Jamus ta soma jefa kayan agaji a Zirin Gaza
Published: 3rd, August 2025 GMT
Rundunar sojin Jamus ta fara gudanar da aikin jefa kayayyakin gaji da suka hada da abinci da magunguna ta sama a Zirin Gaza.
Ma’aikatar Tsaron Jamus da ke Berlin, fadar gwamnatin kasar, ce ta tabbatar da hakan, inda ta ce jiragen rundunar sojin sama sun ajiye kunshin tallafi 34 dauki da tan 14 na abinci da kuma magunguna.
Sai dai a cewar Ministan Tsaron Jamus, Moris Pistorius kai tallafi ta sama ba zai yi wani babban tasiri ba.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, Zirin na bukatar tallafin tan dubu 62 na abinci a duk wata domin mutane su rayu.
Tun a ranar Lahadin makon jiya Isra’ila ta aminci da shigar da agaji ta kasa da sama, inda kasashe irinsu Jordan da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa suka yi ta jefa kayan agaji ta sama.
Ana ci gaba danka kayayyakin tallafin a hannun kungiyoyin agaji na kasa da kasa da suke ci gaba da ayyukan rarraba su.
Ahmad Nadir, na kungiyar lafiya ta duniya WHO, ya ce tsame hannun Isra’ila daga batun karba da rabon kayan agaji ne kadai zai bai wa kwarraru kan ayyukan agaji damar gudanar da ayyukan da za a samu nasara.
A bayan nan ne Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP ta ce kashi uku na al’ummar Gaza ba su ci abinci na kwanaki ba, kuma mutane 470,000 suna cikin yanayi na juriyar tsananin yunwa wanda tuni ya kai ga mutuwar wasu.
Isra’ila dai na ci gaba da fuskantar suka daga kasashen duniya, kan amfani da yunwa a matsayin makamin yaki kan al’ummar Falasdinu, lamarin da gwamnatin kasar ta ki amincewa da shi.
A makon jiyan ne aka fara shigar da kayyakin agaji zuwa Zirin Gaza wadanda galibi ta sararin samaniya aka rika jefawa da jirage daga kasashen Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa.
Arshiyan Kohen, kakakin ma’aikatar tsaron Isra’ila ya ce, za a dakatar da farmakin soji na tsawon sa’o’i 10 a kowace rana a wasu sassan Gaza tare da ba da damar samun sabbin hanyoyin ba da agaji.
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Gutteress ya siffanta wannan matakin da mai sanyaya zuciya bayan damuwa da bala’in da mazauna Gaza suka tsinci kansu a ciki, yana mai fatar gaggauta shigar da kayayyakin agajin da kuma dorewarsa.
Babban jami’in bayar da agajin gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya, Tom Fletcher ya yi maraba da matakin, yana mai cewa yanzu haka yana tuntubar kungiyoyi wadanda za su yi duk mai yiwuwa don isa ga mutane da dama da ke fama da yunwa a wannan lokaci.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Majalisar Dinkin Duniya
এছাড়াও পড়ুন:
Mutane 44 Suka Mutu Bayan Mamakon Ruwa Da Aka Tafka A Beijing
Ruwan sama kamar da bakin kwarya tare da iska mai karfi da aka tafka a kwanan nan ya yi sanadin mutuwar mutane 44, yayin da wasu tara suka bace a birnin Beijing, kamar yadda aka bayyana a wani taron manema labarai da ya gudana a yau Alhamis.
A yayin taron manema labarai da gwamnatin birnin Beijing ta gudanar a yau game da rigakafin ambaliyar ruwa da bayar da agajin gaggawa, an bayyana cewa, bala’in ambaliyar ruwan da ya auku kwanan nan ya shafi mutane sama da 300,000 tare da lalata gidaje 24,000 a birnin Beijing.
Sai dai, yanzu haka birnin na Beijing na kara kokarin farfado da wutar lantarki, da share tituna, da kai muhimman kayayyaki ga mazauna yankin da suka rasa matsugunansu, sakamakon ambaliyar ruwa da zabtarewar kasa da suka auku sanadin mamakon ruwan sama mai karfi da aka tafka a tsaunukan da ke wajen birnin. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp