Ma’aikatan jinya sun dakatar da yajin aiki a faɗin Najeriya
Published: 2nd, August 2025 GMT
Ƙungiyar Ma’aikatan Jinya ta Najeriya (NANNM), ta dakatar da yajin aikin gargaɗi na kwanaki bakwai da ta fara a faɗin ƙasar nan.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne cikin wata takarda da shugabanta ƙasa, Haruna Mamman, da sakatarenta, T.A. Shettima, suka sanya wa hannu.
Rufe gidan rediyo ya haifar da cece-ku-ce a Neja Jami’ar Umaru Yar’adua ta kori ɗalibai 57 kan satar jarabawaSun fara yajin aikin ya fara ne a ranar Laraba tare da niyyar shafe kwanaki bakwai suna yin sa.
Ma’aikatan jinyar sun shiga yajin aikin ne saboda ƙarancin albashi, ƙarancin ma’aikata, da kuma rashin ingantattun wuraren aiki.
Wannan yajin aiki na zuwa ne a daidai lokacin da likitoci ke takun saƙa da gwamnati kan batutuwan suka shafi jin daɗin aikinsu.
Aminiya ta ruwaito yadda yajin aikin ya janyo ya haifar da tsaiko ga ayyukan lafiya a sassa daban-daban na ƙasar nan.
Sun fara yajin ne bayan ƙarewar wa’adin kwana 15 da ƙungiyarsu ta bai wa Gwamnatin Tarayya.
A ranar Asabar ne ƙungiyar ta dakatar da yajin aikin bayan wani taro ta Intanet da shugabanninta suka gudanar.
A ranar Juma’a, ƙungiyar ta gana da Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da Ma’aikatar Ƙwadago, Ofishin Shugaban Ma’aikata, Ofishin Akanta-Janar, da Hukumar Albashi da Alawus da wasu ɓangarori na masu ruwa da tsaki domin tattauna buƙatunsu.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, NANNM ta ce ta dakatar da yajin aikin ne bayan duba yarjejeniyar da suka cimma da gwamnati.
Sanarwar, ta ce gwamnati ta ɗauki matakai masu muhimmanci kuma ta bayar da jadawalin lokacin da za ta cika alƙawuran.
Saboda wannan yarjejeniya da kuma samun masalaha, ƙungiyar ta dakatar da yajin aikin nan take.
Ta kuma umarci dukkanin ma’aikatan jinya da su koma bakin aiki, tare da gargaɗin cewa ba za ta amince a hukunta kowa ba saboda shiga yajin aikin.
Ƙungiyar ta gode wa mambobinta bisa goyon baya da haɗin kai, tare da tabbatar da cewa za ta ci gaba da kare haƙƙinsu.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: jinya tattaunawa Yajin aiki yarjejeniya ta dakatar da yajin aikin
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Kula da Da’ar Ma’aikata Za Ta Fara Daukar Bayanai Ta Yanar Gizo
Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta sanar da cewa, a halin yanzu ana iya bayyana kadarorin ma’aikatan ta hanyar yanar gizo, wani mataki da aka tsara domin saukaka aikin da kuma kara yin lissafi.
Daraktan ofishin na jihar Jigawa Abubakar Bello ne ya bayyana haka a lokacin da ya ziyarci shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri a ofishin sa.
Abubakar Bello ya jaddada cewa sabon shirin na da nufin rage dinbin aikin dake gaban ma’aiakata da kuma saukaka tantance kadarorin domin yaki da cin hanci da rashawa a cikin tsarin.
“Mun sauya dabara zuwa rajista ta yanar gizo don bayyana kadarorin, muna ba wa mutane damar kammala aikin daga gidajensu. Duk da haka, muna neman goyon bayan ku don tabbatar da cewa an sanar da jami’an gwamnati tare da karfafa gwiwar su bi wannan sabon tsari,” in ji shi.
Da yake mayar da jawabi, shugaban ma’aikata na jiha Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya yi alkawarin wayar da kan jami’an gwamnati cikin tsanaki game da muhimmancin bayyana kadarorin su, kamar yadda hukumar da’ar ma’aikata ta ba su umarni.
Ya tunatar da cewa rashin yin biyayya ga kundin tsarin mulkin kasa ne.
Dagaceri ya bada tabbacin bada goyon baya da hadin kai domin cimma burin da ake so na wannan shiri.
USMAN MZ