Ambaliya ta yi ajalin mutum 30 a China
Published: 29th, July 2025 GMT
Ambaliya sanadiyyar wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ta yi ajalin mutane 30 a Arewacin China, lamarin da ya tilasta kwashe mutane fiye da 80,000 zuwa Beijing, babban birnin kasar.
Jaridar Beijing Daily ta ruwaito cewa ruwan saman ya haddasa rufe hanyoyi da dama da kuma katsewar lantarki a kauyuka sama da 130 yayin da jami’an agaji ke ci gaba da aikin ceto.
A jiya Litinin ce Shugaban China, Xi Jinping ya ba da umarnin daukar matakan gaggauwa a yankunan da ke fuskantar hadarin ambaliya sakamakon mamakon ruwan da ake hasashen za a ci gaba da tafkawa.
Xi Jimping ya bukaci mahukuntan yankunan da ke fuskantar hadarin ambaliyar da su gaggauta samar da tsare-tsare domin kubutar da jama’a.
A yanzu haka ana hasashen samun saukar mamakon ruwan sama har zuwa gobe Laraba a wasu yankuna sama da 10 na China.
Tuni dai mahukunta suka sanar da bayar da tallafin kudi yuan miliyan 550 — kwatankwacin dalar Amurka miliyan 76.7 ga yankunan da ambaliyar ruwa ta shafa.
Gwamnatin kasar ta ce ta ware yuan miliyan 200 — kwatankwacin dalar Amurka miliyan 27.86 musamman ga birnin Beijing, inda ruwan sama kamar da bakin kwarya ya kashe akalla mutane 30 tare da haddasa barna mai yawa.
Bayanai sun ce ambaliyar ruwan ta kuma shafi lardunan Hebei, da Liaoning, da kuma Shandong, lamarin da ya haifar da asara mai yawa da asarar dukiya.
উৎস: Aminiya
কীওয়ার্ড: Ambaliya ruwan sama
এছাড়াও পড়ুন:
An Kashe Mutum 3 Yayin Da ‘Yan Bindiga Suka Kai Hari Kan Iyakokin Kano
Majiyar ta kara da cewa, bayan yunkurinsu bai yi nasara ba a Tsanyawa, maharan sun sake wani sabon shiri, inda suka kai hari a kauyen Yar Tsamiya da ke gundumar Faruruwa, karamar hukumar Shanono, da misalin karfe 1:30 na dare, inda suka kashe mutane uku suka, tare da sace wasu uku.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
ShareTweetSendShare MASU ALAKA