Jigawa Na Gabatar Taro A Abuja Domin Tattara Bayanin Kasafin Kudin 2026
Published: 20th, September 2025 GMT
Ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta jihar Jigawa, ta shirya taron yini daya a birnin tarayya tare da hadin gwiwar ELIP kungiyar farar hula ta musamman, domin tattara kayan aiki na kasafin kudin 2026.
A nasa jawabin kwamishinan kasafin kudi da tsare-tsare na jihar Alhaji Ibrahim Babangida Umar Gantsa ya bayyana mahimmancin taron, inda ya ce abubuwan da masu ruwa da tsaki suka yi na da matukar muhimmanci.
Babangida Gantsa wanda ya samu wakilcin Daraktan SDG na ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta jiha, Alhaji Basiru Nasoro ya bukaci masu ruwa da tsaki su samar da bayanai masu ma’ana.
A nasa jawabin, Alhaji Najibullah Ahmad wanda masanin kasafin kudi ne ya bayyana cewa, makasudin shi ne a jawo hankalin ‘yan kasa da jawo hankalinsu tare da samar da gaskiya da rikon amana a cikin tsarin kasafin kudi.
A cewarsa, taron zai kuma baiwa masu ruwa da tsaki damar zakulo wuraren da suka fi ba da fifiko da kuma taimakawa gwamnati wajen yanke shawara, tare da samar da yanayi mai kyau na sanin ya kamata.
Najibullah ya yi nuni da cewa, taron zai kuma bayar da rahoto na shekara-shekara kan yadda kudaden jama’a suka kasance kuma za a ware domin biyan bukatun jama’a.
Shima da yake jawabi, Alhaji Isa Mustapha wanda shi ma ma’aikaci ne a ma’aikatar, ya bayyana cewa tsarin kashe kudi na matsakaicin zango, ya samar da cikakken tsari.
A cewarsa, tsarin ya yi daidai da shirye-shiryen gwamnati, tallafin masu ba da tallafi da kuma shirye-shiryen kamfanoni masu zaman kansu don cimma manufa guda.
Alhaji Ayuba Doro Gwaram, wakilin ELIP wanda ya gabatar da jawabi kan abubuwan da ‘yan kasa suka zaba a shekarar 2024, inda ya yi nazarin abubuwan da ‘yan kasa ke nunawa a cikin kasafin kudin 2025.
Ayuba ya ce, an gabatar da bayanai 1,105, sannan 548 sun bayyana a cikin kasafin, wanda ya nuna kashi 49 cikin 100 na jimillar abubuwan da aka gabatar.
Ya yi nuni da cewa, abubuwan da aka samu sun nuna kashi 26.8 cikin 100 na jimillar kasafin kudi na Naira biliyan 175.442 na jihar Jigawa a shekarar 2025, wanda hakan ya nuna cewa abin da ‘yan kasa ke amfani da shi ya haura na shekarar 2023 a fannin kudi.
Ayuba ya yi nuni da wasu daga cikin kalubalen da suka hada da rashin sa ido kan ayyukan, rashin karkatar da albarkatun kasa da kuma wahalar daidaita bukatu da bukatu a fagen dimokuradiyya.
Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, wasu kungiyoyin CSO da na kananan hukumomi sun bayar da bayanai daban-daban a taron majalisar dattijai da ya kunshi kananan hukumomi 7 na jihar Jigawa.
KARSHE/USMAN MZ
উৎস: Radio Nigeria Kaduna Hausa
কীওয়ার্ড: abubuwan da
এছাড়াও পড়ুন:
Hukumar Alhazai Ta Jigawa Za Ta Shirya Taron Bita Na Musamman Ga Jami’anta
A kokarin ta na ci gaba da zaburar da ma’aikatan ta, Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce za ta shirya taron bitar sanin makamar aiki ga jami’an ta dake dawainiya da alhazai a gida da kuma kasa mai tsarki.
Darakta Janar na hukumar, Alhaji Ahmed umar labbo ya bayyana haka bayan kamala taro na musamman da shugabannin sassa na hukumar da aka gudanar a shelkwatar hukumar dake Dutse babban birnin jihar.
Yayi bayanin cewar, hukumar zata bada bitar ne ga jami’an da kuma shugabannin shiyya-shiyya kan hanyoyin kara kula da walwala da jin dadin maniyyata da kuma dabarun magance kalubale yayin gabatar da aikin hajji.
Yana mai cewar bada horo na da matukar mahimmaci duba da yadda aka fara biyan kudin kujerun aikin hajjin 2026.
Alhaji Ahmed Umar Labbo, yace tuni shirye-shirye sunyi nisa waje fara shirin dunkarar aikin hajjin shekarar 2026.
A cewar sa, tsarin gudanar da aikin hajjin wannan shekarar yasha bam-bam da na shekarar 2024.
Yayi nuni da cewar, a bana, 8 ga watan Oktoba wannan shekerar da muke ciki itace ranar karshe ta biyan kudin kujeran aikin hajji kamar yadda hukumar kasar Saudi Arabia ta bayyana.
A sabili da haka nema Labbo yayi kira ga maniyyata aikin hajjin badi da su gaggauta biyan kudin ajiyar su na naira miliyan 8 da dubu dari 5 kamar yadda hukumar aikin hajji ta kasa NAHCON ta bayyana.
Ahmed Labbo, ya yabawa Gwamna Umar Namadi bisa kula da ayyukan hukumar a kowane lokaci.
NAHCON dai ta baiwa Jihar Jigawa kason kujeru fiye da 1,600 na maniyyatan aikin hajjin.
Usman Mohammed Zaria