Aminiya:
2025-07-31@09:53:22 GMT

Sojoji sun daƙile hari, sun kashe mayaƙan Boko Haram 9 a Borno

Published: 30th, July 2025 GMT

Dakarun Operation Haɗin Kai da ke Arewa maso Gabas, sun ɗakile wani sabon hari da mayaƙan Boko Haram suka kai a Jihar Borno.

Sun kai harin ne yankunan Konduga, Bama da Gwoza.

Shugaban hukumar zabe ta jihar Bauchi ya rasu Adadin Falasdinawan da Isra’ila take kashewa a Gaza yanzu ya haura 60,000

’Yan ta’addan sun yi yunƙurin tarwatsa gadar da ke kan hanyar Marte zuwa Dikwa ta hanyar dasa bama-bamai.

Amma sojoji sun gano abubuwan fashewa guda 17 da suka dasa a ƙarƙashin gadar kuma suka cire su.

A yayin daƙile harin, sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram guda tara, sannan sun ƙwato bindigogi ciki har da AK-47 da bindigar PKT.

Kakakin rundunar sojin a Maiduguri, Kyaftin Reuben Kovangiya, ya ce dakarun na ci gaba da kai farmaki da sanya ido kan ayyukan ‘yan ta’addan a yankin.

Ya ce wannan nasarar na nuna cewa sojoji sun ƙudiri aniyar hana ’yan Boko Haram da ISWAP aikata ta’addanci.

Rundunar sojin ta roƙi jama’a da su ci gaba da bayar da haɗin kai ta hanyar bayar da rahoton motsin duk wani mutum da suke zargi yana da alaƙa da ’yan ta’adda ga jami’an tsaro.

উৎস: Aminiya

কীওয়ার্ড: yan ta adda Boko Haram hari

এছাড়াও পড়ুন:

Tinubu ya karɓi baƙuncin Abdulmumin Jibrin Kofa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya karɓi baƙuncin ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Kiru da Bebeji na Jihar Kano, Abdulmumin Jibrin Kofa.

Aminiya ta ruwaito cewa Kofa, wanda makusanci ne ga jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, kuma ɗaya daga cikin jiga-jigai a jam’iyyar NNPP, ya ziyarci shugaban ƙasar ne a yau Laraba.

Za a kammala shimfiɗa layin dogo daga Kaduna zuwa Kano a 2026 — Gwamnatin Tarayya Tattalin arzikin Nijeriya zai ci gaba da bunƙasa har zuwa baɗi — IMF

Har yanzu dai babu wasu bayanai dangane da abin da suka tattauna, amma ziyarar wadda hadimai daga ɓangarorin biyu suka riƙa yaɗawa na ci gaba da ɗaukar hankalin jama’a.

সম্পর্কিত নিবন্ধ

  • Tinubu ya karɓi baƙuncin Abdulmumin Jibrin Kofa
  • Shugabannin Arewa Sun Tattauna Sabon Hanyar Ci Gaba – Minista Uba Maigari Ya Yaba
  • ’Yansanda Sun Ceto Mutane 28 Da ‘Yan Bindiga Suka Sace A Katsina
  • Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 45 A Jihar Neja
  • ’Yan bindiga sun kashe mutum 5 a sabon hari a Alkaleri
  • Sojojin HKI Sun Ci Gaba Da Kashe Kawunansu
  • An kashe ’yan ta’adda 45 a Neja
  • Sojoji, DSS Sun Hallaka Ƴan Bindiga 45 A Neja
  • Harin Sojojin Sama Ya Hallaka Manyan Shugabannin ISWAP A Borno