Firaministan Kasar Sin Li Qiang Ya Taya Nestor Ntahontuye Murnar Zama Sabon Firaministan Kasar Burundi
Published: 27th, August 2025 GMT
A yau Talata 26 ga wata ne, firaministan kasar Sin, Li Qiang, ya isar da sako zuwa ga Nestor Ntahontuye, don taya shi murnar zama sabon firaministan kasar Burundi.
A sakon nasa, firaminista Li ya bayyana cewa, a ’yan shekarun nan, karkashin jagorancin shugabannin kasashen biyu, wato Xi Jinping da Evariste Ndayishimiye, an cimma manyan nasarori wajen inganta hadin-gwiwar kasashensu a fannoni daban-daban.
Firaminista Li ya ce yana fatan kara kokari tare da Nestor Ntahontuye, don aiwatar da muhimman ra’ayoyi iri daya da aka cimma tsakanin shugabannin kasashen biyu, gami da nasarorin da aka samu a wajen taron kolin FOCAC na Beijing, ta yadda nasarorin dangantakar Sin da Burundi za su kara amfana wa al’ummominsu. (Murtala Zhang)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
An tattauna yadda za a inganta walwalar malamai a Gombe
Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Najeriya (NUT) reshen Jihar Gombe, ta ziyarci shugaban ƙungiyar shugabannin ƙananan hukumomi na jihar, Barista Sani Ahmad Haruna, a ofishinsa da ke Gombe.
Shugaban ƙungiyar, wanda shi ne shugaban Ƙaramar Hukumar Gombe, ya bayyana cewa gwamnati da shugabannin ƙananan hukumomi za su ci gaba da yin duk mai yiwuwa wajen inganta walwalar malamai.
Tinubu ya janye dokar ta-ɓaci da ya sanya a Ribas Saudiyya ta saki ’yan Najeriya 3 da ta kama kan zargin safarar miyagun ƙwayoyiYa ce: “Ba za mu taɓa barin malamai su shiga cikin matsanancin hali ba. Za mu duba matsalolinsu domin tabbatar da walwalarsu da ci gaban ilimi a jihar.”
Sani, ya kuma yaba da yadda NUT ke tattaunawa cikin lumana da kawo shawarwari maimakon ɗaukar matakan da za su iya kawo tsaiko ga harkar ilimi.
A nasa jawabin, shugaban NUT na jihar ya ce sun kai ziyarar ne domin tattauna matsalolin da malamai ke fuskanta, musamman na makarantun firamare da ƙananun sakandare da ke ƙarƙashin kulawar ƙananan hukumomi.
Ya ƙara da cewa manufar NUT ita ce samar da fahimtar juna da haɗin kai tsakaninsu da shugabannin ƙananan hukumomi domin gano hanyoyin magance matsaloli cikin lumana.