Ambaliya: An gano gawar ’yar shekara 3 da ruwa ya tafi da ita a Zariya
Published: 14th, September 2025 GMT
An gano gawar Haneefa, yarinya ’yar shekara uku da ruwa ya tafi da ita lokacin da yayarta Fatima, ke goye da ita yayin ambaliyar da ta rutsa da su a Tudun Jukun da ke Zariya, a Jihar Kaduna.
An tsinci gawar ne bayan kwanaki shida da aka kwashe ana nemanta, a gangaren ƙasan Kilaco, unguwar Gyallesu, da misalin ƙarfe 11 na safiyar ranar Lahadi.
Babban jami’in ƙungiyar Red Cross a Zariya, Abdulmumin Adamu ne, ya tabbatar da gano gawar, inda ya ce hakan ya kawo ƙarshen binciken neman mutanen da ruwa ya tafi da su.
A ranar 8 ga watan Satumba, ambaliyar ruwa a Tudun Jukun, ta yi sanadin mutuwar ɗalibai biyu, Fatima Sani Danmarke da Yusuf Surajo (wanda aka fi sani da Abba).
A wannan lokacin ne kuma ruwa ya tafi da Fatima tare da ’yar uwarta Haneefa wadda ta ke goye a bayanta.
Kakan yarinyar, Malam Suleiman, ya ce an kira shi tare da shaida masa cewa wata bishiya ce ta riƙe gawar yarinyar a bayan Gyallesu.
Ya ce “A yau Lahadi da safe aka kira ni aka shaida min cewa an gano gawar Haneefa.
“Waɗanda suka gano ta sun ce wata bishiya ce ta tare gawar a can bayan Gyallesu Zariya.
“Don haka nan da nan muka yi mata jana’iza daga bisani kuma aka yi mata sutura aka binne ta,” in ji shi.
An yi wa Haneefa sutura tare da binne ta kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliya Gawa yarinya Zariya ruwa ya tafi da
এছাড়াও পড়ুন:
Madagascar Ta Sanar da Kafa Sabuwar Gwamnati Tare da Manyan ‘Yan Adawa
Madagascar ta sanar da kafa sabuwar gwamnati wadda ta kunshi fitattun ‘yan adawa guda uku a manyan mukamai na ministoci.
An gabatar da majalisar ministoci mai mambobi 29, wacce ta kunshi mata 10, a wani biki da aka gudanar a Fadar Gwamnatin Yavoloha da ke babban birnin kasar, Antananarivo.
Shugaban rikon kwarya Michael Randrianireina ya bayyana a lokacin bikin cewa manyan abubuwan da sabuwar gwamnatin ta sa gaba sun hada da yaki da rashin adalci, aiwatar da matakan tsuke bakin aljihu, da kuma samar da yanayin kasuwanci mai dorewa.
Ya kara da cewa kowane minista dole ne ya samar da sakamako mai kyau cikin watanni biyu, yana mai gargadin cewa rashin yin hakan a cikin wannan lokacin zai zama gazawa kuma zai iya haifar da maye gurbin minister a nan take.
An nada Christine Razanahasoa, tsohuwar Ministar Shari’a kuma tsohuwar Kakakin Majalisar Dokoki ta Kasa, a matsayin Ministar Harkokin Waje, kuma an nada Fanerisoua Irinavo, tsohuwar alkali wacce ta dawo daga gudun hijira daga Faransa, a matsayin Ministar Shari’a.
An nada Hanitra Razavimanantsoa, ’yar majalisa daga jam’iyyar Tiaco Madagascar karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Marc Ravalomanana, a matsayin Ministar Kasa a ma’aikatar Sake Gina Kasa. Waɗannan mutane uku suna wakiltar muryoyin manyan bangarorin ‘yan adawa a Madagascar.
Jagoran juyin mulkin, Michel Randrianireina, ya kwace mulki a ranar 14 ga Oktoba bayan tsohon shugaban kasar Andry Rajoelina ya tsere daga kasar a cikin jirgin saman sojojin Faransa bayan makonni na zanga-zanga.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta October 30, 2025 Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci