Sai an samar da ’yantacciyar ƙasar Falasɗinu za mu ajiye makamai — Hamas
Published: 3rd, August 2025 GMT
Ƙungiyar Hamas ta sake jadadda matakinta na cewa ba za ta taɓa ajiye makami ba, har sai lokacin da duniya ta amince da samar da ’yantacciyar ƙasar Falasɗinu a yankin Gabas ta Tsakiya, wani abu da zai sake mayar da yarjejeniyar zaman lafiya da ake ƙoƙarin ƙullawa baya.
A halin da ake ciki yanzu haka ana wata tattaunawa wadda ba ta kai tsaye ba tsakanin Isra’ila da Hamas don ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 60, da kuma sakin mutanen da ke riƙe a hannun ɓangarorin biyu.
A Talatar da ta gabata ne ƙasahen Qatar da Masar suka sanar da matakin ƙasashen Saudi Arabiya da Faransa na goyon bayan samar da ƙasar Falasdinu, don tabbatar da dawamammen zaman lafiya a gabas ta tsakiya.
To amma ƙasashen sun ce hakan za ta yiwu ne kawai idan har Hamas ta amince da ajiye makamai ga mahukuntan Faladinu da ke Ramallah.
A wata sanarwa da Hamas ɗin ta fitar ta ce bazata taɓa ajiye makamai ba, har sai ta tabbatar da samun ƴancin kan Falasɗinawa, da kuma ayyana birnin Ƙudus a matsayin babban birni.
Wannan ba shi ne karon farko da Hamas ke bayyana hakan a matsayin hanya ɗaya tilo ta ajiye makami ba, yayin da ita kuma Isra’ila ke cewa zata yi kowacce irin tattaunawa da Hamas ne bayan sun amince da ajiye makami.
A makon da ya gabata Firaministan Isra’ila Benjamin Natenyahu ya ce ba shakka samar da ƴantacciyar ƙasar Falasɗinu, shimfida hanya ne na rusa Isra’ila don haka ba zai taɓa aminta da hakan ba, kuma dole ne sha’anin tsaron yankunan Falasɗinu ya kasance ƙarƙashin ikon ƙasar sa.
Da yake caccakar matakin ƙasashen Birtaniya, Canada da kuma Faransa na goyon bayan samar da ƙasar Falasɗinu biyo bayan halin da Isra’ila ta jefa al’ummar Gaza, ya ce wannan abu ne da Hamas ta janyo.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Isra ila ƙasar Falasɗinu
এছাড়াও পড়ুন:
Trump Ya Ayyana Nijeriya A Matsayin Ƙasar Da Rayuwar Kiristoci Ke Cikin Hatsari
“Amurka ba za ta tsaya kawai tana kallo ba yayin da irin waɗannan ta’addancin ke faruwa a Nijeriya da sauran ƙasashe.
“Mun shirya, muna da ƙarfi da niyyar kare Kiristoci a faɗin duniya,” in ji Trump.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA