Borno Za Ta Sake Tsugunar Da ‘Yan Gudun Hijira 5,000 Kafin Damuna Ta Kare
Published: 3rd, August 2025 GMT
Gwamnatin jihar Borno na shirin sake tsugunar da ‘yan gudun hijira kusan 5,000 daga al’ummomin Bama su biyar kafin damina ta kare. Gwamna Babagana Umara Zulum ya bayyana haka a wata ziyarar ban girma da ya kai wa Shehun Bama, Dakta Umar Kyari Umar El-Kanemi a ranar Juma’a. Ministan Yaɗa Labarai Ya Buƙaci A Kwantar Da Hankali Kan Dakatar Da Gidan Rediyon Badeggi FM Gwamnatin Tarayya Za Ta Aiwatar da Shirin Daƙile Sulalewar Kuɗaɗen Haraji Al’ummomin da aka kudiri niyyar sake tsugunar da su sun hada da Goniri, Bula Kuriye, Mayanti, Abbaram da Darajamal.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsAppএছাড়াও পড়ুন:
Ambaliya: Mutum 165 sun mutu a Nijeriya a bana — NEMA
Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Nijeriya (NEMA) ta ce aƙalla mutane 165 ne suka rasu, sannan 82 suka ɓace sakamakon ambaliya a bana.
NEMA ta bayyana haka ne a ranar Juma’a a wata ƙididdiga da ta fitar, tana mai cewa ambaliyar ta shafi aƙalla mutum 119,791 a bana — kuma mafi akasari mata ne da yara.
Dadiyata: Buhari ya gaza nemo shi, Tinubu yana da lokaci — Amnesty Mutum ɗaya ya rasu, an jikkata wasu yayin arangama da ’yan sanda a AbujaTa bayyana cewa mutane 138 sun samu raunuka iri-iri, 43,936 sun rasa matsugunansu, gidaje 8,594 da gonaki 8,278 ne ambaliya ta shafa a cikin ƙananan hukumomi 43 da ke jihohi 19.
Ta ce, “Yara 53,314, mata 36,573, maza 24,600, tsofaffi 5,304 da kuma mutane 1,863 masu nakasa ne ambaliya ta shafa a bana.”
Jihohin da suka fi yawan waɗanda ambaliya ta shafa sun haɗa da Imo, Ribas, Abia, Borno da Kaduna.
A halin yanzu, jihohi 19 da ambaliya ta shafa sun haɗa da: Abia, Abuja, Adamawa, Akwa Ibom, Anambra, Bayelsa, Borno, Edo, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kogi, Kwara, Neja, Ondo, Ribas da Sakkwato.