar, kuma za a gurfanar da su kotu bayan kammala bincike.
Ya gode wa jami’an tsaro da al’umma kan haɗin kai, inda ya yi da a ci gaba da bayar da sahihan bayanai domin inganta tsaro a jihar da ƙasa baki ɗaya.