Sojoji sun kashe mayaƙan Boko Haram 12, sun ƙwato makamai a Borno
Published: 31st, August 2025 GMT
Dakarun Operation Haɗin Kai (OPHK) tare da Civilian JTF, sun yi nasarar kashe mayaƙan Boko Haram da ISWAP 12 a Jihar Borno.
A ranar 29 zuwa 30 ga watan Agusta, sojojin sun kai farmaki ƙauyukan Tamsu Ngamdu, Dalakaleri, Gaza da Loskori Kura, inda suka yi artabu da ‘yan ta’addan.
Tsohon Sufeto-Janar na ’yan sandan Nijeriya Solomon Arase ya rasu An ƙone wata mata ƙurmus kan yi wa Annabi ɓatanci a NejaA Loskori Kura, sojojin sun yi nasara, inda suka kashe ’yan ta’adda 12, suka kuma kwato8 bindiga ƙirar AK-47 guda shida, harsasai guda takwas da magunguna iri-iri.
Majiyoyin tsaro sun ce wasu daga cikin ’yan ta’addan sun ji raunuka, bayan artabun da suka yi da sojojin.
Wannan farmaki ya lalata hanyoyin sadarwar ’yan ta’addan da dabarunsu a yankin, ya kuma haifar musu da cikas.
Wannan nasara na zuwa ne a dai-dai lokacin da dakarun Nijeriya ke ƙara kai hare-hare ta ƙasa da sama a Arewa maso Gabas, musamman a dajin Sambisa, tafkin Chadi da tsaunin Mandara, domin kawo ƙarshen ta’addanci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Boko Haram Farmaki hari ISWAP
এছাড়াও পড়ুন:
’Yan bindiga sun sace mutum 40 a masallaci a Zamfara
Aƙalla masallata 40 ’yan bindiga suka sace a wani masallaci da ke Gidan Turbe a Karamar Hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara da safiyar wannan Litinin.
Majiyoyi sun ce an yi awon gaba da masallatan ne zuwa dazukan Gohori da ke yankin Tsafe.
Hauhawar farashi ya ragu a watan Agusta — NBS NDLEA ta kama ɗan Indiya da ƙwaya ta Naira biliyan 3 a LegasWannan harin dai kai tsaye masu ruwa da tsaki na kallonsa a matsayin kawo ƙarshen yarjejeniyar sulhu tsakanin ’yan bindigar da mahukuntan jihohin Zamfara da Katsina.
A baya-bayan nan ne jihohin Katsina da Zamfara suka ƙulla yarjejeniyar sulhu tsakaninsu da ’yan bindigar da suka addabi al’ummar jihohin arewa maso yammacin Najeriyar.
Yarjejeniyar sulhu da aka cimma a dajin Wurma ta samu halartan manyan ’yan bindiga irinsu Alhaji Usman Kachalla Ruga da Muhindinge da Yahaya Sani ( Hayyu ) da kuma Shu’aibu.
A ɓangaren mahukunta, akwai Maradin Katsina da Hakimin Kurfi, Alhaji Mansur Amadu Kurfi da kuma shugaban ƙaramar hukuma Babangida Abdullahi Kurfi.
’Yan bindiga sun saki wasu mutane da suke garkuwa da su a lokacin yarjejeniyar sulhun, tare da barin al’umma zuwa gonakinsu ba tare da wata fargaba ko tsangwama.
To sai dai kuma, ƙasa da wata guda bayan cimma wannan yarjejeniya, rahotanni sun ce ’yan bindiga sun kutsawa wani ƙauye a Zamfara tare da awon gaba da masallata.
Shaidun gani da ido sun ce, maharan sun yi wa masallacin ƙawanya da misalin ƙarfe 5:30 na safe, daidai lokacin da jama’a ke sallar asuba.