An Cafke Mutum Hudu Bayan ‘Yan Fashi 20 Sun Afka Wasu Gidaje A Bauchi
Published: 30th, August 2025 GMT
Ya bayyana cewa, “A ranar 16/08/2025, da misalin karfe 03:20 na dare, an samu kiran gaggawa daga wani da ba a bayyana sunansa ba, yana sanar da cewa tsakanin karfe 02:00 da 03:00 na dare, wata kungiyar ‘yan fashi kusan 20 dauke da makamai sun afka unguwar Madina da bayan tsohon makabarta a unguwar Fadaman Mada, inda suka shiga gidaje da dama suka yi wa mazauna sata tare da kwace musu kayayyaki masu daraja.
Wakil ya bayyana cewa jami’an ‘yansanda daga sashen C Dibision, karkashin jagorancin Dibisional Police Officer, sun hanzarta zuwa wurin tare da hadin gwiwar ‘yan sa-kai. Da zarar ‘yan fashin suka hango jami’an, sai suka tsere suka bar wasu daga cikin kayayyakin da suka sace.
“A nan gaba kadan, da misalin karfe 05:03 na dare a wannan rana, jami’an leken asiri da ke aikin sintiri suka kama daya daga cikin barayin, Ahmed Hassan, mai shekara 20, dan unguwar Tirwun, Bauchi, yayin da yake yawo a Warinje Hills da wayar hannu ta Gionee da aka kwace a hannunsa,” in ji shi.
A cewar sanarwar, bayanin da Hassan ya bayar ya taimaka wajen cafke sauran mutum uku: Ismail Isah mai shekara 18 (wanda aka fi sani da Masha), Uzaifa Abubakar mai shekara 19 (wanda aka fi sani da Damo), da kuma Abdulhamid Idris mai shekara 20.
Kayan shaidar da aka kwato sun hada da bindigar kera gida kirar rebolber, harsashi daya na 7.62mm, wuka, bindigar gida gajera (Dane gun), adduna guda biyu, da fitila.
“A lokacin binciken da ake yi musu, wadanda ake zargin sun amsa cewa su ne ke da alhakin wasu ayyukan fashi da makami daban-daban a cikin Birnin Bauchi. Ana ci gaba da kokari don bin diddigin sauran abokan harkarsu da kama su. Bayan kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu,” in ji Wakil.
Wannan cigaban ya biyo bayan karin matakan da ake dauka wajen yaki da aikata laifuka a jihar. A baya-bayan nan, Kwamishinan ‘Yan Sanda, Sani Omolori-Aliyu, ya bayyana cewa an kama mutane 748 da ake zargi da hannu a cikin laifuka 394 a Bauchi cikin watanni takwas da suka gabata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppকীওয়ার্ড: mai shekara
এছাড়াও পড়ুন:
Gwamnatin Jihar Kwara Ta Kafa Kwamitoci 2 Don Tantance Wadanda Suka Yi Ritaya
Daga Ali Muhammad Rabi’u
Gwamnatin Jihar Kwara ta kafa kwamitoci biyu domin tantance bayanan wadanda suka yi ritaya a matakin jiha da kananan hukumomi.
A cikin wata sanarwa da Kwamishinar Kudi ta jihar, Dakta Hauwa Nuru ta fitar, ta bayyana cewa kwamitocin za su tantance tare da tabbatar da sahihancin bayanan wadanda suka yi ritaya, domin a biya su bisa lokacin da suka bar aikin gwamnati.
A cewarta, kwamitin mutum takwas da aka kafa don kula da kudaden ritaya na matakin jiha zai kasance karkashin jagorancin Mai Duba Asusun Jiha, wato (Auditor General), yayin da wanda ke kula da matakin kananan hukumomi zai kasance karkashin Mai Duba Asusun Kananan Hukumomi.
Sanarwar ta bayyana cewa babban burin kwamitocin shi ne tabbatar da cewa an tattara bayanan masu ritaya bisa gaskiya da adalci, tare da biyan su kai tsaye ta asusun ajiyar banki.
Ta kara da cewa, mambobin kwamitocin sun hada da wakilan tsofaffin manyan sakatarorin, kungiyar tsofaffin ma’aikata, Kungiyar Kwadago ta Najeriya (NLC), da kungiyar kwadago ta TUC, da sauransu.