Sojojin HKI, Daga Jiya Zuwa Yau lahadi Kadai Sun Kashe Falasdinawa 62
Published: 3rd, August 2025 GMT
Sojojin HKI sun kashe falasdinawa 62 daga safiyar jiya Asabar zuwa lokacin bada wannan labarin a yau Lahadi.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa mafi yawan wadanda aka kashen masu neman abainci ne, a cibiyoyin karban abincin wadanda HKI da Amurka suka kafa.
Kafafen yada labarai daga asbitocin Gaza sun bayyana cewa a jiya Asabar yahudawan sun kashe mutane 38 masu neman abinci.
Zuwa ranar jumma’an da ta gabata, sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa 105 cikin wadanda suka fito neman abinci kadai. A ranakun laraba da Alhamis da suka gabata, hukumar abinci ta duniya ta bayyana cewa sojojin yahudawan sun ci gaba da kashe Falasdinawa a gaza akan neman aminci, wanda hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa. Tace tun baya fara wannan shirin bada abinci sojojin HKI sun kashe falasadinwa 1,373 kan karban abinci kadai.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Pezeskkian Ya Ce: Suna Fatan Musayar Kasuwancin Tsakanin Iran Da Pakistan Ta Haura Dala Biliyan 10 August 2, 2025 Araqchi: Abokantaka Da Ke Tsakanin Iran Da Pakistan Wata babbar Jari Ce Nan Gaba August 2, 2025 Jaridar Isra’ila Ta Ce: Gwamnatin Mamayar Isra’ila Ta Sha Kashi A Yakin Gaza August 2, 2025 Dakarun Yemen Sun Kai Hari Kan Filin Jirgin Lod Da Ke Haramtacciyar Kasar Isra’ila August 2, 2025 Rahoton Majalisar Dinkin Duniya Ya Yi Gargadi Kan Barazanar Kungiyoyin ‘Yan Ta’adda A Afirka August 2, 2025 Shugaba Pezeshkiyan Ya Yi Juyayin Shahadar Haniya Bayan Shekara Guda Da Shahada August 2, 2025 MDD: HKI Ta Kashe Falasdinawa Fiye Da 100 A Cikin Kwanaki 2 A Lokacinda Suka Karban Abinci August 2, 2025 Mutanen Kasar Siriya Sun Fito Zanga-Zanga Yin Allawadai Da Kissan Alawiyya A Kasar August 2, 2025 Shugaban Ansarullah: Amurka Tana Da Hannu A Ta’asar Da HKI Take Aikatawa A Gaza August 2, 2025 Kungiyar Wasan Taekwondo Ta Guragu Ta Iran Ta Zama Zakara A Asiya Karo Na 10 A Jere August 2, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunciউৎস: HausaTv
কীওয়ার্ড: kashe Falasdinawa
এছাড়াও পড়ুন:
Iran ta yi fatali da kalamman IAEA Kan Shirin Nukiliyarta
Iran ta yi ikirarin cewa Darakta Janar na Hukumar Makamashin Nukiliya Ta Duniya (IAEA), Rafael Grossi, ya “san”sarai da cewa shirin nukiliyar kasar na lumana ne, don haka ya kamata ya guji yin “kalamai marasa tushe” kan lamarin.
A wata hira da ya yi da tashar Al Jazeera, kakakin Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Esmail Baghai ya bayyana cewa kalaman da Rafael Grossi ya yi a baya sun share fagen ayyukan ta’addanci da Amurka da gwamnatin Isra’ila suka yi wa Iran a watan Yunin da ya gabata.
Ya kamata Darakta Janar na IAEA ya guji yin kalamai marasa tushe game da shirin nukiliya na Iran, in ji shi.
Rafael Grossi ya bayyana a ranar Laraba cewa IAEA ta gano kwanan nan da sake dawowa da ayyuka a wuraren nukiliya na Iran,” bayan ya amince cewa kasar ba ta nuna alamun kara wadatar da uranium ba.
A cikin wani rahoto na sirri da aka gabatar wa Kwamitin Gwamnonin IAEA a ranar 31 ga Mayu, 2025, Babban Daraktan IAEA ya yi iƙirarin cewa “Iran ta gaza bayyana ayyukanta na nukiliya a wurare uku da ba a bayyana ba” kuma ta bayyana damuwa game da tarin sinadarin uranium da ta wadatar zuwa kashi 60%.
A cewar jami’an Iran, rahoton Grossi game da shirin nukiliya na Tehran ya share fagen kai hari ga Isra’ila kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran.
A karshen watan Yuni ne, Majalisar Tsaron Iran ta amince da wani kudiri da majalisar dokokin kasar ta zartar wanda ya dakatar da haɗin gwiwa da hukumar ta IAEA.
Share
0 0 votes Article Rating Subscribe Login Notify of new follow-up comments new replies to my comments Label {} [+] Name* Email* Website Label {} [+] Name* Email* Website 0 Comments Oldest Newest Most Voted Inline Feedbacks View all comments Masu Alaka Trump Ya Umarci Ma’aikatar Yakin Amurka Ta koma gwajin makaman nukiliya October 30, 2025 Isra’ila ta amince da fadada matsugunai a Yammacin Kogin Jordan October 30, 2025 Gaza: hare-haren Isra’ila sun kashe mutane 100 Cikin Kwanaki Biyu October 30, 2025 Sudan : Kasashen duniya na tir da cin zarafi a El-Fasher October 30, 2025 Iran Ta Jaddada Bin Hanyar Diflomasiya Ko Da A Lokacin Yaki Ne Amma Ba Zata Amince Da Bin Umarni Ba October 30, 2025 Qalibaf: Amurka Tana Yaudarar Duniya Da Zaman Lafiya, Alhalin Tana Ci Gaba Da Kai Harin Wuce Gona Da Iri October 30, 2025 Ci Gaba Da Killace Gaza Bayan Tsagaita Bude Wuta Ya Janyo Mutuwar Mutane 1000 A Yankin October 30, 2025 Kungiyar Rapid Support Forces Ta Sanar Da Kafa Kwamitin Bincike Kan Cin Zarafin Al’umma A El Fasher October 30, 2025 An Kafa Dokar Ta Baci A Darul-Salam Saboda Tarzoman Zaben Shugaban Kasa A Tanzania October 30, 2025 Rasha Da Amurka Sun Sake Dawo Da Gwaje-gwajen Makaman Nukiliya October 30, 2025 Categories Afirka Dogayen fina-finai Duniya Gallery IRAN IRAN POLITICS IRAQ Mata MIDDLE EAST Musulunci