Radio Nigeria Kaduna Hausa:
2025-07-31@03:29:08 GMT

APC Zamfara Ta Taya Sabon Sarkin Katsinar Gusau Murna

Published: 30th, July 2025 GMT

APC Zamfara Ta Taya Sabon Sarkin Katsinar Gusau Murna

Jam’iyyar APC reshen Jihar Zamfara ta taya sabon mai martaba Sarkin Katsinar Gusau, Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello, murnar hawansa karagar mulki a matsayin Sarkin Katsinan Gusau na 16.

 

Jam’iyyar a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun sakataren yada labaranta, Yusuf Idris Gusau, ta bayyana sabon sarkin a matsayin mai tarihi da kuma nadin sarautar Allah, wanda ya zo ne jim kadan bayan rasuwar mahaifinsa, marigayi sarki, Alhaji Ibrahim Bello.

 

Sanarwar ta nuna cewa Alhaji Abdulkadir kyawawan halaye na gaskiya, kwazonsa, sadaukarwa, biyayya ga mahaifinsa da ya rasu, da kuma mutunta al’umma ta kowane hali, sun nuna shi ne wanda ya cancanta.

 

A cewar sanarwar, wannan shi ne karo na farko a tarihin masarautar da wani dan da ya haifa kai tsaye ya gaji mahaifinsa, wanda jam’iyyar ta ce hakan yana nuna yardar Allah da kuma ci gaba da gadon adalci na marigayi sarki.

 

Jam’iyyar APC ta bukaci sabon sarkin da ya kiyaye dabi’u da abubuwan gado na mahaifinsa da kakanni, musamman na fitaccen malamin addinin musulunci kuma shugaba, Sambo Dan-Ashafa.

 

Jam’iyyar ta yi addu’ar Allah ya yi masa jagora, ya kare shi, da kuma hikimar Sarki don ya jagoranci al’umma zuwa ga zaman lafiya da wadata.

 

Har ila yau, ta ba da tabbacin ci gaba da goyon bayanta da shirye-shiryenta na neman shawara, jagoranci, da albarka daga sabon sarki.

 

Daga karshe sanarwar da sakon fatan alheri ga mai martaba sarki da daukacin masarautar Gusau.

 

 

REL/AMINU DALHATU

উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa

কীওয়ার্ড: APC Zamfara sabon sarki

এছাড়াও পড়ুন:

An Fara Sabon Zagayen Tattaunawar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka A Sweden

Tawagogin wakilan kasashen Sin da Amurka sun hallara a kasar Sweden yau Litinin, domin fara wani sabon zagayen tattaunawa game da cinikayya da tattalin arziki. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Shugabannin Arewa Sun Tattauna Sabon Hanyar Ci Gaba – Minista Uba Maigari Ya Yaba
  • Birtaniya Ta Yi Allah-Wadai Da Kisan Mutane 33 A Zamfara
  • Gwamnatin Zamfara ta amince da naɗin sabon Sarkin Katsinan Gusau
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a Alkaleri
  • Gwamna Lawal Ya Naɗa Sabon Sarkin Gusau
  • Gwamnan Zamfara Ya Naɗa Abdulkadir Ibrahim A Matsayin Sabon Sarkin Katsinan Gusau Na 16
  • An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025
  • An Fara Sabon Zagayen Tattaunawar Cinikayya Tsakanin Sin Da Amurka A Sweden
  • Matawalle Ya Bada Tallafin Kudi Da Kayayyakin Abinci Ga Iyalan Marigayi Sarkin Gusau