Aminiya:
2025-09-17@21:31:32 GMT

Likitoci sun tsunduma yajin aiki a fadin Najeriya

Published: 12th, September 2025 GMT

Kungiyar Likitocin Masu Neman Kwarewa ta Najeriya (NARD) ta umurci mambobinta da su dakatar da aiki a dukkan asibitocin gwamnati da ke fadin Najeriya daga yau Juma’a.

Wannan mataki ya biyo bayan karewar wa’adin sa’o’i 24 da kungiyar ta bai wa Gwamnatin Tarayya don cika bukatunsu da ba a biya ba.

Wa’adin ya biyo bayan karewar wani wa’adin na kwanaki 10 da ya kare a ranar 10 ga Satumba ba tare da an biya wa likitocin bukatun nasu ba.

Ambaliyar ruwa ta tsayar da ababen hawa cak a tsakiyar birnin Abuja Jonathan ya tattauna da Peter Obi kan tsayawa takara a 2027

A ranar daya ga watan Satumba, NARD ta gargadi gwamnati cewa za ta fara yajin aikin sai baba ta gani idan ba a saurari bukatunsu ba cikin kwanaki 10.

Likitocin, wadanda su ne suka fi yawa a asibitocin koyarwa da asibitocin kwararru, sun sha shiga yajin aiki a shekarun baya saboda matsaloli kamar su rashin biyan albashi, rashin jin dadin aiki da kuma yanayin aiki mara kyau.

Shugaban NARD, Dr. Tope Osundare, ya shaida wa Aminiya a ranar Alhamis cewa sabon wa’adin ya fito ne daga taron sa’o’i shida da Majalisar Zartarwa ta Kasa (NEC) ta kungiyar ta gudanar ta bidiyo a ranar Laraba.

Aminiya ta rawaito cewa likitocin na bukatar a biya su kudin horar da likitocin gida na shekarar 2025 da aka rike musu, sai bashin watanni biyar na karin albashi da aka yi tsakanin kashi 25 zuwa 35 cikin dari, da sauran bashin albashi da suka dade suna bi.

Sauran bukatun sun hada da biyan bashin kudin kayan aiki na shekarar 2024, biyan kudin kwararru cikin lokaci, da dawo da amincewa da takardun digiri na biyu na Afirka ta Yamma.

Osundare ya ce duk da alkawarin da gwamnati ta yi wa kungiyarsu na magance matsalolin, sun dage sai an dauki matakin cika su nan take kafin su yarda su koma aiki.

Ya ce: “Gwamnatin Tarayya ta kira mu jiya kuma ta yi alkawarin magance matsalolinmu.

“Mun yi taronmu, kuma bayan tattaunawa na sa’o’i shida, mun yanke shawarar bai wa gwamnati sa’o’i 24 don tabbatar da biyan kudin MRTF ga wadanda suka cancanta, MDCN ta sabunta takardun mambobinmu, da kuma magance sauran bukatunmu.

“Idan babu wani abu da ya faru kafin karshen yau (Alhamis), za mu fara yajin aiki nan take gobe (Juma’a).

“Gwamnati ta gaggauta daukar mataki kan bukatun da ke gabanta.”

A safiyar Juma’a, Osundare ya tabbatar wa Daily Trust cewa yajin aikin ya fara.

“Abin takaici, ba a cika ko da daya daga cikin bukatun da muka gabatar cikin wa’adin sa’o’i 24 ba, kuma yajin aikin ya fara a safiyar nan kamar yadda NEC ta umurta,” in ji shi a cikin gajeren sakon da ya tura wa wakilinmu.

Da aka tambaye shi ko yajin aikin na gargadi ne, sai ya amsa da cewa, “Za mu sake duba lamarin bayan Gwamnatin Tarayya ta dauki matakin da ya dace.”

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: NARD Yajin aiki yajin aikin

এছাড়াও পড়ুন:

NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa

More Podcasts Najeriya a Yau Daga Laraba

Ambaliyar ruwa na cigaba da salwantar da dukiyoyi da rayukan al’ummomi da dama a sassa daban-daban na Najeriya.

 

Ko a farkon makon nan, hukumomi sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar a jihohi akalla 11.

Sai dai wasu alummomin tuni suka dauki matakai don rage barnar da ambaliyar ka iya yi musu.

NAJERIYA A YAU: Masu Nau’in Jinin AS Sun Fi Masu Nau’in AA Lafiya DAGA LARABA: Dalilan Da Suka Sa Nayi Yunkurin Kashe Kaina Har Sau Uku

A kan wadannan matakai shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci zai yi nazari.

Domin sauke shirin, latsa nan

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu bai shirya gudanar da sahihin zaɓe ba a 2027 – Buba Galadima
  • Gwamnati ta fara duba yara marasa galihu kyauta a asibitin Aminu Kano
  • Najeriya Na Asarar Dala Biliyan 10 Bayan Girbi Duk Shekara- Gwamnatin Tarayya
  • NSCDC Za Ta Fara Sanyan Ido Kan Muhimman Abubuwan More Rayuwa A Jihar Kano
  • NAJERIYA A YAU: Matsayin Doka Kan Hawa Mumbari Ba Tare Da Izinin Gwamnati Ba
  • Sulhu Da ‘Yan Bindiga Ya Fara Shan Ƙasa, Sun Yi Garkuwa Da Masallata A Zamfara 
  • Ƴan Bindiga Sun Sace Malamin Krista Na Ɗarikar Katolika A Kogi
  • Likitoci Sun Tsunduma Yajin Aiki Na Dindindin A Abuja
  • Sarki Sanusi II ya koka kan yawan cin bashin Najeriya
  • NAJERIYA A YAU: Yadda Wasu Al’ummomi Suke Kare Kansu Daga Barnar Ambaliyar Ruwa